← Book details Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 45

Sashe 19

Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Da kin san yadda Jawad yake son ki, yake fatana ya girma ya yi ku'di dan ya jiyar da ke da'di, da ba abin da sai sake damun ki na dai wani abu da ku'di zai iya siyansa." "Da kin san yadda nake son ki, nake kwana nake tashi da ke, nake jin kin fi duniya da abin da yake cikinta da baki yi kishin auren Farida ba". "Bari yau na fa'da miki gaskiyar magana ba dan ki yarda ki karbi soyayyata ba, sai dan ki gamsu iyakacin gaskiyar kenan, ina da yakinin ban ta'ba yi miki karyar da ban cancanci ki 'ki gasgata ni ba". "Farida na cikin jerin matan da ubangiji ya kaddara mini zan aura. Rabuwarmu ta zama tilas Sa'adah domin itama kaddarata ce. Kin sani idan ina tare da ke wallahi duk yadda nake zage 'kwanjina akan ki, zai yi wahalar gaske na iya aure, bani da wannan 'kwarin guiwar saboda tsananin son da nake miki. To fa'da mini ta yaya zan auri Farida alhalin ya hakan zama dole, na farko mutuwa na iya kauda ke, na biyu kaddara ta rabamu, kinga da ki mutu ki barmu, ai gwara kadarar rabuwar tunda idan da rai ai da rabo". Sannan Dan Allah bai isheki daraja ba ace ke ce kika biya sadakin kishiyarki, ke kuwa ni zan biya na ki, na tabbatar abin da Jawad yake yi miki a shekarunsa ya isa ki gane ubangiji yana tare da ke". Jikinta ya yi sanyi ta san kalamansa duka ba karya, illah wadda ya ce ta fi duniya, da hakane ai da sai ya bari kaddarar ta kasheta in yaso shima ya zauna jiran wa'adinsa babu aure har ya mutu, su hadu a aljannah su sake rayuwar da babu bacin rai, amma yanzu ya gama curarta ya bari wannan makirar da take boye ainihin kalarta, ta san komai nasa, ta mallake shi, shine zai zo ya mata da'din bakin wai ta zarce duniya? kai namiji Hankaka ne tabbas. Ganin ta yi lakwas sai ya ce "kin gamsu kin yarda?" Ai kuwa tamkar wadda ya mareta har huci take yi ta ce "Wallahi ko shiga kunnuwana wai kana sona fiye da duniya bata yi ba, na dai yarda Baffah da Jawad na zarce komai a gunsu". Ya fesar da zazzafar ajiyar zuciya ya ce "shikenan ba sai kin yarda ba. Ko ba kya sona mu komawa aurenmu, son da nake Miki, da wadda Jawad yake miki ya isa yasa ki rayu cikin farin-ciki". Ta goge kwalla ta ce "har abada ba zan yi farin ciki a hannun ka ba, ka rufe idonka ka ce mini ina ha'intarka, ka rufe ido ka ce mini ana maka sharing dina" Muryarta ta fara rawa tabbacin tsumin bacin rai ya taso, ta nisa ta ce "ka rufe idonka ka barni ka dauki wadda kasan na tsaneta saboda munafuncinta, ta faki idon mutane ta tsokane ni, amma sai ta layance a kuma bata gaskiya. Allah ne ya rufawa al'umma asiri ba karatun lauyanci ta yi ba, dan anga kwarewa wurin bada kariya ga karya". Da 'kyar ya ce na janye kalamina, wallahi tashin hankali ne da kishinki, Amma nasan ha'inta dai babbar ha'inta ba zaki yi ba, na san ni ka'dai ne na muaamalance ki, na tabbatar da hakan har zuciyata". Wani abu mai nauyi da ya danne kirjin Sa'adah shekaru uku ya fa'da mata sai