← Book details Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 45

Sashe 29

Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Takaici a zuciyar Sa'adah tamkar ta rushe da kuka, ta ki sakar masa hannu dan ta nuna mata itace matarsa. Sannan dan ta tabbatar mata ita bakuwa ce yanzu a wurin Mk, shine take mata iso a gabansa?
Ta daure ta hadiye damuwarta ta yi kamar bata ga hannuwansu a sarke ba, ta cewa Farida "Sannun ki".
Daga inda take tsaye ta kalli Mk ta ce "ya ya jikin?"
Daga haka ta tsuke bakinta, tana karanta duk addu'ar da ta zo bakinta, tabbas Mk ne ya wula'kanta ta saboda ya nunawa Farida ita ba wata tsiyar ba ce. Shiyasa ya ki zame hannunsa da yake cikin nata.
Amma ai ya yi da yar halak.
A hankali Mk yake kallonta ta kasan ido, yana nazartar yadda take kokawa da fishin da ya ke yun'kuro mata.
Cikin hikima ya zare hannunsa a hannun Farida, gumi sai yanko masa yake yi.
Da sauri Farida ta 'kara karfin A.C da gudun fanka, saboda zufar da taga na karyo masa wadda kawai ta fargaba ce. A ransa ya dinga nazarin anya zai iya jarumtar ri'ke mata biyu kuwa? Saboda yadda ya dinga zullimin kasancewarsa a gabansu a lokaci 'daya.
Mk na wanna tsinkayen ya ga Farida ta ajiye kwandon hannunta tabbacin ta fasa tafiyar kenan.
Wato duk ha'kurin mace ta iya shu'umanci indai akan kishi ne?
Yau ya gasgata hakan domin ko kaffara ba zai yi ba, idan ya yi rantsuwar saboda Sa'adah ta 'ki tafiyar.

