← Book details Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 45

Sashe 16

Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da sanyin muryar ya ce "fishi take yi da ni Baba! Amma da zarar anyi auren zamu dai-dai ta, tana sona wallahi"
"Ashe dai ta san ciwon kanta, domin kuwa ka yi mata laifin da duk wadda ba ya jin tsoron zuciyarka zai fa'da maka cewa "komin girman laifin da ta yi maka, hukuncin da ka dauka akanta ya yi tsauri, ya wuce makadi da rawa, ko kadan babu a ragayya cikinsa".
Jikin Mk ya dinga bari sosai, shi da kansa ya san kunyar Baffah ya jita irin wadda bai yi zaton anan kusa akwai wadda ya ta'ba jin irin wannan kunyar ba.
Amma ya tabbatar da ya fito ya fa'di laifin da ta yi masa na cigaba da mu'amala da tsohon saurayinta, da ba wadda zai dora masa irin wannan laifin na bai yi adalci ba, domin munin abin ya baci, ba ta da hurumin yin hakan ta kowacce fuska tunda ba muharraminta bane bata da alaka da shi ta kowacce fuska, sai tsohuwar soyayya.
Amma son da yake mata ba zai bari ya fadi wannan al'amarin ba, domin da yawa wasu zasu zargeta, zasu kyamaceta, tunda idan ya ce tana tare da wani ne musabbmabbin rabuwar kowa da abin da zai raya a ransa, ba a kuma isa ace sai kowa ya yarda ba barna suke aikatawa ba, shi yasa ya zabi ya boye a ransa shi ka'dai, amma kuma dole su nisanta da juna tunda ba abin da shaidan ba zai dinga raya masa ba, zai dinga zarginta ne ko da kuwa ba hakan bane a zahiri kasancewar sa dan Adam mai rauni ba a ma'asumi ba".
*UZZIRI*
*Duba da muna cikin kwanakin nan masu tarin falala da albarka, sai nake ganin ya kamata mu jingine Wannan labarin dan samun damar ribatar kwanakin da ubangiji ya rantse da su, ba lallai mu riski na wata shekarar ba*. *Dan haka zamu tafi hutu sai bayan sallah idan muna cikin rayayyu zamu zo mu karasa abin da ya yi saura in sha Allah. Dafatan ubangiji ya karbi ibadunmu ya sa mu yi hidimar sallah lafiya, kar mu manta da yiwa KASARMU addu'a.*
*Ubangiji ya bamu damuna mai albarka*.
*Na gode muku sosai da yabawar ku kan rubutuna.
*Barkan mu da ibada! Barkan mu da bikin farin-ciki. Ina fatan ubangiji ya karba mana kyawawan aiyukanmu, ya shafe mana kurakurai. Ina yi mana Barka da bikin Babbar sallah, ubangiji ya dawo mana da Alhazanmu lafiya, ya kuma zaunar mana da kasar mu lafiya.*
*Allah ya maimata mana*.
A tunaninsa space din da ya bayar a tsakanin su, dan ya samu zuciyar sa ta nutsu ne, ta daina wasiwasi akan ta, ashe laifine tunda ba kowa ne yasan azabar da yake dandana adalilin hakan ba.
A sanyaye ya ce "shikenan Baba na yarda da hukuncinka zan kuma yi biyayya akansa in sha Allah".
Tari ya sarke shi sai da ya lafa masa, ya ce " duk Ranar da kuka dai-dai ta da ita ka zo ka dauke ni, ka kaini gabanta, tunda nema muke yi".
Suka yi godiya sosai suka Mike bayan sun ajiye masa kudi.
A mota Mk ya ce "Karfi ka ji dadi da dake Ni, duk yadda aka yi dama kana son ka samu damar da zaka dakenin shine yau da Ubangiji ya ara maka dama, ka cire tausayi ka tafka mini bulalar da sai da na ji tamkar na saki fitsari a wurin".
Cikin dariya sosai 'Karfi ya ce "Ashe baka iya tsiya ba, da ka saki fitsarin ai kaga dole na yi bi'kin wurin da ka bata, dole kuma na ruga wajen Farida na karbo maka wasu kayan ai ko banza ka wahalar da ni".
Mahmud da ya ga yadda bulalar ta kwanta a kafada zuwa gadon bayan Mk ta tashi sosai wani wuri har ya yi baki tabbacin ya fara fashewa jini ya kume a ciki.
Ya tattaro dukkan alhini ya yaba a fuskar sa yana faman fadin "sannu Bichi ashe haka ta shige ka wlh mancewa na yi ta dukan doki ce ba bil'adama ba"
Mk ya ce "idan ban yi hakuri ba na Yi ya ya da kai?"
