Sashe 1
Hamshakiyar Uwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*HAMSHAƘIYAR UWA🧕ðŸ»*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_
*DOKA*
_Ban amince wani ya É—ora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_
*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*
*Page 11*
Maman Nana ta gyara zama sannan ta ce, "Ni dai a tawa shawarar abin da na ke ganin za muyi shine muje mu samu Hajiya uwarmu ce mu faɗa mata cewa muna son ta yi haƙuri da waɗannan al'adun yanzu zamani ake ciki. Shamaki ya yi sauri faɗin ai kina ba Hajiya hujja da zamani kin tashi duk wani bayanin ki na baya ya ɓare. Sanna duk bayani sai kin bata hujja. Maman tace To Kinji Maman Iman. Fatima tace aini nama rasa wane tunani zanyi domin duk ta inda ka zagayo Hajiya ta riga ta bi ta wuce, sai dai mu yi ta bakin Maman Nana Muje babu hujja ɗin, mu buƙaci kawai ta bar waccan al adar harma mu bata misali da Afra tunda ta san da maganar. Duk suka yi tsit kowa na nazari, suka maida kwallon su kan A'isha Ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce, Ni kuma nawa ganin kar muje mu tsaya mu fidda yadda za mu tare matsalar in ta faru. Misali shi Shamaki ko yaya ya samu matarsa sai ya faɗa mata cewa budurwa ce, in ma jini ta ke buƙata sai mu tanada shi mu aje. Batun girki kuwa sai mu rubuta mata a waya mu tura mata tana karantawa ta na yi da taimakon su Juma. Kunga mu fita a tunanin ya zata kalli abin kuma wane hukunci zata mana in muka tunkare ta da maganar. Kamar kowa zai amince da haka. Amma sai Shamaki yace ai bata taɓa bukatar ganin jini ba. Sannan da na mata ƙarya take take ganewa kuma ku kun sani hakan sai ya fi komai zafi a gurinta.Sai dai ɓargaren girkin in kuna ganin zata iya fahimta ita Babyn sai ayi hakan. Maman Umar ta ce Ni kuma nafi yarda da muje mu sameta mu ɗan latsa mu gani ko zata yarda. In munga alamun bazata yarda ba sai kawai mu watsar da maganar mu bi abin da addu'a. Dan abin ya zo a ƙurarren lokaci ne ai da mun saka ita yarinyar gurin koyon girki ko wata ɗaya tà yi." To haka dai shawara ta tashi ba tare da sun samu mafita ba, amma sun yanke cewa za su je gidan Hajiyar a jibi su ɗan latsa in da laushi sai su yi maganar. Maman Afra har ta fita ta dawo, tace da Maman Iman ki zo mana da kayan mu gani a gidan Hajiya. Maman Umar tace wane kayan me? Na DIJANGALA ENTERPRISE ƊIN da take ta koɗa mana. Mama Iman tace ok Insha Allah zanzo da shi.
Shamaki ya numfasa tare da faɗin Allah ka bamu mafita. Cike da sarewar gwiwa da kuma addu'a Allah ya fidda shi. Ya nufi gida. Kafin ya kai an kira Isha'i ya isa suna raka'ar ƙarshe, ya shiga ya suka ƙarasa sannan ya ɗora, ya fito ya tarar da mutane suna kjranshi kamar kullum. Ya na ta sallamar su har Buhari masinjan Ofishin A'isha Maman Afra ya miƙo mishi takardun masu kayan ɗaki. Ya amsa ya ce Malam Buhari zan duba a gida. Gobe sai kamin bayani. Malam Buhari ya ce akwai na Ujila a ciki wannan na saman tace ba su bi ƙa'idar kawowa ba, amma mabuƙata ne in da hali ka saka hannu kai da Hajiya ita dai ta saka. Yace to ba damuwa zamu yi magana da Hajiyar. Ya gama sallamar kowa sannan ya nufi gurin Hajiyar. tana jan carbi ya zauna gefe kafin ta kammala. Ya ɗauki takardar saman da aka ce ta gaggawa ce yana dubawa. Zai iya taimakon Yarinyar ko dan sunan Babynsa da take da shi, ya ɗarsa hakan a zuciyar sa. Maimaita Rabi Abubakar, bai san sunan mahaifin ta ba, amma yasan da wahala su zo neman taimako domin ya kula cewa mahaifin Baby mutum ne mai wadatar zuci. zuciyar shi ta kasa nutsuwa ya gangara can ƙasa gurin lambar waya ya duba lambobin da kyau, gaban shi ya faɗi, ya ciro yawa yana soma saka lambar sai ga sunan da ya sawa Baby ya fito. Soyayyata. Baya buƙatar sake sanin wata hujja iya wannan ta wadatar. Ya zare takardar ya aje gefe domin gagarumar matsala ce in har Hajiya ta ga wannan takardar, sannan ya ci gaba da duba sauran. Hajiya ta katse shi da faɗin "An shigo?" Ya dube ta da sauri na shigo sannunku da gida, ya gaishe ta cikin girmamawa ta amsa tare da tambayar kasuwa, ya ce Alhamdulillah. Sai kurum ya ji kamar daga sama ta ce "Ya kabaro 'yan uwannaka?" Ya zaro ido tare da faɗin na'am. Ta share zance