Dan haka ya yi kicin kicin da fuska, ita kuma sai kokarin yi masa fifta take yi.
Yayin da Sa'adah da Zainab suke ganin ikon ubangiji na yadda Farida ta kankane komai, Zainab da Mk ne suke mamakinta. Yayin da Iyah ta san dama Farida zata yi abin da ya fi haka.
Abbas ne ya leko daga bakin kofar ya ce "Farida ina ta faman jiran ki, so nake na yi maza na kai ki na dawo, kafin su tafi kar abar shi ba kowa, Hajiya ta tafi tun dazu, zan biya na dauko su Anty Amina Kuma".
Ai kuwa ta ce "je ka dauko su kawai, idan Akil ko Ahamad sun zo, sai je su dauko mini motata, ko kuma na fita na hau adaidaita sahu".
Abbas ya yi sakare yana mamakinta a ransa tare da cewa "Ah adole ita ba zata basu damar ganawa ba, duk da dai bata nuna bacin rai ko damuwa ba.
Sai a lokacin Mk ya ce" amma kin san ban son Ahamad yana hawa motar ki saboda ba ya tuki da nutsuwa, Akil kuma yana shago sai dare ya fara jah yake zuwa".
Ta marairaice ta ce "Ba damuwa sai na hau adaidaita sahu".
"A a bana so kin sani, bana so".
Ya sake sassautawa "ya ce ki je ya kai ki, ana idar da Sallar isha ki rufe gidan, sannan ki taimake ni ki sha maganin ki please".
Ya fa'da cikin sigar rarrashi da kulawa.
Amma ta yi mirisisi ta ki tafiya, lamarin da ya sake dagula lissafin Sa'adah, wai yau a gabanta wata macen take nunawa ta fita son Mk, ta fita kusa da shi.
A gabanta shima ya ke nunawa wata macen tattali da kulawa? Wannan shine duniya rawar yanmata.
Shirun da Farida ta yi ya tabbatarwa da Mk bata amince bane, ya kalleta a tausashe ya ce "Ban son ki wuce lokacin shan maganin ki ne, gobe idan zaki taho, ki taho da shi, sai ki yi ta zamanki, amma yanzu taimake ni ki je ki kular mini da lafiyar ki".
Nan ma ta yi shiru, Mk ya ce "shikenan ai, tunda so kike mu kwanta gaba'daya".
Dakin ya yi shiru na mintina uku, Zainab na mamakin irin wannan al'amarin, ta kasa cewa komai duk da bakinta cike
yake da tarin maganganu, da suke bu'katar fashin ba'ki.
Irin kallon da Farida take yiwa Mk da idanuwanta masu maiko ya sa
nan da nan zuciyar Sa'a ta hauro, ta kalli Abbas dake bakin kofa yana tsayawur jiran Farida, amma ganin Sa'adah yasa ta fasa tafiyar dan kar ta samu damar 'dagawa mijinta hankali 😀
Ta ce "Uncle Abbas"
"Na'am Anty Sa'adahtu".
"Tafiya zan yi, kuma akwai sakon da zan fa'da masa, zo ka ri'ke mini shi zuwa waje na mintina kadan".
Da sauri Abbas ya shigo yana cewa "daga nan ma na zagaya da shi, dazun nan likita ya gama ce mini kwanciyar ta yi yawa, ya dinga yin atisaye ko a cikin dakin nan ne".
Ya isa jikin gadon ya mikawa Mk hannun, ya dago shi.
Ya sunkuya ya janyo masa takalma a a kasan gadon ya saka sannan ya mikar da shi, suka fita a hankali.
Zainab ta dinga jin wani irin farin-cikin iyakar da Sa'a ta nunawa Farida.
Sun Jima da fita sannan Sa'adah ta dauki handbag dinta zata bisu, Farida ta ce "Gogel ko zaki fitar masa da kujera, jikin nasa ba kwari har yanzu".
Da sauri Sa'adah ta saki murfin kofar, ta dawo ta zuba mata ido, sai kuma ta sassauta fishinta tace "Da a ce Sa'adatu Kika kira ni da shi, da ko kula ki ba zan yi ba, sai dai na ce miki to, ko da ba zan yi abinda kika ce din ba, sai dan na nuna miki am matured now. Amma tunda Kika 'Kira ni da Gogel zan tabbatar miki har yanzu waccan Gogel din ce dai da kika sani, Billahillazi ki fita a idona, kada ki sake yun'kurin shiga tsakani na da shi, ko ki nuna mini ga yadda zan yi masa, if not kin dai sani. Ba zai zamewa Iyah Basiru komai ba wajen nuna miki har yanzu ina cikin shekarun da ba a mini kan kara ban yi na ice ba".
Daga haka ta juya tana cewa "Zainab zo muje, idan na gama sai mu wuce ba sai na dawo nan ba".
Suka fita bayan Zainab ta cewa Farida Allah ya Kara lafiya.
Sun zo inda su Mk suke zaune, Zainab ta yi masa addu'ar samun lafiya mai dorewa ta yi gaba, haka Abbas ma ya mike suka basu wuri.
Sa'a ta zauna tamkar gaske magana zata yi masa, amma ban da cika tana batsewa ba abin da take yi.
Ta tabbatar Farida na hango su ta windo, shiyasa ma da ta zata zauna sai ta juya baya ta yadda ba zata ga fuskarta, ba haka ma Mk bayansa zata hango.
Banda son ta nunawa Farida dan taki tafiya ba shine dalilin da zata hanata magana da shi ba, da bata tsaya kula Mk ba, tunda agabanta yake nunawa Farida soyayya har ya na lallaba ta.
Dukkansu kowa fishi yake da dan'uwansa, domin ganin ta da ya yi da Khalil ba karamin kidima shi yake yi ba, dan haka, ya danne zuciyar sa ya ki mata magana.
Amma dai a kasan ransa sun bashi dariya ita da Farida kwarai da gaske.
Mintina ashirin na cika ta tashi ga mamakin Mk ya ga ta mi'ke tana murmushi ta fito da wayarta ta Kira Zainab tana fa'din idan Abbas na kusa ki ce masa ya zo mun gama".
Aikuwa sai da Abbas ya zo, ta tafi bata ce da shi uffan ba, sai Abbas ta yiwa sallamah da fatan samun lafiya ga marar lafiya. Mk ya bita da ido yana ganin yadda take tafiya, sai ayyanawa yake yi ko sai yaushe zata daina rikicin gan-gan?
Ban da karfin halin Sa'a ya zata zo ta tarar da mace da mijinta, sannan ta ce sai ya fito waje sun yi magana alhalin ba maganar zata yi ba, kawai son rikici ne da son nunawa Farida karfin da take da shi a zuciyar sa.
A mota Zainab ta ce "Tabdi yau na ga kishi, ashe haka abin yake?"
Sa'a da dama kiris take jira sai kawai ta fashe da kuka.
Jikin Zainab ya yi sanyi sai kuma ta ce "Menene abin kukan kuma? Duk irin jarumtar da Kika yi".
Ta kasa magana illah kukan da ya ki yankewa, tana ta hararo hannun Mk a cikin na wata a gabanta kuma, tabbas har ta mutu ba zata daina kokawa ba.
Da kyar Zainab ta shawo kanta, "kin samu labarin auren Halima next week?"
Murya a dakushe ta ce " a a"
Zainab ta ce "to ai ke ce kinki shiga cikin group din mu na old girls a WhatsApp".
A sanyaye sosai ta ce "Bar ni kin ji, inace ga abin da biyewa 'kawayen ya janyo mini, kina kallon yadda wai magana da Malam ya zama sai an mini iyaka. Ta rushe da kukan da ya sanyaya jikin Zainab, itama idonta ya ciko ta kasa ce mata komai, tana tuki tana taya Sa'adah kuka.
Da kyar Zainab ta shanye kukan ta ce "Ai Halima tana cikin bala'i ke har Safinan ma, domin dai saurayin Halima ya ki aurenta ne adalilin wastewarsu suke yi. Dake akwai alaka tsakanin su da gidan iyayen saurayin shine aka masta masa amma ko kadan babu kwanciyar hankali a tare da ita.
"Ita Kuma Safina har yau dai bata karbi result dinta ba, kiga dai a bayansu da shekaru masu yawa kika shiga makarantar amma kin kammala kin barta".
Aure kuwa shiru kake ji sai dai ana nan ana addu'a. Komai lokaci ne. Amma su kam hakkin kashe aure ne ya saka suka kasa samun nasu auren".
Chapter 29 · 0% Book details