Sashe 44
Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Sosai Mk yake ji da yarinyar nan. Aka sanya mata sunan Hajiya Babba! Wato Aisha, Farida ta sanya mata Amira.
Mafi yawa Mk ya fi yawo da Amir da Amira tun Sa'a na jin wani iri har ta hakura ta gane ba dan komai bane illah ya samu Amir ne bayan ya dauki lokaci babu haihuwa, ita kuma Amira only girl ce.
Jawad ya kammala karatunsa na sakandire, ya wuce kasar Canada yana digiri dinsa akan engineering.
Haka rayuwar ta cigaba da gudana cikin nasarori da kuma kalubale kala-kala.
A yanzu haka Mk ya samu appointment ya zama minister ilimi na kasa, yayin da ya nada Mahmoud mai magana da yawunsa.
Yana Abuja tare da Farida a dalilin itama ta samu transfer a wurin aikinta zuwa Abuja.
Da kuma amincewar Iyah amma tana da wurinta a gidan, idan anyi hutu suna zuwa ita da yara har da Hajiya.
Tana kano tana cigaba da zurfafa iliminta, a yanzu haka digiri na uku take duk a fannin shari'a.
Duk week end din duniya sai ya biyo jirgi ya zo, sai dai idan baya ' kasar.
Ta da'de da tarewa a gidan Jawad, haka nan Mk yana kan yi musu gini da ya zarta wadda take ciki, a jere.
Ta dauko Hajiyar Bichi suna zaune tare cikin girmamawa.
A yanzu da shekarun hankali da girma ya zo mata sai ta gane ba abu mai Dadi a rayuwar mace irin samun miji na gari mai adalci, ita da kanta idan ta tuno ta'barar da ta yi a baya sai ta ji kunya ta kamata, ta kuma godewa Mk domin ba abin da bai mata ba, ta kuma gasgata shi da ya ce shi din tamkar Sumayya ne a wajenta ba wai miji kawai ba, ba abin da bai yi mata, yana kuma tsaye akan dukkan bu'katunta, sannan yana hakuri idan borinta ya tashi.
Haka nan ta gasgata shi da ya ce Baffanta Babansa ne ba nata ba, domin ba abin da bai yi musu ba, ya rushe gidansu ya zamanantar da shi, ya kai iyayenta sun sauke farali.
Itama ta je, ta koma Umrah, duk da bata aiki kuwa.
Ranar juma'ah ta yi ferfesun naman rago ta kaiwa Hajiyar Bichi dakinta, sannan ta ce "Hajiya zan je na gaida su Baffah".
Da murmushi Hajiya ta ce "Ki gaishe su Sa'a, Ubangiji ya yiwa kokarinki albarka, yasa kema naki 'Ya'yan suji 'kanki.
Ta isa gidansu ta tarar da iyayen nata zaune a falo sun yi shar da su tamkar tsufa bai cimma musu ba, ta zauna tana cewa "wayyo Baffahna".
Da wata irin 'Kauna ya ce"sarkin hakuri, giwar mata, mowar 'ya'ya".
Ta murmusa ta ajiye masa kwanon naman a gabansa.
Inna ta ce "Danma dai uwa mafi uba ko da uban sarki ne".
Cikin tsokana ta ce"Ai ni Baffah kam ya wuce ki Inna, sai dai ki yi 'hakuri kawai".
Ta mike ta shiga kicin din da yanzu yana cikin falon ta debe bowls ta zuba musu, suna ci, suna saka mata albarka.
Ta hada kan kayansu kananu ta wanke su tas.
Ta yiwa Innah ganeral sanitation duk kuwa da ta daukar mata Yar aikin da take zuwa ta yi mata shara da wanke wanke.
Amma duk da hakan duk karshen wata sai ta zo ta yi mata gyara na mussaman.
Baffah ya tsura mata ido yana godiya ga Ubangiji, da ya arzuta shi da samun 'Yaya mata, ya tarbiyaantar da su har ya aurar da su, yanzu gashi sun zame masa gata, sun janyo masa mazajensu suna ta hidima da shi, ya yi Imani ko yana da 'yaya maza ba lallai su yi masa abin da Mukhtar daIdris din Sumayya suke yi masa ba.
Gashi kuma ya'yan nasa sun haifa masa 'Ya'ya takwas maza, domin nassin al'kura'ani ya nuna jikanka 'danka ne.
Madallah da iyayen da basa zaben jinsin da suke son su haifa, suke godiya ga Ubangiji ta hanyar tarbiyaantar da ya'yansu mata cikin adalci da tausayi.
Sa'a ta koma gidanta, iyayenta suna saka mata albarka da nemawa zuri'arta tsari daga rudin *HALIN YAU*
Wani week end ya zo Kano, suna zaune a falo ya kalleta ya ce "sai nake tuna shekarun baya da kike ce mini kin yi mafarki, kin zama big Madam, na zama Alaji, na 'kera mana mansion"
Itama ta ce "Na tuna amsar da ka ke bani cewar banga ka 'kara Aure ba?"
Ya fashe da dariya tare da janyota Yana cewa 'dukkan mafarkin ki Allah ya tabbatar miki su, kin zama big Madam abin alfaharin kowanne miji, tashi muje mu yi nafila mu sake godewa Ubangiji da cika ya mana ni'imominsa.
Wani watan Ina son dukkan ku mini rakiya na gano 'Dan-iyah a Canada har da kannesa zamu tafi".
Ta ce "Jawad bai zama 'dan Malam ba Sai D'an Iyah?"