Ya nisa ya ce "Ya zan yi ne 'Karfi? da gaske yarinyar nan so take sai dukkan rauni na ya bayyana, ga dai idanuwanta cike suke da soyayyata amma bakinta sai ambaton kiyayya yake, bayan na san abin da nake gani a idonta akwai ninki ba ninki a zuciyarta, Ni kuma ba zan bata damar da zata ja ni a kasa ba, wahalar da na sha akanta bana jin nan kusa akwai namijin da ya shata, ko da na ki dawowa da ita na tabbatar na fita shiga tagayyara akan rabuwarmu!
Yanzu kuma naga Shirin shayar da ni wata azabar take yi, bata daukan wayata, jiya kuma 'kaddarar zan yi gamo da ba'kin ciki ta kawo ni shago, kawai sai ganinta na yi da wani dan guntun halitta sun zo tare a motarsa, a gaban motarsa fa ba mayafi sai wannan rigar da hular lauyoyin da basu rufe kwalliyarta ba, gaban rigar bai rufe komai ba".
Ya fada yana dukan sitiyari, Mahmud shima ya ji kishin yaron ya kama shi, amma ya daure ya ce
"Kai ka bada kofar da zata yi hakan da ka mayar da ita tuntuni da bata zo tana sake shayar da mu wannan ba'kin cikin ba".
'Karfi ya shanye dukkan yadda zuciyarsa take bugawa ya ce "Mk tsakani fa da Allah tsananin rabo ne zaisa yarinyar nan ta saurare ka, ka yi mata zunubin da 'ya'ya mata basa yin sassauci a cikinsa, ka tsaurara kwarai da gaske. Ka yi tsam da ranka wallahi ko Baffah kawai dan zuciyar sa irin ta mutanan da Allah ya zaba ya musu alheri da ha'kuri ne. Banda hakan da tuni gaba ne a tsakanin gidanjenku, amma ko ni din nan Baffah ya na mutuntata ni adalilin ka! Barah gaf da zaka dawo ranar juma'ah ya mini waya akan idan ba damuwa na zo washagari asabar dan Allah. Na taho cikin wasi-wasin menene ya faru, ina zuwa sai ce mini ya yi Daurin aure zamu je Bichi, za'a yi auren cousin dinka, baka nan bai kamata bamu halarta ba, muje mu wakilce ka, a hanyarmu ta dawowa ya ce mini ya ji dadin tafiyar mu domin na debe masa kewar ka kwarai da gaske. Wlh da na dawo gida sai da na yi hawayen tausayin bawan Allahn nan, sonka yake irin son da babu algus, gefe daya kuma na dinga jin kunyar matakin da ka dauka akan jininsa, matu'kar da gaske son Sa'adah kake yi sai ka na'de kafar wandon jure dukkan borenta har mu samu ta zo hannu".
'Karfi ya zarce da fadin "Ka gama da ita, ka sha da ita, ba abin da zata yi maka ta huce tarin takaicin da ka cusa mata".
Jikin Mk ya yi sanyi yana ayyana ina ma zai iya fitowa ya fa'di irin abin da ta yi masa da ya tabbatar an gane shi din adali ne na gaske, domin aure ba adadi ya mutu a irin wannan matsalar sannan kuma zubewar mutunci shi ya biyo baya, tunda duk macen da aka saka adalilin tana mu'amala da wani namiji komin kankatar muaamalar kuwa mutane da yawa zasu mata hukuncin babbar mu'amalar take yi.
Basu zame ko ina ba sai gaban Hajiyar Bichi suka fa'da mata abin da Alh Isa ya ce.
Ta yi jugum ta ce "Ashe kuwa Allah ne ya so ni domin wlh ni kaina kunya ce ta sa nake ta jan kafar zuwa gidansu Sa'a, yanzu kuwa na fasa ba zan iya ba, maganganun Babanku akan turba suke, yanzu ne kake so mu shige maka gaba alhalin a farko ka nuna musu baka da iyaye".
Hankalin Mk ya yi tashin gauron zabi.
A hankali ya ce " Amma Hajiya da bakin ki kika ce zaki rarrasar mana ita".
Ta ce " eh na fa'da amma yanzu na gane bai kamata na shiga ba, domin a lokacin da yarinyar nan take cikin tasku ai baka yarda na yi iko irin na uwa da kai ba, ka ga kuwa bai kamata ace yanzu ita na yi mata karfa-karfa ba, tunda na san da dukkan zuciyarta tana sona tana girmama ni, ku je Mahmoud ya taya ka, zan biku da addu'ar dacewa ubangiji ya huci zuciyarta, amma ni kaina ban jin zan iya yafe irin abin da ka yi mata idan aka yi mini irinsa".
Idonsa ya ka'da ya ce "wai har me na yi ne haka Hajiya? Saboda na zabi na bar abin da ta mini a zuciyata shine kuma sai aga ni na zalunceta, na san dai laifin bai wuce kawai dan na yi aure ba".
Daga 'Karfi har Hajiya suka hada baki wurin cewa " Ai kuwa ya fi karfin ace kawai, kai yanzu ka barta ta auri wani mana indai kawai ne".
"Bana son haka 'Karfi bana son wannan kwatancen"
Chapter 16 · 0% Book details