← Book details Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 45

Sashe 5

Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Cikin gaskiya da amana take ri'ke da Jawad komai yake so yi masa take yi, duk sadda ta je makaranta bata mantawa sai ta siyo masa abinda zai ji da'di, sun shaku sosai, da ke mai son jiki ne indai suna zaune to kuwa rabin jikinsa yana jikinta, sau tari Mk ke cewa "kina fama da kanki, amma sai ki kama katon yaro ki jingina wa kanki".
Murmushi take yi ta ce "Duka duka nawa ne adadin nauyinsa?"
Sosai ta samu saukin Ciwonta duk tashin da zai yi baya kayar da ita, kamar sadda take Nigeria, domin kwararren likitan ('kashi) take gani a asibitin jamiar, sannan zurfafa ilimin da take a fannin magunguna ya na taimakawa wurin sake sanin maganin da ya kamace ta.
Jawad yana ta karatunsa domin haziki ne sosai kamar Babansa bai yiwo shiriritar uwarsa ba, ko acan da suke da tsarin ilimi mai nagarta sosai yake ja, domin parfomance dinsa is very high hakan na farantawa iyayen nasa rai shiyasa komai ya ce yana so suke rige rigen yi masa.
Ba abin da yake damunsa sai rashin Jin muryar uwarsa a waya, tunda Mk yana ha'dasu da Hajiyar Bichi, da kuma Baffah, amma ya kasa samun layin Inna da Sa'adah ta ke amfani da shi, ita kuma tunda take ganin missed call din lambar waje ta kuma gane lambar Ingila ce sai ta yi blocking din layin shiyasa basa samun layin. kunyar Baffah take hana Mk tambayarta. Rannan Jawad sun gaisa da Baffa ya ce "Baffah ka bawa Mami wayar zan yi magana da ita".
Baffah da bai san Iyah ta rufe musu hanyar samunta ba ya ce "yanzu tana makaranta, Ni kuma bana gida ku nemeta a layinta ko na Innar ta.
Domin kuwa basu jima da barin kasar ba ta ce da Sumayya tana son waya, a satin ta turo mata da kudin waya mai tsadar gaske, tunda murna suke yi ta yarda zata ri'ke waya, alamun ta cire komai a ranta akan Mk, zata fuskaanci rayuwarta ta gaba.
Tsawon wattanni takwas kenan Jawad bai ji muryar uwarsa ba, a hankali sai abin yake 'dan ta'ba shi har abin ya fara bayyana a komai nasa, ya rage yawan surutu, ya daina walwala a tsakanin su, ya zama shiru shiru, sannan yafi son zaman daki fiye da falo.
Abin ya fara damun su mussaman Farida, ta yi tambayar duniya ya ce ba komai, Mk da ya gaji da yadda Farida take yawan damuwa da canjin Jawad ya ce "kifa daina damuwa, tunda dai ba wani abin aka masa ba, miskilin yaro ne na gaske, ni na yi mamakin yadda ya sake da ke tashi guda".

A marairaice ta ce "gaskiya akwai abin da yake damunsa domin ai ba haka ya ke ba, kamata yayi mu gano damuwarsa ko da cikin hikima ne".
Ranar alhamis da yamma, Mk da Jawad suna gida, yayin da Farida ta ke makaranta adalilin tana da lectures.
Cikin hikima ya hilaci Jawad akan ya ji me ya kawo changes din da suke gani a tare da shi, tunda bai fi sati da canjin nasa ba.
Cikin muryar kuka Jawad ya ce "Mamina! Na dade ban ganta ba, sannan tunda na zo bamu yi waya ba".
ya fada yana rushewa da kukan sosai.
Jikin Mk ya yi sanyi yasan Jawad ya yi kokari wattanni takwas da yawa, domin bai taba yin wata daya bai ganta ba, ko da yake hannun Hajiya duk karshen wata sai ya je ya yi kwanaki biyu.
Sannan tun farko yafi kulafacin uwarsa fiye da shi.
Jikinsa ya janyo shi yana fa'din ka yi shiru yau din nan zaku gaisa, ai da tun farko ka fa'da mini wannan ne damuwarka da tuni na magance maka ita.
Da kuka sosai Jawad ya ce "Am scared Malam".
Da mamaki sosai ya ce "Mai ya ke firgita ka?"
Last week na kalli wani firm a Fox movie (pendamic) yaron ciki ya tafi boarding school, shiru shiru bai ga mamar ta je ba, sannan baya samunta a waya Ashe she was died bai sani ba".
Kuka sosai ya sake barkewa da shi, zuciyar Mk ta dinga bugawa tamkar Sa'adatu ta mutu ne da gaske sune basu sani ba, domin yadda ya santa da Jawad bai zaci za'a shafe wannan wattannin bata nemi jin lafiyarsa ba.

