Sashe 39
Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin kukan ta ce "Me yasa sai ita zaka aura? Me yasa na shafe shekaru hudu, Ina binka ka mini afuwa ka 'ki, karshe sai ka hukunta ni da auren wadda na tsana, Dan Allah baka ji a zuciyarka ka tozartani ba?"
Da sauri ya ce " Ni ban tozarta ki ba, domin 'auren da na yi 'kaddarata ne, wadda ko muna tare ba zan iya tsallakewa ba.
Ta ture shi ta ce "Ai kuwa zamu rayu a haka cikin damuwa, domin zuciyata ba zata huce ba, har sai ka yarda ka wulakantani, ka mini hukuncin da ya wuce laifina".
Ya sake rungumeta tsantsan tamkar zai mayar da ita cikinsa ya ce "Anya mutum yana tozarta zuciyarsa da rayuwarsa? Amma tunda shine abin da zaisa ki yafe mini, shine abinda zanyi ki dawo mini da nutsuwata, to na yarda na wulakanta ki, amma wallahi ba intentionally na yi hakan ba, ki yafewa masoyinki, kamar yadda na yafe miki, ko na tuna abubuwan da kika yi mini, a take nake jaddada cewar Ubangiji ya zama shaidar na yafe miki, ya kuma hane ni tunowa".
Da rawar murya ta ce "Ai ni ko ina son na manta din ba zai yiwu ba, a da kai din nawane ni ka'dai, kome zan yi maka na san ba inda zaka je ka kwana zaka dawo gare ni ne, amma yanzu fa? Zan dinga rabaka ne da wata muddin rai".
Ta karasa cikin kuka na sosai.
Shi kansa da ya tuna bala'in da ya shiga da ya ganta da Khalil ya gamsu ita din jarumace, domin shi akanta ba zai iya shanye abin da ita ta shanye ba, ya dinga ji har zuciyarsa yana taya ta Jin ciwon kaddarar nan da ta kutso musu.
Ya Dora bakinsa daidai kunnenta ya ce "Daga yau din nan ba zan sake maimata miki wannan kalmar ba! Ki ri'keta ta zame miki jagora a zaman da ubangiji ya kaddara zamu yi".
Ya nisa ya ce "Wallahi ban taba son wata halitta a doron 'kasa irin ki ba, Hajiya ce kawai ta fiki darajah a duniyata.
Ke nake yiwa so na 'kauna, so na sha'awa, so na burgewa, wani irin so nake miki da a kullum ina tuna ki sama da sau sabain a rana, ke kadaice nake tuna abin takaicin ki, amma sai na tsinci kaina da yin murmushi.
Ke kadaice kike mini iyashege ya burge ni.
Ke kadaice macen da idan na kalla sai na tsinci kaina da yawan ambaton Alhamdulillah!
Ke ka'daice macen da idan na ta'ba ki, ba ki mayar mini da marta ni ba, nake Jin bacin rai da tashin hankali.
Haka nan ke ce macen da nake fatan idan na tsinci kaina a aljannah na fara tozali da ita cikin jerin matayen da ubangiji zai bani.
Wallahi idan kika cire Hajiya ba wadda nake jin sonsu a raina da zuciyata irin ke da d'anki."
Ya nisa ya cigaba da cewa
"Ba zan miki karyar bana son Farida ba, ba zan miki karyar bata da wata daraja a idona ba, hakanan ba zance miki bana jin da'din zama da ita ba.
Sai dai idan har gaskiya zan fa'da miki! Ina jiye miki a wayi gari Farida ta yi kunnen doki da ke a zuciyata, koma ta zarta ki, domin ita din mai hakuri ce, mai kawaici ce, ta sani na fi sonki, amma bata ta'ba tayar mini da hankali akan hakan ba.
Zuciya a kirjina take kawai, amma bani nake sarrafa ta ba, ubangiji ne, Annabi kuma ya ce an gina zuciya da kaunar wadda yake kyautata masa".
Jikinta ya laushi irin tubus din nan, tana gasgata dukkan furucinsa, ta kuma gasgata tana da kafiya da kaifin harshe.
Tun ranar da ya auri Farida bata sake jin nutsuwa a zuciyarta akansa ba, sai yanzu.
Ta nisa ta ce "Shikenan! Ka yi ha'kuri zan gyara, zan kuma kiyaye, amma dai ka dinga mini uzziri, ni akan ka, bana iya sarrafa kishina, ka taya ni addu'a, ka kuma kara ha'kuri da ni, kar kuma ka bu'de kofar da wata macen zata kamo ni a zuciyarka".
Ta fa'da hawaye na zubowa.
Da sauri ya matsa ya rungumeta, yana jin tamkar an yaye masa wata katuwar masifa a rayuwarsa, yana jin wata irin salama tana mamaye dukkan zuciyarsa.
Ashe wannan 'daaurin da 'kirjinsa ya yi, ashe wannan fargabar da yake tsintar kansa a ciki, duk saboda rashin samun aminci ne daga wajen Sa'a?
A yanzu da ta yarda zasu zauna lafiya sai ya ji tamkar anyi masa bushara da gidan aljannah ne.
A fili ya dinga fa'din "Alhamdulillah! Allah kasa karshen tashin hankalin da zamu fuskanta kenan, Allah ka sanya wannan shine karshen jarrabawar mu".
Sau uku tana yun'kurin yin magana sai ta kasa, da ya lura da hakan sai ya ce "fill free, fa'da mini abin da ke ranki".
