← Book details Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 45

Sashe 20

Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

gidan ta dawo sanye cikin uniform tabbacin Ma'aikaciyar lafiya ce. Mk ya tasa ta gaba yana fa'din " bazai yiwu kullum kina barin aminina shi ka'dai a gida ba, dole zamu lalubo wadda zata zauna ta kula da shi. Tababa da ke mai kunyace ta fice ta bar Mk na yi musu sha'kiyancinsa da baya gajiya. Za su tafi ta kawo turare ta bawa Jawad, da wata kullin leda mai dauke da man shafawa da na zafi ta ce na Hajiyar Bichi. Mk ya tsaya cak yana fa'din" Tababa ta Malam ki ji tsoron ubangiji, ita kuma Farida ina nata sakon, gaba'daya kin saka son zuciya a lamuran ki, saboda ba kawar ki ba ce ita" Da sauri ta koma daki ta dauko kyawawan mafitai guda biyu ta ce ga shi nan, ta yi maka fifita ni bana son sarhutunka". Ya karba yana fa'din kin fanshi kanki, yayin da mijinta ya yi gaba yana fa'din ranar da za'a mata amarya ai ban san irin boren da zata yi ba, idan ka ga yadda ta yi kukan aurenka sai ka yi mamaki, ta taya Sa'adah kuka irin wannan ina kuma ace ita za'a yiwa?' Mk ya murmusa ya ce ai kuwa dai Tababa kwantar da hankalin ki, daga yadda na ga kin iya karrama ba'ko , zaki dade kina jan zarenki, muma kaddara ce ta fado mana, Ina fatan idan kuma kaddarar ta fa'do muku ba zaki yi watsi da kyawawan dabi'unki ba". Ya damkawa yarinyarta karama kudi, Yana ta godiya da karamacinsu, ya tafi ya barta da sanyin jiki tana addu'ar kasancewa ita ka'dai. Har la'asar Mk na Wudil domin tare da aminisa suka je ainihin gidan su Baba Isa ya ziyarce su, suka dinga sa masa aalbarka ya ajiye musu buhun shinkafa da katon din taliya, har da ku'di a kanin Baba Isa Wanda shine babba a gidan yanzu. Sai da suka fito ya ajiye Aminin nasa a kwanar gidansa, suka yi sallamah. Sun tsallake gadar Wudil ya samu wuri ya tsaya. Ya ce "Jawad dawo gaba kusa da ni, kana mini hira". Hakanan kuwa aka yi, sun zo dai dai Yar gaya, Jawad ya ce "Allah sarki Muhsin Yargaya! ko yana ina yanzu?" Ya dinga bashi labarin Muhsin da irin halin da yake ciki da matar Babansa. Nan Mk ya fahimci inda Jawad ya samu dalilin juyawa Farida baya, ya dinga jin tausayin yaran da suke fuskantar kalubalen rashin rayuwa tare da uwarsu. Cikin hikima ya ce "Ashe Muhsin ya fa'da maka u have to be careful with Aunty saboda kar ta raba mu?" "Eh mana Malam! Saboda na san kai baka san hakan zai iya faruwa ba". Mk ya yi murmushi ya ce "Jawad kowa da halinsa! Da zata raba mu da tuni ta yi hakan, fa'da mini ta ta'ba dukan ka lokacin da muke Uk?" Ya girgiza kai alamun a a, Mk ya zarce da fadin "abinci ne bata baka ko?" Da sauri Jawad ya ce "Ah Malam tana ba ni, every day sai ta cika mini lunch box dina, abincina ya fi na kowa yawa, kullum sai na dawo da shi". "Ka ga kenan ba halin su daya da Waccan da abokinka yake baka labarinta ba". "Amma Malam ai ita kake so ba Mami ba". Jikin Mk ya yi mugun sanyi a shekaru sha uku Jawad ya yi wannan maganar? Al'amarin yaran yau idan kana daukar maganar su tabbas zasu raba tsakanin ka da jama'a ne, ka yi ta ganin tamkar kitsa musu magana ake yi. Ko kuma ana koya musu iyashege ne alhalin kuma abin a jikinsu yake, sai dai ayi ta nuna musu kyakkawar turba cikin azanci da nasiha. Mk ya nisa ya ce "wa ya fa'da maka bana son Mami? Ita ce fa ta haifa mini kai! Kasan kuma u are my only son, dole kuwa ta zamo very precious to me". Da'di ya kama Jawad ya ce " To yaushe zata dawo gidan mu, tunda we are Muslims, polygamy is allowed, above all ma ka mini al'kawarin zan dawo hutu na ganta a gidanmu ba a gidan Baffah ba". "Eh na yi maka ban kuma manta ba. Amma matsalar itace bata mini magana, bata gaishe ni, har Baffa yana mata fa'da amma still bata ji ba". "Ni zan fa'da mata ta daina yin haka tunda kullum sai ta ce mini arogance ba kyau, ba dabi'ar mutanan kwarai bane". " Yauwa sannan ka fa'da mata, kana son ganinta a gidanmu, if not jirgin nan da zaka siya mata zai zama nawa". Dariya Jawad ya dinga yi yana cewa" Malam ka damu da jirgin nan, amma ai yanzu na ce har da kai zaka shiga. Ni ban san me yasa ta daina son dawowa ba, bana manta sadda take kukan so take ka zo ka dauke ta mu koma gidanmu" Jikin Mk ya yi sanyi ya ce "tafiyar da muka yi, muka barta ne, amma idan zan sake komawa da ita zan tafi, kai kuma ka zauna tare da Anti a anan". "A a Malam gaskiya ba a yin haka, da ni za'a tafi" " To na yarda da kai zamu tafi, yanzu idan ka je gurinta sai ka yi ta bata hakuri ta dawo ta zauna da mu". Murna tamkar Jawad ya zuba ruwa a kasa ya sha, wani irin farin-ciki ya bayyana a dukkan jikinsa Sun iso kano Mk ya kalli Jawad cikin uniform dinsa sai ya dinga tuno shima lokacin da yake makarantar su ta 'Karaye. Haka yake tamkar Jawad, sai dai da alamu Jawad yana iya zarta shi tsayi domin a yanzu ma ya kusa kamo shi. Tsayin Jawad da saurin da karatunsa ya yi sai ake ganin tamkar ya zarce shekarunsa. Da tarin kauna ya ce " A ina kake son yin hutunka?" Kai Jawad ya sunkuyar ya ce "gidan Hajiya". Mk ya ce "Antinka fa tana can ta shirya maka something special". "Zan je amma ni gidan Hajiya zan zauna". "Me yasa to ba zaka je unguwa uku ba?" Ya marairaice tare da cewa " Na san idan na ce can zani ba zaka yarda ba". Da sauri Mk ya ce na yarda Jawad! Ka yi hutunka duka acan idan kana so".
Chapter 20 · 0% Book details