dan saura. Ta ce "to shikenan na yafe maka. Amma ka sani gaskiya ban da buri ko sha'awar auren mai mata kishi kashe ni zai yi, kawai ka barni na auri wadda zan sami nutsuwa, ka bar ni nima na dandana wani namijin kamar yadda ka ke dandana Balarabiyar Yemen". A sanyaye ya ce "Sa'a ina jiye miki tsoron kar ki zama ajalina, domin kuwa banda lafiya, duk sadda na ganki sai kin yi mini fami a akan jinyar da nake yi". Kai tsaye ta ce" Tunda bakin cikin ka bai mayar da ni gawa ba, na tabbatar kaima ba zaka zama ba". Cikin gajiyawa ya ce "Next week Jawad zasu yi hutu, gaba'daya zai yi hutunsa a gurinki". Maimakon ta ji dadi saboda ta san dan ya faranta mata ne yasa ya yanke wannan hukuncin, sai ta yi nufin gwasale shi. Ta ce "bana bu'katar ganinsa ma bare ya mini hutu, inace saboda kar ya zo na zuga shi yasa ka kai shi makarantar kwana? Saboda kana son sai ya so Farida sama da ni yasa ka hana ya kwana a gidan nan sai dai ya zo ya yini? To shima na barka maka shi ban bu'katarsa, Ni kuwa a duniya me zaka mini na huce, ka zalunce ni iyaka". Kafin ya yi magana sai ganin Innah suka yi, a ladabce Mk ya sunkuya ya gaishe ta, ta amsa babu yabo babu fallasa, daga gaisuwar bata ko tambayi Hajiyarsa ba bare matarsa, ta juya tana cewa "kin dora girki kin barshi zai kone, daga cewa zaki karbo sako?". Wannan shagulatin bangaro da Inna ta yi masa ya matu'kar dukan zuciyar sa, yana ganin rashin nasarar sa a fili, Bai ga laifinta ba ko kadan, domin ya fahimci tana kan fahimtar su Baba Isa da Hajiyar Bichi ne. Wato Baffah ne kawai hoope dinsa. Akwai gumurzu kenan dan kuwa sai inda karfinsa ya kare, yanzu ne zai yi 'dambar jefa alkalamin sa cikin Tawada. Domin ya ga maneman nata dukkansu basu da makusa, shine ma mai tarin kalubalen rashin samun goyan baya a wurin iyayemsu, da Sa'adatu sa'ar Mata. Har sati ya zagayo Mk bai da nutsuwa, Farida kanta bata da sukuni adalilin halin da take ganin Mk a ciki, duk yadda take jin kishin Sa'adah sai take yin jarumtar boyewa. Take ta hadiye sauyin da take gani a tare da shi, gefe daya ma sai take hilatar sa da bashi labarin fa'dansu da Iyah a FGC, idan kuwa ta yi hakan sosai ta ke samun walwalarsa ya yi ta dariya, hirar kuma ta yi tsayi. Ranar dauko Jawad da wurwuri Mk ya tashi yana ta saurin tafiya, wani irin zumudin dawowarsa yake yi domin shine tsani na biyu da zai taimaka wurin shawo kan Sa'adah. Ya tuna yadda Jawad ya matsa mata ta gaishe shi ranar visiting. Ya sake tuna rokon da ya mata akan ta yarda su taho Kano tare, dalilin da ya zama sanadin da ta doke shi. Ya dinga murmushi yana jin kwarin guiwa na shigarsa. Tun jiya kuma Farida take ta faman hada masa snacks din barka da zuwa. Domin a harkar Baking ta yi zarrah, abinci wahalar sarrafawa yake yi mata amma idan ta yi za'a ci cikin dadin rai ba wai iyawa ne ko kadan bata yi ba. Amma harkar cake da su meatpie hadi da su samosa tafi karfi anan. Wannan karon har wani cake ta yi masa na mussaman, tamkar na murnar zagayowar haihuwarsa saboda girmansa da kyaunsa. An rubuta