← Book details Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 34

Sashe 5

Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya ta share kamar bata son ji har da cewa "Yau ka canza mana tsari, har lokacin bacci ya kusa ba muyi abinda ya kamata .ba." Shamaki yace insha Allahu za mu fidda komai kafin mu kwanta. Sannan ya sake marairaice murya in faɗa Hajiya?" Ta tattara hankalinta gare shi "Faɗi ina ji amma da sharaɗi, ko ka faɗamin koma menene, bana buƙatar ka fara roƙo na in amince da buƙatarka." Yaɗan yi shiru. Tace Inhar haka zaka yi to ina son ka bar zancanka. Sai yanzu ya fahimci gaba ɗaya Hajiya batasan komai ba tsabar lissafi ne kawai ta rikitashi ga shi har ta yi nasarar tarfashi zai faɗa mata, ƙila in da abinda ta sani bai wuce tasan ya je gidan Maman Umar shida sauran 'yan uwansa ba. Ya dube ta ta kafe shi da ido. Ya sunkuyar da kai, yace Wai Hajiya wa ya faɗa miki cewa mun haɗu da su 'yan uwana? Tayi ɗan murmushi mai sauti. Ta fahimci ya gano shurinsa ta ke yi bata da masaniyar komai. Ta ɗaure fuska. " Sai ana magana ka sauka daga kan layi kasan da lokacin bacci na ya yi zan miƙe kira min Azima ta shafa min maganin ƙafa. Yace to Hajiya bari mu gama maganar, dama fa kan batun girki ne na ranar taron ki da amarya ke yi, sai kuma maganar budurci. Ya ɗanyi shiru ko zata ce wani abu amma bai ji ta ce komai ba, dan haka ya ɗago kai ya dube ta. Shi take kallo har lokacin. Ya ci gaba, saboda ita Baby 'yar talakawa ce ba lallai ta iya girkin zamani ba,, a taimaka a sa su Juma.. Ta ɗaga mishi hannu. "Na taɓa cewa ga kalar girki da Amaryarka za ta yi?" Ya girgiza kai. Tace to "Wannan ban karɓa ba,ta zo ta dafa irin wanda ta iya na gidan nasu ta bamu muci, anrufe wannan batun sai kuma wanne ka ce?" Ya haɗiye yawu maganar budurci ne ce kawai duk yadda tazo bama sai mun tattauna maganar ba. Saboda likitoci suna ta bayani shine har Maman Afra take bada misali da matsalar Afra ta kwanaki. Hajiya ta ɗaga masa hannu, bana son wannan maganar ka barni akan ra'ayina. Yayi ɗif domin ta rufe ƙofar magiya tun farko, dan haka ya ɗakko ƙaramar laptop ɗinsa dake gefe a jaka zai fara yi mata bayanin kasuwa. Azima ta shigo da sallama ta tambayi Hajiya cewa a fara shafa magani yanzu? Hajiya ta yi mata izni.

