Sashe 35
Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Ta yun'kura ta laluba akawatinta ta dauko rigar barcinta ta saka, ta debo ruwa, tare da 'karamin tawul 'dinta, ta dinga goga masa a jiki. Hankalinta ya matu'kar tashi, ba ta san har yanzu haka son Mk yake da karfi a zuciyarta ba, sai da taga yana zazzabi nan, saboda gaba'daya jijjiga yake yi.
Damuwarta ta kai kololuwa, ta dinga jin inama ita take wannan ciwon shi kuma yana jinyarta.
Ta dauko paracetamol ta bashi da kyar. Tana hawaye, tana tofa masa addu'a.
Mk bai samu sassauci ba sai wajen 'karfe biyun dare. Barci ya yi awon gaba da shi.
Sai da ya yi barcin sannan itama ta kwanta kusa da shi, hannunta rike da nasa hannun.
'Kiran farko akan kunnensa, ya tashi baya jin ciwon komai sai kasala, ya jima yana zaune yana kallon yadda take barci, tana sauke numfashi a hankali. Gashinta da ya sha gyara, yanzu duk a hargitse.
Wula'kancin da ta yi masa na rashin yarda da shi a farko ya matu'kar tayar masa da hànkali, zuciyarsa tana gasgata sonsa ne da gaske ba ta yi a yanzu.
Amma damuwar da ya gani a fuskarta a lokacin da bashi da lafiya, ya fahimci sonsa take da dukkan zuciyarta, kishi ne babban matsalar da idan ba'a yi taka tsan tsan ba zai sake ruguza musu rayuwar aurensu a karo na biyu.
Ya kudiri aniyar yi mata addu'ar samun sassauci akan kishinsa da take yi da ya wuce ka'idar Sharia da mizanin hankali, tunda ko aka ran kanta ba zata ji dadin rayuwarta ba.
Da kyar ya sauka ya shiga bayi, ya yi wanka, ya doro alwallah, sai da ya yi nafila, sannan ya tashe ta, ya fice zuwa masallaci.
Ya dawo, ya tarar da ita zaune akan sallayah da hijab a jikinta.
Ya cire jallabiyar jikinsa, ya kishingi'da a bakin gado, tana daga zaune a inda take.
Ta ce "Ina kwana, Ya jikin?"
A hankali ya amsa da cewa ", Lafiya lau Alhamdulillah".
Daga nan kowa ya yi shiru, sai tunanin zuci suke yi.
Tsawon lokaci kafin ta ji ya yi gyaran murya ya ce "Yau nake son mu tafi, amma jikina babu kwari, ba zan iya tukin nan ba".
A hankali ta ce "Ubangiji ya baka lafiya, sai mu jira zuwa gobe, mu ga mai zai zartar."
Ya yi shiru! Yana kallonta, yana jin sonta da tausayinta suna neman kassara shi.
A hankali ya ce "sanyi nake ji, da sauri ta mike ta fara kokarin ware bargo, Dan ta rufa masa.
Ya kalleta ya ce "Ba shi ba".
Zuciyarta ta buga, ta sani tun fil'azal idan yana zazzabi, sai dai ta cire kayanta ta mannu da shi, dumin jikinta shine maganin sanyin da zazzabi ke sababa masa ji.
Ta yi sororo bata san me yasa a duk sadda ya nemi ta'ba ta ba, sai ta ji wani irin bacin rai ya taso mata ba.
Tsayuwar da ta yi, yasa shi fahimtar abin da yake son ta yi masa ne, ya sake sanyaya jikinta.
Ya waske kamar bai gane halin da take ciki ba, ya sake cewa "Dan Allah".
A sanyaye ta cire rigar jikinta, ta bar pant dinta, ta isa gare shi, ta kwanta, ya yi mata wata irin runguma mai tsananin gaske.