← Book details Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 45

Sashe 25

Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ya daga kai sama ya ce "Allah ka zame mini shaida, na yi iyakacin kokarina, na mikata inda zata sami nutsuwa amma basu fahimce ni ba, Allah ka sani ban yi fishi ba, Ina dai roka mata sassauci kar abarta da zabinta, a bata mafi alheri."
Ya sauake idonsa a akanta da duk jikinta ya mutu, kunyar 'karar da ta kai shi na kamata, ba ita kadai ba har Sumayya, Innace kawai take kan ba'kanta gara da suka yi hakan.
Ya nisa ya ce" ki cewa wadda kuka aminta da shi, ya tura iyayensa Gogel wajen Babanku Ayuba, ni ba sai sun zo mini ba".
Ya mike ya barsu da sanyin jiki.
Yana fita kuwa, ya kira Mahmoud ya zo ya same shi.
Ya kalli'Karfi ya ce "Mahmouda Ina ba'kin cikin sanar da kai cewa duk yadda nake ganin Zan shawo kan Iyah akan al'amarin ta da Mutari abin ya ci tura, na rasa inda zansa kaina kunyar yaron nake ji. Yau din nan sun je can gida sun fa'dawa Yayana Akan na matsa sai ta auri Wanda ba shi take so ba, na samu umarnin akan lalle na barta ta tura musu iyayen wanda take so".
Takaici ya kama Baffa ya kasa cigabada maganarsa.
Sai ya nisa ya ce "Bazan iya fa'dawa Mutari wannan maganar ba, domin ya riga da ya gamsu na isa da ita, to gashi sun hade min kai, sun nuna mini *HALIN YAU* na rashin girmama ra'ayin magabata. Dan haka ka fa'da masa ya yi hakuri dan Allah, yau ma zan sake maimatawa da ina da wata yarinyar da na bashi, in fatan ubangiji ya albarkaci Jawad da ya ratsa a tsakanin mu".
Jikin 'Karfi ya mutu kwarai da gaske! Kenan biyu babu zasu yi? Mk ka'dai zai iya sadaukarwa da Sa'adah, amma matu'kar ba Mk ba kuwa zai shiga ya fafata da kowanne mahalu'ki dan ya tabbatar ya hana shi daukarta, a yanzun ma abin da zuciyarsa take kissima masa kenan indai yana raye bai kamata ya bari ta subucewa Mk din ba.
Ya riga da ya hakura da ita, badan ya daina sonta ba, sai dan ya san ubangiji ya dubi girman hakurinsa ya bashi mace ta gari, matar da ako ina zai bugi kirji ya ce ta gari ce, matar da take sonsa da dukkan zuciyarta, take mutuntunta shi, take hakuri da dukkan matsalolinsa, ya sani ba iyawarsa ba ce, horewar ubangiji ce.
Ya nisa ya ce "Baffah mu bamu sare ba, har sai ranar da muka ga an daura mata aure".
Ka cire kanka cikin maganar kawai, ka barmu da ita, yanzu ne zamu kafa alkalamin mu cikin tawada, jikina yana bani bakin alkalamin mu bai bushe ba".
Baffah ya nisa ya ce "To Ubangiji ya dafa muku, ya yi zabin alheri".
Kwanaki uku kenan 'Karfi ya kasa fa'dawa Mk sakon Baffa adalilin har yanzu jikin nasa ba kwari, jiyama sai Mahmoud din ne ya mayar da Jawad makaranta, da hutun ya kare a jiyan.
Sai da aka sake yin kwana biyu'Karfi ya tarar da Mk har gidansa suka tattauna sakon Baffah! A farko maganar gaba'daya rikicewa ya yi, amma 'Karfi ya shawo kansa ta hanyar fa'din ina tare da kai Bichi banji a raina zamu rasata ga'badaya ba, fatana mu yi addu'a, mu bi hankali kar kuma mu sare, mu yi ta binta tunda mu muke nema, sannu a hankali har mu samu mu damketa".
Mk ya nisa, ya ce" tunda na rabu da yarinyar nan wani abu mai tsananin nauyi ya tokare ni a kirji da makoshi, har yau din nan bai fada min ba, sai kara girmama da abin ya yi a yanzu da nake ganinta da wasu, wai ya zanyi ne? Wallahi na fara debe kauna da rayuwa domin Ni ka'dai nasan azabar da nake hadiya mussaman ace dare ya yi lokacin da zan samu na huta, a lokacin ne nafi shiga tasku bana iya barci, yanzu kuma abincin ma baya shiga".
