← Book details Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 45

Sashe 22

Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Ya sani tabbas burinta ne tun tana secondary ta zama lauya, shiyasa a lokacin da zai samo mata gurbin karatu ya yi iyakacin kokarinsa ta samu fannin shari'a, Dan ta sami sau'kin halin da take ciki a wanccan lokacin.
Sai gashi duk irin fa'di tashin da yayi akan karatun nata, ashe a mahaifin wannan Dan isakan yaron da ya tsana, zai fara yi wa rana? Ya sake zubawa hoton idon suna kallon juna ita da Bar. Mustapha, da ya kasance saurayi, wani irin al'amari mai nauyi ya danne masa zuciya, idan ba Sa'a ba kishin Sa'adah ne sanadin mutuwar sa domin zuciyar sa zata iya bugawa.
A fili ya dinga ambaton "wallahi ba zan iya ba, ba zan jure ba, dole ki ajiye aikin nan, inko ba haka ba rana daya za'a tarar na zama gawa".
Karfin addua ne kawai ya daidaita Mk.
A yammacin ranar ya shirya ya nufi gidansu yana jin yau kam dole sai ya ganta.
Yana zuwa ya tarar da wani bacin ran domin tarar da ita ya yi tana zance da Anwar da ta ganshi kuma ko dar bata ji ba, bare ta sallami bakon ta saurare shi.
A sanyaye ya juya ya tafi, cikin sanyin jiki.
Hankalin Mk ya yi matu'kar tashi domin ya fara gasgata Sa'a cewa da gaske take zata dora ikon da Sharia ta bata akan ikon Baffa.
Ya kasa jurewa, washagari da yamma ya bita gidan Sumayya, da kyar ta saurare shi adalilin Idris din Sumayya na gidan ya masa masauki a katafaren falonsa na kasa.

Sumayya tana ta fishin akan me zai saurare shi, bayan ya san duk irin ba'kin cikin da suka sha adalilin sa.
Haka dai ya lallaba su tare da fa'din ai mahaifin Jawad ne, dole kuwa ayi taka tsantsan.
A rikice Mk yake fa'din "ya kike so na yi miki ne Sa'adatu? Ke fa kika mini laifi, ke kika zalunce ni, yanzu na samu, na farfado daga gashin Kumar da kika mini, shine kike son sai kin Kai ni kasa, wai me na miki ne da ban cancanci na sami nutsuwa da ke ba?".
Ya nuna kansa da yatsa ni kike cewa ba Kya so? A akan idona kike hira da wani namijin, kika wulakantani a gabansa? Ashe ba ni da wata alfarma a gurinki komin kankatarta, sai na fa'di na mutu ko sai na hadu da mummunar jinya sannan zaki gane ina son ki?"
"Ki na fadawa mutane ba Kya so na ko?"
Ya fa'da da wata irin murya mai nuna sarewa kwarai da gaske.
Ya mike shikenan Sa'adatu, shikenan, na yafe miki komai, ko na mutu ma, na yafe miki".
Ya tafi ko waiwaye bai yi ba.
Kwana ta yi tana jin fargabar ko ya tafi kenan?
Washagari Jawad ya biyota gidan Sumayya ya tarar da ita a compound din gidan tsaye da Alh Mamman da alamu rako shi ta yi zai tafi.
Wani iri Jawad ya ji, ya zo zai wuce su, ba tare da ya musu magana ba.
Alh Mamman ya ce" zo mana tare da yafito shi. Jawad akan dole ya karasa ya ce "ina yini a tsaye kerere, sannan fuskar nan a hade tamkar bai san murmushi ba, bare dariya.
Alh ya ce " da gani wannan shine 'Dan nawa ga shi nan sak Babansa".
Ya zura hannu ya dauko bandir din Yan dari biyu sabbi ya mikawa Jawad yana fa'din ka sha Ice-cream".
Jawad ya sake daure fuska fiye da dazu "Ya ce Babana zai mini fa'da ka ajiye' ka bawa masu bara".
Ya juya ya bar Alh Mamman da kudi sororo yayin da kunyar duniya ta kama Sa'adah, ta kasa cewa komai, mussaman yadda take bashi labarin hankalin Jawad da yadda yake sonta yake tausayin ta.
Haka Suka rabu ita a kunyace, shi Kuma jikinsa a sanyaye na mamakin iskancin karamin yaro irin wannan wato ya san kishin uban sa?
Sai da ta bari sun kwanta ta dinga yiwa Jawad nasiha da nuna masa rashin tarbiyar da ya yi ka iya ta'ba cigabaansa. Ya amsa da ya daina.
Bayan kwana biyu ta je kotu Anwar ya dawo da ita.
Jawad na compound din suna ball da su Ayman da Anis har ma da Khairat, suka ga shigowar motar Su Sa'adah.
Dukkansu yaran suka ruga wajen Yi mata oyoyo tare da gaida Uncle Anwar, soasai suke sonsa saboda yadda yake ciko musu leda da kayan ciye ciye.
Jawad ne kawai bai doshi inda suke ba sai kawai ya ja ya tsaya ya rungume hannunsa a kirjinsa.
Sa'a ta yafito shi da hannu, ya karaso ya tsaya bai ko kalli inda Anwar yake ba.
Ta ce Jawad ga Uncle kullum na tambayar ka".
Ya sake dauke kai ya ce "na ganshi sannunsa".
Ba'kin ciki tamkar ta hadiye zuciya.
Ta ce "ba zaka gaishe shi ba?"
Ba kunya ko shakka ya ce "Ai ba ubana bane" a hankali, sai dai dukkansu sun ji shi.
Ya juya ya barsu.
Anwar da ransa ya baci sosai, dole ya mata sallama ya tafi.
Ta shiga gidan a fusace tana neman Jawad tana jin tamkar zuciyar ta ta Fado dan tsananin bacin rai.
Chapter 22 · 0% Book details