Na farka na ganni kwance kayana a jiƙe sharkaf kaina a cinyar Umma, ga Abba na min fifita. Ajiyar zuciya irinta masu kuka na ji Jamila na yi, na tashi zaune da sauri nace Umma menene? Sai naji gaba ɗayansu suna min sannu, na tuna me yafaru. Da sauri nace Dan Allah Umma ban taɓa gani kuna faɗ ba sai a kai na. Na soma kuka, Abba ya ce ke komai ya wuce kar kiyi kuka. Umma tace ba inda ke miki ciwo? Na girgiza kai alamun babu. Umma Ta ce "To miƙe kije ki cire kayan." Na tashi Jamila ta zo da sauri ta riƙe min hannu muka nufi ɗakinmu, ina jin Abba yana lallashin Umma wai ita ma ta tashi taje ta kwanta.
A ɗaki na tambayi Jamila ko na yi Alhaji ne. Tace suma na yi Lokacin da nake ƙoƙarin furta cewa na fasa auren Aliyu." Nace iko Allah ni wannan wane irin so ne nake masa?Jamila tace Abba da Umma jikinsu ya yi sanyi da wannan son da ki ke masa. Abba ya ce gara kawai a ɗaura a kai ki. Wani daɗi naji a zuciya ta, na ɗakko Al'ƙur'ani na ce bari in sake jaddada karatuna gobe a gabansa zan yi ina son in burge shi sosai. Gashi na ci Sa'a ina daga cikin ɗalibai mu uku da Malam ya ware zamu yi karatu mu kaɗai kuma biyun maza ne ni kaɗaice mace. Jamila tace kinsan kina da muryar ƙira'a ne sosai Yaya Baby. Nace na sani 'yan ajinmu sai suce wai ina shan na'a na'a ne. Jamila tace "Baiwa ce. Haka na shiga raira karatu muryata tana ratsa tsakar gidanmu ko ina ya yi tsit. Na tabbata iyayena suna alfahari da ni in suka ji ina rero karatun Kur'ani. Washegari tun daga sallar asbashi ban koma ba, kafin bakwai tuni na gama shiri na sha atamfarmu ta anko da sabon hijabi, Umma tace in ɗauki takalmi a cikin kayan lefena in saka. Na gama shiri tsaf sannan na zauna na rubutawa Shamaki saƙo kamar haka..
Sanyin zuciyata fatan ka tashi lafiya tare da dukkan yaran mu da kuma Hajiyata. Dan Allah ina ƙara tunasar da kai cewa yau ne saukarmu zuwanka ya fi komai mahimmanci a guri na. Ina saka ido. Bayan na tura na jira amsar shi, amma bai aiko min ba, na kira layin naji yana waya. Ance ƙarfe takwas ta yi mana a makaranta amma ni harda minti goma, gaba ɗaya duniya ta daina min daɗi bani da tabbacin zuwan masoyina. Har Jamila ta fahimta ta tambaye ni,na faɗa mata damuwata. Ta shiga lallashina akan tasan zai zo, kawai dai wani abin yake yi bai amsa kira na ba. Nace amma ai nayi masa saƙo sai ya bani amsa. Jamila dai ta shiga lallaɓani, muka tafi gurin sauka.
Fili ya cika tantsam Malaminmu ya nuna min ajin da aka ware mana mu 'yan sauka, na shiga dukkan masu saukar sun hallara kowa na cikin farin ciki masu hoto suna ta ɗauka. Na samu guri na zauna, Fatima Shu'aibu ta kalle ni. tace "Lafiya kuwa Rabi'a Abubakar naganki shiru. Na yi ɗan tsaki tare da faɗin ba komai. Na ƙaƙaro ɗan murmushi Malam Awwal ya ce za a bar Mutum uku su yi karatu ɗaiɗaya ya faɗi suna? Na tambaye ta cikin sanyin jiki. Fatima tace "A'a, amma dai nasan kina ciki. Nace ba lallai bane. Ina rufe baki yana shigowa. Ya ƙara tunatar da mu yadda zamu natsu sosai a gurin karatu da kuma yadda zamu fito cikin tsari. Sannan ya kira sunan maza biyu, Aminu Sani da Ashiru Ya'u. Suka fito, ya dube su yace akwai ta ukun ku ita ce Rabi'atu Abubakar na tashi da sauri na fita domin nasan cewa ina cikin waɗanda za a sa su yi karatu ɗaiɗaya, makarantarmu suna ji da muryata a ƙira a. Malam ya ce ku ukunnan kune zaku yi karatu, kuma Alhamdulillah kune kuka zo na ɗaya zuwa na uku. Dan haka ku zama cikin shiri na amsar kyautuka. Nan dai muka shiga murna duk da cewa bamu san waye zakara ba. Ni dai nasani bana wuce ta biyu ko ta uku a duk jarabawa ban taɓa yin ta ɗaya ba, yanzun ma ban yaudari kai na ba, na fi zaton ta uku. Shiko Aminu kowa yasan baya tsallake na ɗaya. Bayan an kiramu mun fita zuwa rumfar da aka tanada mana kujeru mun zauna sai na soma raba ido ina zan hango wani nawa. Na hangi .Abbanmu a rumfar iyayen yara cikin sabon yadinsa shi da Abba su Zuhra. Sannan na hangi Umma tare da wasu danginta na Kurna. Can a wata rumfar na hango Dangin mahaifina matan har da yaransu, amma damuwata ban hango masoyina ba. Duk sai naji raina yana ɓaci. Da aka fito da mu muka karanta fatiha da shafi biyu na baƙara sannan muka koma muka zauna, aka ci gaba da gabatar da abubuwa har zuwa lokacin da aka zo kan karatunmu. Ashiru aka soma kira aka ce ya zaɓi surar da ya ke son karantawa ya karanta. Ya zabi suratul Yasin. Da ya gama aka tsai da shi akan mumbari aka gabatar da shi a matsayin wanda ya zo na uku, aka bashi allonsa,sannan aka bashi kyautar sa ta musamman daga hukumar makaranta saboda taimakon Malamai gurin koyar da ɗalibai na ajin ƙasa. Sai kuma aka kira Aminu Sani cikin mamaki ya lalle ni, Nima haka domin dai na bayar ni za a kira. Shima dai bayan ya gama karatu an gabatar da shi a matsayin shugaban ɗalibai, ya kuma amshi kyautar yabawa da zuwa sahun bayan liman a lokutan salla a makarantar. Lokacin da aka kira ni sai da ta kusa sani ta taɓani domin takaicin rashin halartar Aliyu yasa komai ya saɓule min. Na tashi jiki ba ƙarfi na hau mumbari, an bani damar karanta duk surar da ta min, sai na samu kaina da karanta suratul Muhammad domin ina son ta. Ina faɗin Muhammadur Rasulullah! Sai na ji muryata ta soma rawa lokacin da na ji ɗaukacin gurin an amsa da S.A.W. Haka na kammala ciki zubda Hawayen da ba zan iya fassara dalilin zubar su ba. Guri ya ɗauki kabbara ga masu hoto da bidiyo amma babu sanyin zuciyata. Malam ya gabatar da ni a matsayin ɗalibar da ta zo ta ɗaya acikin kaf ɗaliban set uku da muka yi sauka. Sannan aka bani kyautar Shugabar ɗalubai wato Amira. Sannan aka bani kyautar ɗalibar da tafi kowace ɗaliba ladabi da biyayya ga malamai. Har zan sakko sai aka sake tsaida ni aka bani wata kyautar itama an naɗe ta, aka ce daga mijin da za a ɗaura mana aure da shi sati mai zuwa....

🖊️🖊️🖊️
*HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*

*NA*

*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*

_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_

*DOKA*
_Ban amince wani ya É—ora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_

*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*

*Page 14*
Chapter 5 · 0% Book details