Anya tunanin Jawad ba gaskiya bane?
Ya kasa cewa komai bare ya rarrashe shi wani irin abu ke masa yawo a jikinsa, ga dai sanyi a garin amma wata irin zufa ne ta fara karyo masa.
Ya dauko waya ya dinga gwada layin Inna amma sam baya tafiya.
Dabara ta fa'dowa Mk ya dinga lalubo lambar Zainab Ma'aji amma bashi da ita. Ya rasa yadda zai yi sosai Jawad ya firgita shi shima.
Da kyar ya shawo kan Jawad ya yi shiru bayan ya yi masa al'kawarin idan har ba'a sameta a waya ba, zai shirya musu tafiya Nigeria next week.
Duk kokarin Mk ya samu Sa'a a waya ya ci tura.
Tunda ko Baffah da ya mata maganar Jawad na ta cikiyarta ta daure ta kira shi su gaisa.
Kai tsaye ta ce "idan da rabon zamu gana zai dawo ya tarar da ni, Ni bazan kira shi ba, tunda ba shi da wayar kansa".
Daga Baffa har Inna ba wadda ya tilastata.
Mk da ya gaji da kiran lambar Baffah yana cewa tana Makaranta ko shi baya gida, sai ya kira layin Sumayya ya bawa Jawad suka yi magana yana ta mata kukan yana expecting Mami has gone.
Tausayinsa ya cika zuciyar Sumayya, ta dinga lallashinsa tare da al'kawarin daga yanzu zuwa kowanne lokaci zai ji muryar ta, tana nan cikin koshin lafiya.
Suna gama waya kuwa ta tura musu sabuwar lambar Sa'a.
Jikin Mk har bari yake wurin kiranta, amma sama da sau goma ta ki picking.
Tana kwance a dakinta tana kallon
Yadda Kiran ke ta shigowa.
A ranta tana fa'din har abada ban son jin ka, Jawad din ma na yafe maka shi".
Mintina goma sai ga kiran Sumaayya a layin Inna, ta dinga yi mata fa'da tamkar ta shigo ta wayar ta daketa, saboda itama ta kira layin nata bata dauka ba a tunaninta Mk ne.
"Iyah kalaman Jawad sun tayar mini da hankali tunaninsa mutuwa kika yi ake boye masa, idan kina haka har yanzu akwai kullin Mukhtar a ranki. Ki amsa masa waya Jawad ne zai yi magana da ke yafi sati yana cikin damuwar rashin ji daga gareki".
"Ni wlh Anty har Jawad din ma bana bu'katar jinsa ina masa addu'a, ina fatan ta zame masa garkuwa a ko ina yake".
Sumayya ta ce " To shi laifin me ya miki haba Iyah! Ki ji tausayi mana".

Da kyar ta shawo kanta ta yarda zata 'daga wayar.
Ba a jima sosai ba kuwa, 'Kiran ya sake fa'dowa wayarta.
Ta dauka ta yi shiru, sanin da Mk ya yi dabiarta ce ba zata fara yin magana idan ya 'kira a waya tun fil'azal sai bai wani damu ba, ya dinga yin sallamah, ya koma cewa hello nan ma shiru, ya mayar da wayar hand free, a tunaninsa jiyota ne ba ya yi. Yaayin da Sa'adah tsananin bacin rai ne ya kamata akan me zai mata magana, ya bawa Jawad din wayar mana.
Murya a sha'ke ta ce "Jawad!"
Ran Mk ya baci wato tana jinsa amsawa ne ba zata yi ba.
Amma a zuciyarsa ya samu nutsuwa kwarai da gaske da ya gane tana nan cikin koshin lafiya har ma tana da kwarin guiwar yin wulakanci, dan haka sai ya mi'kawa Jawad wayar a fusace.
Ya tsurawa Jawad ido yadda ya ke magana yana wani irin murmushi, ya sake kallonsa sosai yana ganin ba kammanin Sa'a tare da yaron illah wushirya da farcen hannayensa, inka dauke Wannan tamkar Mk aka raba biyu aka yi shi dan tsananin Kamar da suke yi.
Ya nisa ya tuno yadda Sa'adah ta tsaya a gabansa tana sheganta masa yaro, banda dai so baya shawara ai da bai kamata ya cigaba da son Sa'adah ba.
Chapter 5 · 0% Book details