'Karfi ya nisa ya ce "ka daina damuwa komai zai wuce, idan ka ga ka rasata, to kawai ka dauka babu alheri ne a kasancewar ku, ubangiji ne ya karar da zaman. Sai ka duba ai ka rayu shekaru bakwai babu ita, kuma baka mutu ba, idan har ita zata iya yin jarumtar hakuri da kai gaba'daya, bayan ta sha dukkan ba'kin ciki da tashin hankalin son komowa gareka, to kuwa kaine ka fi cancanta da irin wannan jarumtar".
Mk ya yi shiru yana gasggata Sa'a ta fi shi jarumta, tunda har zuciyarta bata buga adalilin aurensa ba, don kuwa shi yanzu ya gama yin imanin duk ranar da aka daura aurenta da waninsa tabbas a ranar ajalinsa zai sauka adalilin bugawar zuciya, ko hawan jinin da ya zarce kima.
A raunane ya kalli 'Karfi ya ce "Ai ita mace ce, ubangiji ya sanya musu wani irin karfin jure dukkan kalubalen tarbiya da kishi, amma mu ba a bamu wannan ba, namiji karfin gwagwarmaya aka bashi, da karfin tsayawa iyalinsa akan dukkan bu'katun yau da kullum".
'Karfi ya nisa ya ce "Hakane! Abin da nake so yanzu da kai shine, ka dora jarumtar gwagwarmaya a zuciyar ka, tunda ka gamsu muna da karfi da juriya anan bangaren, to idan kuwa hakane, zamu yi gwagwarmaya har mu samu mu kwato abin da yake namu ne".
Tun daga ranar suka fara yiwa Iyah wani irin naci, mai cin rai.
A Rana su kanje sau uku, kowanne lokaci zuwa suke yi, tun Inna tana ganin zasu gaji su daina, har ta fara ganin ba zasu gaji ba, domin kuwa kullum zaryar kara gaba take yi, ba baya ba.
Haka gidan Sumayya, hatta Idris a yanzu tausayin Mk yake ji, shiyasa ya fa'dawa mai gadin gidan matu'kar Mk ne suka zo, to ya bude masa gate kai tsaye.
Tsawon sati uku ana wannan zaryar bai fi kuma sau biyar suka samu nasarar ganinta ba, a cikin zuwa fiye da arbain.
Duk inda hankalin Mk yake a tashe yake, yayin da Mahmoud yake ta karfafa masa guiwa duk da shima bai yi zaton kafiyar Sa'adah ta kai haka ba.
Ranar alhamis da hantsi suka isa gidan Sumayya, sun shafe lokaci mai yawa a zaune, sannan ta fito, sanye da hijabi fuskar nan a daure, ta iso, da alamu tilas aka yi mata.
Dr Karfi ya mike ya na fa'din barka da fitowa sarauniyar mata. Ta yi shiru tamkar ba da ita yake ba, domin ta lura shine jagoran wannan nacin da suke mata kamar ba'kaken mayu.
Ya ce "Allah ya huci zuciyar giwa kuma gimbiyar Mata, ba zamu gaji da bada hakuri ba, ba kuma zamu gajiya ba, har sai kin dawo mana da walwalar da ta yi mana tutsu. Ki yi ha'kuri, ki zo ki haska mana zuciyar aminina da gidansa gaba'daya, Ina rokon ki, badan mu ba, sai dan ubangijin ki, ni shaida ne na irin tsananin son da yake Miki".
A tunzure Sa'a ta ce "ka dinga jin tsoron ubangiji Baban Dady! Sai yanzu! Sai yanzu! Sai yanzu zaka tirsasa ni, me yasa a wanccan lokacin baka tirsasa shi ba, me yasa ka bari na wulakanta, na tabbatar ba zaka so ayiwa kanwarka abin da aka yi mini ba. Amma yanzu da yake farin-cikin abokinka kawai ne a gabanka, ka na'de 'kafar wandon yi mini dole, kasan ina jin nauyinka, akan me zaka takura ni irin haka, an ta'ba yin aure dole, to ko Baffah ma na tabbatar masa bana son wannan mutumin, kaima na fa'da maka, ka sakar mini mara, na ro'ke ka".
Ta karasa cikin kuka sosai, Dukkan su sun yi laushi, mussaman Mk da yake jin tamkar ya hadiyi zuciya saboda yadda yake jin ciwon yadda take fadin bata sonsa, a gaban kowa.
Mahmoud ya kalli Agogon hannun sa, ya ce "hakuri zaki yi, ba yadda zamu yi ne, ki 'kara hakuri, ubangiji zai baki ladan masu hakuri.
Ya kalli Mk ya ce " ina da appointment nan da mintina talatin a makaranta, zan wuce, idan ka gama kawai mu hadu a gidanka bayan azahar".
Daga haka ya fice da sauri, da mukallin motar Mk a hannunsa.
Tana tsaye tamkar soja. A hankali Mk ya ce "zauna mana Dan Allah".
Bata yi musu ba, ta zauna.
Chapter 25 · 0% Book details