← Book details Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 45

Sashe 11

Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Ya yi dariya ya ce "inace dan kin san bana son kina gatsa sunana ne yasa kike ta fa'da, to idan kin so kina iya cewa Mukhtar Kabir Bichi. Zan amsa miki amma nan gaba ka'dan Billahillazi idan akace ki fa'da ba zaki iya ba, zan fa'da miki wallahi ba zan ta bin kanki akan ki dawo gareni ba. Kina so, Ina so to karmu wahalar da juna dan wallahi kika ce zaki ja ni a kasa, ba zan yarda ba, ki rabu da Alh Mamman ban son ganin ki da shi".
Da guntun hawaye ta ce "sannu ubana, to shi nake so, domin kuwa kullum zai ta ganin yarinta ta ne, dama kuma ai tsofaffin sun fi dadiin harka.
Sosai ransa ya baci, a fusace ya dinga kwankwasa gilashin har Mahmoud ya ankra ya iso ya ja motar har kofar gidan Suka kaita, Mahmoud Yana ta faman tsokanarta ya san ai anshirya sai maganar shan biki, duk yadda take jin nauyin 'Karfi yau haushin sa take ji dan haka har ta sauka kala bata ce masa ba.
Da shigarta Sumayya ta dinga bin ba'asin kukan da take yi, bata boye mata ba, ta bata laabrin wula'kancin da Baffa ya janyo mata a wurin Mk na sawa ya kawota.
Ran Sumayya ya baci sosai ta ce "ai sai dai ki dau dangana domin kuwa Baffah burinsa bai wuce ki komawa uban Jawad ba. Duk irin bacin ran da ya jefa mu, duk irin yadda ya jingine ki shekara da shekaru, yanzu kuma dan gata da rashin kishin naka, Dan ya dawo sai ka sake bashi aure?".
Kwalla ta cika idon Sumayya tana ji a ranta Mk bai cancanci auren Iya ba, har ga Allah ta fi sonta da Anwar, amma ko ita ai ba karamin ba'kin cikin Mk ta hadiya ba.
Amma sanin maganar mahaifin su gaba take da kowa, yasa ta hadiye maganganun a zuciyarta, sannan kuma tasan komin borin da Iyah zata yi ba wadda take so irin uban na Jawad.
****
Sai bayan magariba ya isa gidansa, ya iske Farida cikin cotton din doguwar riga kirar Pakistan, kanta dauke da hular da ta dace da rigar, sai kamshi take yi, ta yi kyau sosai, amma saboda ba ita yake son gani a yanzu ba , sai yaji ba haka yake bu'katar ganin kirjinta ba, so yake ya kamo wadda zasu cika masa hannu kamar yadda dazu ya lalubo na Sa'a da nufin zai kamo bakinta.
Ya zauna a kujera ta tashi ta kawo masa ruwa da lemon coke, da cake da ta yi a yammacin yau
Yana zaune ya rike kansa alamun yana cikin rashin sukuni.
A hankali ta ce "halan baka jin da'di ne?"
Dai-dai lokacin sai ya dinga jin muryar Sa'a na masa kuwwa tana fadin Alh Mamman take so, ai tsofaffi sun fi dadin harka.
A fusace ya mike ya ce mata "A a asibiti ne a kaina". Sannan ya wuce ya haye sama.
Jikin Farida ya yi mugun sanyi, ta zauna tana ambaton Allah.
Ta jima tana nazarin me ya same shi, kaso mafi yawa tafi zaton Sa'adah ce ta zaunguro shi, kishi ya kamata sosai, domin ta lura duk sadda ta ganshi a burkice to ba shakka itace ta birkita mata miji.
Haka ta yi ha'kuri ta kwashi abincin ta bishi da shi, abin mamaki kuma sai ya rungumeta yana fa'din ta kara hakuri da shi, Yana cikin wani irin al'amari ne da yake neman fin karfinsa Dan Allah ta kara hakuri, ta kuma yi masa uzziri.
Matsananciyar sha'awar Sa'a da ya taho da ita tasa ya kasa fita sallar isha, domin akan Farida ya sauketa, sai da suka nutsu, Suka yi wanka sannan suka yi jam'i tare.
Ana idar da Sallar isha Baffa bai tsaya a shagonsa ba, saboda yadda ya ke zumudin tattauna al'amarin da Mk ya zo masa da shi a yammacin yau, dan haka kai-tsaye gida ya dawo. Sai da ya kamallah cin abincin da aka gabatar masa ya wanke hannu da baki.

Ya kalli Inna ya ganta duk a takure tun safe haka ya ke ganinta sukuku.
Cike da kulawa ya ce "me yake damun ki ne Salamatu?"

A sanyaye ta ce "Ba komai jikin ne nake jinsa ba tsanani, amma lafiya ta kalau".
Chapter 11 · 0% Book details