← Book details Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 45

Sashe 30

Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin kuka sosai Sa'a ta ce "Tabbas su Halima sun yi wa rayuwa ta illah, Amma kuma ai da gudunmawata, yarda na yi da su, sannan nima ina da tawa matsalar, bayan wadda suka cusa min, kawai iza mini wutar suke yi, Amma ni na hura abata.
Dan haka na yafe musu, amma bana fatan mua'amala ta sake hadamu, rabona da su tun ina gidan Malam, in sha Allah kuma rabuwarmu kenan domin tarayya da su halaka ce, na rufe babinsu har abada, dan haka kema daina yi mini maganar su".
Zainab ta dinga lallashin Sa'adah da maganganu masu taushi, tana nuna mata, ta yawaita addu'ar sau'kin kishi, itama zata taya ta, sannan yadda ta yi maganar a fita mata da shi waje suyi magana a gadarance, amma ya tashi duk da baya jin da'di ya isa ta gane har gobe ita ke jan ragamar zuciyar sa, sai dai dole ya yiwa Farida adalci domin matarsa ce, dole kuma zai sota.
Zainab ta nisa ta ce "Dan Allah Sa'adah ki 'dore da kyawawan dabi'un ki, kar ki bari kishi ya mayar da ke 'yar gidan jiya, kin san dai yanzu ba ke ka'dai bace, kuma Wallahi duk son da namiji yake yiwa mace indai ta cika kishi da korafi, fita fit take yi a zuciyarsa.
Ke ce uwargida tunda baki yi wani auren ba, dole ki 'dauki hakuri mai yawa. Ki koyi hakuri da juriya, duk yadda kike da mutum kar kiyi zancen abokiyar zamanki da ita mussaman dangin miji, domin duk ranar da abu ya ha'do ku da su, sai sun zayyane mata komai, a hada da sharri ma, daga nan girman ki ya zube a idonta, itama kuma ta sami damar da zata dinga fa'din munanan dabi'un ki".
"Na gode miki Zainab! Na sani ke din mai sona ce ubangiji ya sanya mu cikin masu zumunci dominsa".
Sa'a ta fa'di hakan a sanyaye.
Zainab ta ce "gida zan ajiye ki, ko gidan Anty Sumayya?".
A tunzure ta ce "gidan ubana zaki ajiye Ni, ai Ni da gidanta sai ta neme Ni".
Zainab ta yi shiru! ta san tana tofawa baza su rabu cikin da'din rai ba.
Wasu daga cikin halayyar Sa'a a jinita ne ilimi ko shekaru ba zai sa ta sauya ba, rikici na cikin abin da ba zata daina ba.
A Daren ranar Baba Isa ya dawo asibitin ya fa'dawa Mk ranar juma'ah mai zuwa za'a mayar da aurensa da Sa'adatu, amma ta nemi abarta ta kintsa kafin ayi maganar tariya tunda titsiye ubanta ya yi mata, ba dan tana so ba.
Ya ce " Na kuma yi mata wannan laminin, dan haka ba zata tare ba, sai ta shirya, wannan umarni na ne".
Baban ya nisa ya ce "Soyayya da sanin darajar Dan Adam ne kawai ya sanya Malam Basiru zai sake baka aure a Karo na biyu! Ka sani da ni da mahaifinka ra'ayin mu daya, shawarar mu daya, hakanan neman kudinmu daya, abin da Zan fa'da maka yau, na tabbatar da yana raye a gabansa zan fa'da maka domin ka sani idan ina waje baya ta'ba nuna shine ubanku yana dora ni akan komai nasa matu'kar anan Kano ne, da bashi da dan'uwan jini.
To ka saurare ni da kyau ni na karba maka amanar yarinyar nan, idan har ka bari ta wulakanta ina rantse maka da Allah ni ka wulakanta, na kuma tabbatar idan har ka wulakanta ni, zaka wulakanta Kabiru, hakkin abotarmu ba zai bari ka ga haske ba, ko bayan ba raina, ina maka wasiyya akan yarinyar Malam Basiru domin ni dai banga mai arziki a wannan zamanin irinsa ba, Ubangiji ya bashi wadatar zuciya, ya bashi alheri mai yawa, wadannan kuma sune kololuwar arziki".
Da tsananin farin ciki Mk ya ce "Na ji Baba, in sha Allah ba zan sake kunyata ku ba, komai zata yi zan yi ta ha'kuri, zan kara hakuri akan ha'kuri. Ya sauko ya durkushe a gaban dattijon ya ru'ko hannun sa ya ce " Baba ina maka shaida baka watsar da iyalin amininka ba, har yau din nan da tsufa ya cimma maka sosai, baka huta da yi mana hidima ba. Ina yi maka fatan samun aljannar da Annabi ya yi bishara ga masu kyautatawa iyalan wadda suka rasu".
Jin wannan albishir din ya sake 'karfafawa Mk jiki, domin zuciyarsa ta yi haske. Washagari da safe aka sallame shi.
Ya isa gida bisa rakiyar Dr 'Karfi, tarba na mussaman ya samu daga Farida.
'Karfi bai jima sosai ba ya tafi. Mk ya dinga biyewa Farida na yadda take ina ka saka da shi.
Ya fito wanka ya tarar da ta ajiye masa kaya a bakin gado, gajeran wando ne tiri kwata kalar ruwan 'kasa, sai farar riga ti.shet ya fesa body spray ya sanya kayan da ta riga ta feshe su da turaransa na Versace.
Tawul din da ya dauro, ya dauka ya rataye shi a bandakin, yana fitowa ita kuma ta shigo dauke da tiren kayan abinci.
Yana zaune bakin gado yana kallon yadda ta yi masa shimfida, ta fara zuba masa abincin da ya kasance dankalin turawa da miyar albasa sai gashashiyar kaza, gefe yankakkiyar kankana ce jawur da ita, an lullubeta da ledar rufe abinci.
Sama sama ya ci abincin, ya mayar da hankalinsa wurin shan kankana, ya kalleta ya ce "zanga ranar da zaki daina bani lemo da safe".

