← Book details Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 45

Sashe 14

Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

miki zamu je lokacin da zaki ta kira na cikin tsananin son na dauka ba kuma zan saurare ki ba Nima". Da kuka sosai ta ce ka auro har da Halima Mutari, menene hadina da kai da zan damu ne, kuma Wallahi ba zan yarda da wannan abin da kake mini ba, Baffah na dawowa Zan fada masa ya bawa 'Karfi kyautar aurena shi nake so, dan kuwa birge ni yake saboda sanin ya kamatansa". Jinsa ya yi shiru na dan lokaci ya sa ta dago ta ga idanuwan nan sun sake kadawa tamkar garwashi, wani irin tsoro ya cika zuciyar ta amma bata ce komai ba. Cikin murya ba amo ya ce "sonsa kike yi da gaske ko kuwa ramawa Kika yi dan na ce zan auri Safina? Ai bance ina sonta ba ni, akan me zaki nemi hada ni da aminina, ke dai burin ki a duniya bai wuce ki tayar mini da hankali, ki kassara zaman lafiyar zuciya ta ba ko? to Billahillazi zaki san kin fa'da min wannan mummunar kalmar wai yana birge ki. Na rantse miki U will pay for it" Ganin yadda ya fusata ya sanya ta shamace shi ta mike ta shige cikin gidan da saurin gaske tamkar gudu gudu. Sai da ta tsaya ta gyara fuskarta, tana raya yadda zuciyar ta take fatali da hudubobin Innah da Anti Sumayya akan kar ta bari ta dinga kula Mk, batavsan dalilin ba, bata iya wannan jarumtar. Ya jima a zauren kafin ya tafi, ya roki Akeel ya tuka shi zuwa gidansa domin ba zai iya tuki ba. Kwana ya yi cikin wani irin matsanancin kishi, bai yi barci ba duk juyin da zai yi Sa'a yake gani da wani namijin cikin shigar farin taufafi, sai kuma da ta ce Mahmoud na birgeta. Tabbas idan bai tashi tsaye ba, ba zai samu Sa'adah ba, domin sosai ya hango wani irin fishi mai danne soyayya duk karfinta kuwa a tare da ita. Washagari daga fitowar Mk daga masallaci ya dauki mota bai zame ko ina ba, sai gidan Alh Isa. A falonsa na waje ya tarar da shi bisa al'adar sa na zama ya gana da iyali, baya tashi sai 8 sai ya shiga ya kwanta zuwa goma sai ya tashi ya karya. Ganin da Alh yayi Mk na bu'katar yin magana da shi ya sa ya sallami iyalinshi, ya ce su basu wuri. Bayan sun sake gaisuwa. Mk ya sunkuyar da kansa kasa ya ce "Dama zuwa na yi, na fa'da maka, ina son kaje wurin Baffah ka tambayar mini auren Sa'adatu". Alh Isa ya yi shiru, yana jin wani irin bacin rai na taso masa. Mk ya sake yin kasa da kansa yana sauraronsa, amma tsawon lokaci bai ji Baban ya yi magana ba. Ya dago sai ya ga Alh yana goge hawaye a idonsa. A sanyaye Mk ya ce "lafiya kuwa Baba? Subhanllah! Ban san a cikin damuwa kake ba dana bari har ka samu nutsuwa". Sai lokacin Alh ya nisa cikin rawar murya ya ce "Takaicin yadda wannan ranar ta riske ni ne, Ni ka'dai babu mahaifinka, domin da yana da rai da bulala zansa na zane maka jiki don in tabbatar maka har yau din nan ina maka kallon yaro dan karami da bai kai yaronka Kabiru ba! na kuma ganar da kai irin isar da na yi da kai, don na lura ka manta. Amma tunda bashi da rai ai dole na yi ta ha'kuri da duk cin kashin da kuke mini tunda na san idan shine na mutu na barshi ba zai fita a cikin sha'anin ahalina ba". Hankalin Mk ya tashi, ya rasa inda zai tsoma ransa ya rarrafa jikin dattijon da girma ya sake kama shi ainun. Ya ce " Dan Allah Baba yanzu ma doke ni indai zaka huce! Ai komin girman da zanyi har gobe Ni yaro ne a gabanka dole na jira abin da zaka zartar". Hawaye ya sake zubowa Alh ya ce "Ai