da kallon takardun hannunsa, "Waɗannan kuma na menene?" Ya Kalli takardun cikin sanyin jiki tare da zargin wata cikin yan uwan nasa kenan harta sanar da Hajiya ko kuwa dai Hajiyar ce da kanta ta gano cewa sun yi zaman to ta yaya zata gano hakan. Yace, na masu buƙatar kayan ɗaki ne. "Wancan fa da ka aje gefe?" Yawun bakinsa ya tsaya cak, ya hura iska tare da ajiyar zuciya, takardar wasu ne da Maman Afra ta ce ba su cike ƙa'ida ba, na sakasu a gefe ne domin sai mun kammala da waɗannan. Ta tsura mishi ido. Wace number ka ɗauka a takardar?" Zufa ta karyo mishi cikin sauri yace ta Maman Afra Anty A'isha. ,ta ce in kirata inji Malam Buhari da ya kawo saƙon,to naji ƙiwar in tsaya binciko lambar ta a waya ta sai na ɗauka a nan. Ta saki ɗan murmushi mai sauti. "Kenan ita bata samu zuwa zaman ba?" A ina? Ya tambaya da sauri. dai dai lokacin da Juma ta shigo da sallama. Hajiyar ce ta amsa domin shi ya suma da mamaki gami da fargaba. "Juma tana gaida kai tunanin me kake yi ne?" Ta katse shi. Banji ba ne Juma sannu da ƙoƙari. Juma tace ina amsawa, hidima ta zo ai dole abubuwa sun yi yawa. Yace Ummm haka ne. Ya soma kiran layin A'isha. Ta ɗaga. Ya ce Maman Afra kina jina kuna lafiya? Tace lafiya lau,yace Malam Buhari ya kawo saƙo ya ce min kin sako wani Form na Ujila kuma kince muyi waya. Tace "Haka ne." To amma kinsan dai abin nan komai a tsare yake, zan maido miki ki aje shi su jira kamar yadda sauran mutanen suke bin layi, inhar muka fara irin haka za su iya sanar da wasu cewa mun basu agajin gaggawa kuma sai ki ga mutane sun fara zuwa irin wannan roƙon,ke kanki sai su ɓata miki tsari. Tace haka ne, kuma suma mutanen basu dawo ba, munyi da su zasu zo da mahaifin yarinyar yau amma shiru. Domin masu kawo takardar sunce marainiya ce, ita kuma takardar ta nuna cewa marasa ƙarfi ne. In sunzo sai a faɗa musu su jira, sai a saka su a jerin wani watan ko?" Yace haka ya yi suka yi sallama ya ɗago kai ya kalli Hajiya wadda ke faɗawa Azima abinda zata zuba mata daga jerin abincin da Juma ta jere. Yace Naman Afra tace a gaishe ku. "Muna amsawa, ta faɗa ba tare da ta kalli gurin da yake ba. Azima tace Yaya Shamaki me za a zuba maka?" Barshi Azima sai anjima bani dai robar ruwan can. Ta miƙo masa tare da faɗin "Kamar ya yi sanyi da yawa." Hajiya tace Kije ki ci abinci zai fi buƙatar mai sanyin domin naga kamar ya yi zufa. Shamaki yace ai kuma yau ba zafi kuma ga AC ma. Tayi murmushi mai sauti. Ya san wannan murmushin na Hajiya na tuhuma ne. Ya soma tunanin yadda zai ƙoƙarta a bagarar da maganar, ya san Hajiya tana son ƙure shine. Ya miƙe bari inje inɗan watsa ruwa. Tace to babu laifi. Ya kwashi fayal fayal ɗin. Sai tace "Ajiye su zan duba." Duk da faɗuwar da gaban shi yayi sai yace to,ya ɗan sake su kan ya kai ƙasa suka tarwatse, sai ya tattara ya haɗa su ya saka na su Baby a tsakiya.
Ya tafi yana shiga ɗaki ya soma faɗin Innalillahi wa'inna ilaihirra un. Ya zauna bakin gado ya ɗauki waya da sauri ya kira layin Maman Umar yace maman Umar wai in tambaye ki. Tace "Injinka." Waya sanar da Hajiya mun zauna Meeting? " Tasani! Na shiga uku?" Ta tambaya cikin gaggawa kuma atsorace. Yace yanzu na zillo daga falon nata kuma taƙi faɗa min ya akayi ta sani,na ruɗe fa ko dai acikin su Maman Nana akwai wadda ta yi subul da baki? Maman Umar ta ce babu,duk cikinmu Maman Afra ce kawai ta tafi, su gasunan kuma itama wallahi baza ta sanar da Hajiya ba. Yace to yanzu me zance mata tunda dole in koma yanzu dan akwai wata damuwar wadda tafi wannan ɗaga hankali. "Wacece ?" Ta tambaya cikin sauri. Baya buƙatar su sani dan haka ya ce ki share kawai, amma wallahi kamar in nutse bana cikin natsuwa yanzu haka. Tace kawai ka nutsu in zaka koma ka tanaji wata.maganar ko labari ɗankko mata zancan masoyinta wannan zai ɗauke mata hankali har mu tattauna yadda a kayi ta sani. Yace shike nan. Ya watsa ruwa cikin ƙarfin hali, ya saka Jallabiya mai gajeren hannu sanan ya fita zuwa gurin. Hajiya ta gama cin abinci tana shan shayi ya zauna idanun shi suna kan fayal ɗin, har yanzu suna inda ya barsu. Ya ɗarsa a zuciyarsa cewa har Hajiya ta gama dubawa ne ta ajiye ko kuwa dai dama shine ya ke tsorata kansa.