Ta tura baki gaba ta ce "Amma dai ka yi mini al'kawarin ba zaka ha'da ni zama da wata matarka ba, kuma yanzu na tabbatar waccan part din na Amaryarka ne".
Ya sake ru'ko ta sosai ya ce "Ban manta al'kawarin ba, amma sai nake ganin a waccan gidan da kika tsara yadda za'a gina shi, na miki wannan al'kawarin, yanzu kuma ai bashi bane".
Da rawar murya ta ce"kar ka hadani zama da ita, kar ka bari na dinga ganin mua'amalarku, zaka iya rasa ni a dalilin ciwon zuciya ko hawan jinin farat 'daya".
"Ina son ki koyi jarumta Sa'adah! Ina son hankali na ya tsaya a wuri daya, a yanzu da nake matu'kar mararinki, idan na rabaku zan halaka ne, Ina tabbatar miki zan tare ne a inda zuciyata tafi so, shi kuma adalci wajibi ne ka yiwa kowa.
Addinin musulunci! Addinin adalci ne, ubangiji ya sani namiji ba zai iya raba soyayyar matansa ta zama daidai a zuciyarsa ba, sai akace an masa uzziri anan, ma'ana bai yi laifi ba dan ya so wata sama da wata ba.
Har ilah yau Sharia bata ce dole abin da ka yi da wannan, idan ka koma wajen wannan ma sai ka yi mata irin wannan ba, domin ansan ba zamu iya ba.
Amma duk da hakan sai da Annabi ya yi ta wasiyyar kar mu jingine mace, mu ratayeta ita ba sakakkiyar mace ba, ita ba matar aure ba, dole a rabon kwana, muhalli, abinci da sutura ya zama daidai (eqaul).
Shari'ar musulunci ta yiwa mata gata da adalci, ta yadda ko ba ke aka fi so ba, to kuwa indai ana kan tsarin sharia din ba za'a ki wulakanta ba".
Ya numfasa sannan ya ce "ki min hakuri zaki koma wanccan gidan amma ba yanzu ba, ki bari nima na koyi jarumtar da zan kiyaye ka'idojin shari'a".
A hankali ta ce"To" ba dan tana so ba, sai dan kar ta cigaba da yi masa gardama yana ganin Farida ce mai biyayya kawai.
Ya tsura mata ido yana kallonta, sonta sai huda dukkan sassan jikinsa yake yi, cikin kasalalliyar murya ya ce "har yanzu baki huce da ni ba, har yau baki yafe mini ba?"
Murya ba amo ta ce "me yasa ka ce haka?"
"Har yanzu ban ji kin kira suna na ba, Na sani kuwa idan kina fishi ne kike gatsa sunana dan ki nuna mini iyakata. Idan kuma ba kya son shiga shirgina sai ki yi maganar ki ba tare da kin kama sunan ba"
Ta zuba masa wani irin kallon da yake kidima shi, tana murmushin da wurshiryarta ta bayyana, hawaye kuma ya zubo mata Ta ce "Malam".
Farin-ciki ya dirar masa fiye da wadda yake ciki, rabon da ya ji ta ambaci Malam a bakinta, tun ranar da suka hadu a gidan 'Karfi kafin komai ya tabarbare musu.
Ya sa baki yana lashe dukkan hawayenta da yake zubowa.
Ya yi gyaran murya ya ce "nan da kwanaki shida zaki tare, Ranar juma'ah mai zuwa.
Yanzu mu je ki za'bi funtures din da kike so, masu harkar 'kawata gida, za su zo su shirya miki".
A hankali ta ce "Na gode sosai! Amma ka barsu, domin yanzu ina da kishiya idan ta gane haka na zo, zata samu dama akaina".
Ya kalleta ido cikin ido tsawon lokaci sannan ya ce "Na ta'ba rokon ki a shekarun baya ina so ki ji a ranki nima tamkar Sumayya nake a wurin ki, ashe baki dauke ni hakan ba?"
Ta kasa bashi amsa.
Ya ce "Wallahi Sa'adah ko wani kika aura ni zan miki komai da uba yake yiwa yarsa domin Baffah zan yiwa, lokaci ya yi da zai huta, a yanzu abin da nake ji game da shi ba wai kallon mahaifinki nake masa ba, kallon nawa uban nake masa, domin ya mini abin da na tabbatar uba ne kawai zai yi wa 'dansa.
Na yarda da maganar da ake cewa ko baka haihu ba, idan ka yi alheri ga marayu da masu rauni, ka zauna da mutane lafiya, ka yi hakuri da cutarwarsu, to ubangiji sai ya turo maka wadda zai yi maka abin da ko 'danka ba zai maka ba, haka nan idan kana da zuri'a ubangiji zai baka wadda zai jibanci lamarinsu ko da baka numfashi".
Baffah uba na ne, da ubangiji ya bashi, komai zan yiwa jinisa a duniya ban biya shi ba, dan haka ki yarda da ni, ko ba aure a tsakaninmu Ni din mai yi miki komai ne, mai kuma tsaya miki ne a ko Ina".
Ya yi shiru! Sai kuma ya cigaba da cewa "wanccan gidan da kike magana akai tun ranar da kika ce mini filin ki Baffah ya siyar ya bani ku'di, zuciyata take ta bugu akan na baki shi kyauta, sai dai bani da halin bawa Farida irinsa, dan haka na bawa Jawad shi, na je an canja takardun, sunan Jawad ne akai.
Idan na gamsu sosai zan iya ware miki gida, shikenan sai ki koma gidan d'anki kafin na samu damar da zan sake yi muku wasu gidajen a jere amma ko haraba ba zan ha'da ku ba".