Ta mike da sauri tana cewa"wallahi na dafa maka shayin ga su cups nan flask din na manta".
Cikin kankanin lokaci ta kawo masa, da kanta ta zuba masa, tunda ba ma'abocin shan shayi da madara bane.

Bayan ya kammala ta 'ballo masa magungunansa ya sha.

Ya mike ya ce " Bari na sauka na dan kewaya, bana jin ciwo a tare da ni, amma sam jikina babu karfi".

Ta ce "hakan ma babu laifi, ko na dauko maka lucozade it will help".

Ya kalleta ya ce "Bari na kewayo dai, so nake mu yamutsa shimfidar can."
Ya yi nuni da gado.

Kunya ta kamata ta yi murmushi, ba tare da ta sake cewa komai ba.
Ya juya ya fita.

Hakan kuwa aka yi, domin bai wani jima ba ya dawo, hakanan duk yadda yake jin rashin kuzari, sai da ya zartar da kudirinsa. Duk yadda take ro'kon ya bari ya warware sosai, amma bai ji ba.

Sai fa'di yake "kewar ki na yi sosai, har addu'a nake na samu sauki na dawo gida, ba dan komaai ba, sai dan na kasance tare da ke".

Da'di ya matu'kar kamata, ta tabbatar tana da matsuguni a zuciyar mijinta. duk dai abin da Sa'adah ta yi mata a asibiti, yasa ta gane har gobe tana da karfi a zuciyarsa.

Yini guda bai fita ko ina ba, da aka yi azahar ya ci abinci, ya sha magani barci ya yi sosai.

Dan haka bai fita ba, sai a washagari, ya fita zuwa gidan Hajiya, fa'da da Jan kunnen da ta yi masa akan ya ri'ke Sa'a da girma ba ka'dan bane.

Fa'di take "ubanta mutum ne har da rabi, ka ji tsoron ubangiji ka ri'ke ta da Amana, na sha fa'da maka ba hankalin ku daya ba".
Ya amsa da zai kiyaye.

Daganan ya leka shagonsa, ya kuma gaida Baffah.

Baffah ya ce "wannan karon ma sadaki kawai zaka bata"

Da sauri ya ce "A a Baffah bar ni kawai na yi mata komai, gatan zai mini yawa, yanzu Ina da halin yin dukkan abin da ake yi, na gode sosai da karamci, Ina fatan kar Allah ya sa na sake kunyata ka Baffah".

"A a ni ba ka kunyata ni, bare ka nemi tsari da sake maimaitawa, ba komai tsakanin mu sai karramawa, domin tunda kaki fa'dar abin da ya hadaku, kuma kowa ya gane itace mai laifin, sai na gane kai din jarumine, adaline, mai kuma kaunata ne, Koda ha'kurin ka ya kwace amma ai hankalinka bai kwace ba, domin baka tozarta mini Iyah ta hanyar fa'din aibunta ba, dan haka Ni baka mini komai ba, sai alheri."

Ya zarce da cewa "a farko da zan baka ita, sai da na jaddada maka kar ka bari ta kangare maka, duk kuma wadda ka ga tana mu'amala da su, hankalinka bai kwanta da su ba, ka shata musu layi, Ina jin dai baka dauki wannan shawarar ba shiyasa kuka tsinci kanku a halin da kuke ciki, ba fa zan rufe ka ba, kaima kana bari soyayyarta na rinjayar ka a gurare da dama, a farkon rikicin banyi magana bane saboda yadda ka boye komai ka sata itama ta rufe komai"
Mk da ya san Baffah gaskiya ya fa'da sai ya sunkuyar da kansa kasa, ya kasa cewa komai.
Tsawon lokaci kafin Baffa ya sake cewa "Na horeka da yin adalci a gidanka, ka yi iyakacin bakin kokarinka, ka yi adalci, sai kuma ka barwa Allah ya taya ka. Domin a yanzu ma ina sake fa'da maka duk abin da bai maka a tare da Iyah ba, tun kafin ku yi nisa ka taka burgi akansa, su mata da ka gansu idan ba a kula da tarbiyar su ba, nan da nan zasu halaka kansu su halaka mazansu".
Jikin Mk ya yi sanyi, domin kuwa a kullum dabi'un Baffah na fahimtar da shi bai gama saninsa ba, har yau din nan bai ci karo da mutumin da ya fi mahaifin Sa'a karamci da fadar gaskiya ba, ko da kuwa gaskiyar akan kansa ne.
Mk da ya rasa mai zai ce sai kawai ya sunkuyar da kansa kasa ya ce "Madallah da zuciya irin taka, dama ka sha fa'da mini ba Sa'a ce ta hada mu ba, ba kuma zata zama dalilin rabuwarmu ba, tabbas na gasgata hakan".
Chapter 30 · 0% Book details