Da murmushi ya ce "shi ya ce mini sunan da zai sanyawa jirginsa kenan 'Dan-iyah Airlines*.
Yana kuma fatan ya samu sarautar 'Dan-iyan Bichi.
Zan fadawa Baban Khairat zamu tafi da ita, ta gano mutumin nata, wata'kila dai zumuncin Jawad da Khairat nan gaba ya bada mamaki".
A zuciyar Sa'a sai fata take Allah ya tabbatar da wannan hadin.
Basu Jima da dawowa daga Canada ba, Sa'adah ta dinga jin sha'awar samun karamin 'da, ba tare da ta yi shawara da kowa ba, ta ziyarci asibiti ta cire loop. Alokacin shekarun Mahmoud Junior uku.
Ai kuwa cikin ikon Ubangiji sai gata da ciki, ta kame bakinta ba wadda ya sani ko shi Mk din sai da ya girma sannan ya fahimta, ya dinga rawar jiki yana Sanya mata albarka, Fa'di yake "da gaske tsohon nan yake yi Iyah da ya ce ke ce uwar 'ya'yana daure ki ta haihuwa na miki alakawari ba zan taba gajiya da ke ba."
Addu'a ta dinga yi akan ta sami baby girl, cikin kudurar Ubangiji kuwa sai gashi ta samu yanmata guda biyu wato 'yan-biyu, murnar da ta yi ba ka'dan bace, dukkansu kuma ita suka biyo wato identical twins ne, fatarsu mai matu'kar kyau ta dan yi duhu kadan. Rabi'atu (Janan) Salma(Jadida).
Wani irin so Mk yake yiwa 'dinsa shi da kansa ya tabbatar tsananin kamar da suke yi da tauraruwar zuciyarsa ne.
*Shekaru Sha biyar a gaba*.
Girma ya fara kana Mk da matayensa, suna zaune cikin farin-ciki mai yawa, tuni ya kammala shekarun takwas dinsa na minista, ya dawo kano ya cigaba da aiki a jamiarsa a matsayin babban professor. Yayin da Sa'a ta zama babbar lauya mai zaman kanta, ganinta ma sai da hanya, saosai ta yi tsada, sai dai ta kfa gidauniyar tallafawa matan da ake xin zarafinsu mussaman'kananu.
Tun daga Kan ya biyu ba a sake haihuwa a gidansa ba, tun yana mita har ya gaji mussaman da suka girma, har kuma matar Jawad ta fara Haifa musu jikoki.
Farida tana nan tana rayuwa Kan magani, yaranta sun girma har yau da Amir bai ji a bakin Sa'a ko Mk asalin mahaifiyarsa ba, amma mutane sun sa ya gasgata Sa'a ce ta haife shi, Amma Bai ta'ba nunawa Farida cewar ya sani ba, haka nan duk abin da ya shafe shi kai-tsaye Farida ce akai da kuma ita ake jingina shi.
Engr Kabir Mukhtar Kabir(Jawad)
Zaune a ofishin gidan radio na muryar Amurka, (V.O.A). Yana amsa tambayoyin da shahararren 'dan jarida kuma amininsa Muhsin 'Yargaya yake masa, saboda irin nasarorin da ya cimma a rayuwarsa cikin 'karancin shekaru irin nasa.
Jawad ya murmusa shi da kansa ya tabbatar yana cikin jerin matasan da suka cimma burin rayuwarsu a cikin shekarun da basu wuce na samartaka ba.
Farko shi shekarunsa talatin da biyar, amma babban ma'aakaci ne a ma'aikatar 'kera motoci na Amurka (ganeral motors), sannan 'dan-kasuwa ne kwarai domin ya zuba hannayen jari a kamfanin 'kera jiragen sama daban dabana a kokarinsa na samun cikar burinsa na siyawa uwarshi jirgi, domin har yau din nan burin yana nan kusan tare yake girma da abinsa.
Sannan shi din maigidanci ne da yake tare da iyalinsa cikin kasar Amurka, matarsa Khairat da Yayansa mata biyu Sumayya (Nana) da kuma Sa'adah (Iyah).
Sannan wakili ne a kamfanin motar kasar Nigeria (fijo) da yake jahar Kaduna da ake ta kokarin farfado da shi.
Ga'badaya ya canja ya girma ya zama tamkar Mk a lokacin da yake cikin shekaru irin na Jawad din.
Muhsin ya jefo masa tambayar menene sirrin nasararsa?
Ya murmusa ya ce bana haufi tsayuwar iyayena wajen karatuna, tarbiyata, da kuma koya mini neman na kaina, tun Ina karami sun taka muhimmiyar rawa. Sai Kuma addu'a da suke maka.
A Ina ka samo 'Dan Iyah da yanzu kafi amfani da shi, yake a matsayin saka hannunka?
Ya sake murmusawa ya ce saboda mahaifiyatane inkiyarta ne.
"Fara bamu tarihinka a takaice."
Ya zayyano tarihinsa a takaice.
Muhsin ya ce "Wato dai kana da kanne da yawa".
Ya ce "mu bakwai ne a wurin mahaifinmu"
"Kaine na nawa, kuma dukkan ku kun kasance daga iyaye guda?"
"Ni ne babba! Mu biyar mahaifiyarmu ta haifa, sai guda biyu na abokiyar zamanta".
Muhsin ya yi dariya ya ce "Ashe yan boko ma suna yin poligamy?"
Cikin dariya 'Dan Iyah ya ce "saosai ma kuwa domin a yanzu haka ina daf da daukan second wife, sai dai daga kanta in sha Allah na rufe kofa domin Khairat mai kishi ce irin Maminmu".