yanzu idan na dake ka kana iya daina zuwa wurina dan ka nuna mini abota ce kawai ta hada ni da ubanku ba jini ba, yau shekaru bakwai ina kwankwa'dar bacin ran jingine yarinyar dattijon arziki irin Malam Basiru, Ina fama da kunya da nauyinsa iri iri. Amma saboda Ubangiji ya zuba alheri mai yawa a zuciyarsa tunda nake jinyar nan da bana iya fita sosai duk juma'ah sai ya zo ya gaishe ni, ba tare da tunanin ina da halin da zan mayar masa da yarinyarsa dakin miji amma banyi ba. Ni kuma na san isane kawai ban yi ba, ka zo yin aure ka saka ni a maganar tsundum tare kuma da uban 'yar da ka saketa. Dan ya gane zan iya nemo maka sabon aure, na yarinyarsa ne ba zan gyara ba, Abin da baka sani ba na shiga lamarin aurenka ne dan kar na ji kunyar kushewa ne kawai! Sai yanzu kuma ka zo ka ce wai naje na nemar maka auranta, saboda kawai ka nuna mini amfanina a gurinka sai sadda ka so Abu akaran kanka, idan baka so ba kuwa da ni da wadda baka sani ba duk daya". Maganganun Dattijon ba karamin rikita Mk suka yi ba, ba karamin tayar masa da hankali suka yi ba. Ya kasa bude baki ya masa magana, sai ya hado kalmomi sai ya ga sun yi kadan su wakilci ba da nufin hakan ya yi ba, tsawon lokaci yana gurfane yana ta goge zufar da take yanko masa. Ya ciro wayarsa ya dinga lalubo lambar'karfi amma ya kasa saboda yadda kalaman Baba suka kassara shi, da kyar ya tsaida hankalinsa, ya samo lambar, Mahmoud! Ya na dagawa ya fara masa sababi ya dauka akan Sa'adah ne zai kira shi da sassfe, har yana cewa " Lokacin da ka rabu da ita menene ba'a fa'da maka ba akan ka yi hakuri amma baka ji ba". Murya a dusashe ya ce " Ina cikin masifa 'Karfi taimake ni ka zo ka same ni a gidan Baban Na'ibawa". A sukwane 'Karfi ya ce menene, ko jikinsa ne ya tashi?" A sanyaye sosai Mk ya ce"ka bar komai ka zo yanzu Dan Allah" sannan ya kashe wayar yana ta faman fadin innalillahi. Mintina biyar Mk ya kasa ha'kuri ya ce "Ka dubi girman Allah ka yafe mini Baba wallahi ba haka bane a Raina, amma na gamsu na yi laifi ban kyauta ba! ka mini afuwa fishin ka dafi ne. Baba abota babban al'amarine da ya wuce a kira shi da kawai, domin sai da Annabi ya jaddada mana mu ri'ke Aminan iyayen mu, mu sadar da ZUMUNTA da su domin ya nuna mana suma suna da Hakki akan mu, ina ba'kin cikin cewar da ka yi baka isa da ni ba". Alh baice komai ba, illah ajiyar zuciya alamun ya dade da abin yana cinsa a zuciya. Ya nisa ya ce "Idan ban yi hakuri ba yaya zan yi Muhammadu?" Dai-dai lokacin Mahmoud ya iso cikin tashin hankali, ya gaida Baba cikin girmamawa. Mk ya ce 'karfi laifi na yiwa Baba tsawon shekaru bakwai yake ta kallona da abin, Amma ya ce " takaicinsa daya da Baban Samira baya raye domin da a gabansa zai zane ni tamkar yadda za'a zane Jawad, shine nake so ka kawo masa dorinirka ta cikin motarka ka zane masa ni domin yanzu shi ko ya dake ni ma sai ya ji a jikinsa, tunda lafiyar lallabata ake yi, ka cire tausayi ka zane ni har sai ya ce ya isa haka". Da sauri 'Karfi ya juya mota ya dauko wata irin sharbebiyar dorina ta dukan dokinsa ce da ya mutu, shine yake ta ajiye da dorinar yana yiwa yaransa barazana da ita. Daga shigowarsa, yasa iyakacin karfinsa ya shammaci Alhaji ya zamba'dawa Mk dorinar nan, a kidime Mk ya zabura domin kuwa ba karamin kidima shi bulalar nan ta yi ba Ba dan tsananin jarumtar da ya saka a zuciyar sa ba, ba abin da zai hana ya zunduma ihun neman agaji.
Chapter 14 · 0% Book details