welcome to Home Dear Jawad!. Lamarin da ya farantawa Mk rai ba ka'dan ba, ya dinga gode mata, tare da yabawa. Yana futa ta zube kan kujera, tana son ta ga dame Mk ya rageta? Ta gama tunaninta ta gamsu bai rageta da komai ba, ko a harkar auratayya kuwa, anan bangaren ma ta lura yana daga mata kafa soasai saboda lalurarta, amma bu'katar sa ta zarta yadda yake mu'amalantar ta saboda rauninta da yake gani. Tsananin son Jawad da yake yi ne kawai yake dan mintsinin zuciyarta, domin ta gane son uwarsa ne ya shafe shi. Ta kuma amince ba laifi bane yin hakan, sai dai zuciya da bata da kashi, yasa take jin rashin da'din soyayyar, duk da kuma zata shaidi soyayyar Jawad bata rufewa Mk ido ya kasa tsawatar masa ba, yana iyakar kokarinsa wurin saita yaron, ko akan al'amarinta ma ba ya yi masa ta Da'di. A bangare 'daya ne, take ganin raunin Mk akan 'dan nasa, matu'kar suka fita shopping, indai ya ga ta zabi kaya to kuwa sai ya daukarwa uwarsa irin kayan sai banbancin kala, Mk kuma baya iya hana shi, ko cewa ya yi ya rage, da zarar ya bata rai shikenan zai ce ya dauka. Ta dinga jin sha'awar haihuwa na mamayarta, ta daga hannu ta ce "Na sani sarai baka manta da ni ba ya Allah! Idan ka tashi bani, ka bani mai lafiya, mai jin kai, mai kuma albarka. Ina neman tsari da wadda zai gigita zaman lafiyata da ta mutanan da suke kewaye da shi, Ina neman tsari da marar lafiyar da jinyar sa zata shagalar da ni yin ibada da yawan tuba da godiya bisa ni'imomin da ka mini marasa adadi". Hawaye ya ziraro mata ta sa tissue ta goge idanuwanta, ta sake cewa"Allah kar ka bari na kunyata, kai ka halattawa maza yin mace sama da daya, albarkacin yarda da hakan da na yi Allah kar ka bari na wulakanta akan wata da muka yi tarayya a jinsi guda". Kuka sosai ya kwace mata saboda kishin Sa'adah na neman hanata sukuni a zuciya. Ta Dade kafin ta tashi ta yi wanka, ta doro alwallah ganin takwas har da rabi sai tada sallar walaha, tana ta rokon a sau'ka'ka mata kishi, a kuma karawa Mijinta sonta da tausayinta. Ta rufe addu'ar da yiwa Mk fatan samun cikakkiyar lafiyar da zai gamsar da su, da kuma budin arziki, ta sake rokar masa ikon yin adalci, tana kuka take cewa Allah ka hana shi zaluntata, Allah ka bashi karfin zuciyar da zai yi adalci na gaskiya. *Ko mata nawane masu irin wannan dabi'ar?* *Shin kina sallar Duha kuwa?* *Idan ba kya yi maza ki fara domin Allah ya yi rantsuwa da lokacin, sannan kin yiwa gabbanki sadaka a yinin gaba'daya*. Sun iso Wudil, Mk ya ji bari ya ziyarci tsohon amininsa da suka yi F.C.E. Bichi tare. Ya laluba ba lambar wayarsa, ya dai dinga shiga hanyar ya gano gidan. Ai kuwa a kofar gidan ya tarar da shi yana alwalar sallah juma'ah. Da wata irin murna ya kar'bi Mk! Ganin lokacin sallah ne kawai sai suma suka yi alwalar suka zarce masallaci. Suna dawowa aminin nasa ya baibaye su da abinci tamkar dama yasan da zuwansu, Mk ya dinga tsokanar su da cewa wai har yanzu baka kara aure ba? Kullum uwargida na office?" Dai dai lokacin matar
Chapter 19 · 0% Book details