Sashe 43
Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ai kuwa ya hassalo yana fa'din "wulakanci ki ya tashi ba? Ni kika fa'dawa wannan maganar?"
Ta kasa magana saboda a yanzu shakkarsa take ji sosai, ba kamar da ba, hawaye ya balle mata.
"Ta ce ta zo har 'dakina ta tsokane ni, bayan ka san har fa'da maka na yi akan ka yi mata togaciya, amma ba bincike ba komai, ka bi bayanta, ka rarrasheta, ni kuma ka zo kana mini jidali".
"Jikinsa ya yi sanyi, fishinsa ya sauka, ya isa gareta da nufin rungumeta, ta goce ta ce "Tun bamu je ko ina ba kana son sai na gaza?".
Ya sassauta murya ya ce "Tausayinta nake ji, bata da lafiya sosai, bata samu haihuwa ba, sannan na fi son wata akanta, fa'da mini dan Allah bata cancanci a ririta farin-cikinta ba?"
Ta zuba masa ido ta ce "Ban son wannan tausayin da ka tsananta akanta, ina jin fargabar abin da nake gani a idanuwanka akan lamarinta".
"Ni meyasa baka jin tausayi na irin haka?"
Ba ja in ja ya ce "Ina tsananin sonki Ubangiji ne shaida, kina da cikakkiyar lafiya, Ubangiji ya hore miki, kina haihuwa Ubangiji ya arzurtaki, Ubangiji ya arzurtaki da mahaifin da ba kowanne 'da ne yake samun irinsa ba.
Fa'da mini ta inda baki kereta ba".
Ya ru'ko ta, tana cigaba da kuka tana cewa "Allah ka bawa Farida haihuwa ko wannan tausayin da yake neman zame mini barazana ya yi sau'ki".
Haka ya lallabata.
Haka da Farida ta dawo, ya ja kunnanta da cewa "da bakin ki, kin ta'ba cemin kina fakar idon mutane kina tsokanarta, to ki bari tunda bata so, Nima bana so, ki kiyaye bana son muna samun sabani".
Ta tsiri fishi! Ya tattara ya watsar da ita, ya shareta, dake bame yawan fishin bace da kanta kuma ta dawo hanya.
Haka rayuwar take gudana yau fari gobe tsumma kowa ha'kuri yake yi da abin da rayuwa ta zaba masa.
A haka Allah ya sauki Sa'adah lafiya! Ta haifi danta lafiyayye mai kama da Jawad sak, kenan Mk shima ya biyo.
Kwananta'daya a asibiti aka sallamota bayan an tabbatar da lafiyarta da ta jariri.
Tana zaune a dakinta ta tsurawa jaririn ido tana ayyana abubuwa masu yawa, bai zo da wuri ba a lokacin da Mk ya matsu ta haihu, haka bai yarda ya fito a jikin Farida ba, bai kuma fito a jikin wani namijin ba, tabbas kudurar Ubangiji yawa ne da ita, duk tsawon shekarun nan sai da ya jira ya fito ta tsatsonsu a lokacin da ba a yi zato ba, Wannan ka'dai ya isa aya ga mai hankali.
Dai dai lokacin Mk da Farida suka shigo. Dukkansu suka isa gareta cike da kulawa suna yi mata sannu.
Farida ta rungume yaron da tun jiya da ta 'dora ido akansa ta ji son yaron ya shigeta tamkar ta sace shi ta gudu.
Sosai ta rungume shi, karon farko das tausayinta ya kama Sa'adah!
Mk ya dinga tambayarta ko abin da take so ko bu'kata?
Ta ce "Ba komai so dai nake yi na je gida ko kwana goma ne! Ka ga Umman Fanshekara bata jin da'di ba iya zama mini zata yi ba".
Ya girgiza kai da sauri ya ce "ba zai yiwu ba, abar maganar".
Ta yi shiru tana cewa "An barta".
Mamamki ya kama Farida ada kallon mijin ta ce take yi masa indai akan Sa'adah ne, ashe ba ita ka'dai yake hana yin wasu abubuwa ba har da tauraruwar tasa.
Tsawon lokaci sannan Farida ta mike da nufin basu guri ta ce "Tamkar na tafi da shi, tamkar na dawma ina kallonsa".
"Tafi da shi mana Farida ai d'anki ne".
Sa'a ta fàdi hakan a tausashe sannan ta mike da kyar tana janyo akawatin kayan yaron, Mk ya ce karfa ki fa'di".
Ta dire a gaban Farida ta ce "Ki tafi da shi, ki dauwama kina kallonsa,ya dauma a 'danki, ina miki al'kawari ni dai a bakina wani mai rai ba zai ji ni na haife shi ba, ke din masaniyar magaganganuwa ce, kin san wadda zaki sha ya taimaka ruwan nono ya zo miki, na shayar miki da shi na kwana 'daya da yini, ubangiji ya taya ki tarbiya da juriyar raino, ina kuma yi miki fatan ki samar masa 'kanne ta tsastonko masu yawa".
Mk ya mike da sauri ya rungume Sa'a yana jin sonta yana sake tumbatsa.
Da rawar murya ya ce"Tunda kika yi sa'a Baffah na ya haife ki, na sani zaki yi abin da yafi haka na karamci! Na gode miki sosai Ina tabbatar miki har yau din nan ke ta dabance a cikin duniyata. Allah ya miki albarka! Idan har aljannarki tana 'damfare da yardata ne, wallahi daga yau na yarje miki, daga yau din nan Ubangiji ka shaida komai Sa'adatu zata mini na kuskure, har zuwa karshen zaman mu na yafe mata, na yarda da ita, Ubangiji ka yarda da ita"
Farida tana tsaye tana kallonsu tana Jin inama itace Sa'adah! Ta matsa kusa da ita ta kalleta cikin ido ta ce "Wallahi Sa'adah kin fini kirki, kin fini hakuri, na tabbatar a yanzu da nake jin 'kaunar yaron nan ba zaan iya yin kyauta da 'da ba, koda na haifi guda goma.
Ba abin da zance miki, sai fatan alheri, Ubangiji ya fini yabawa".
Ta saba 'danta ta fice da shi, sai lokacin Sa'a ta fashe da kuka, tana jin girman 'karfin halin da ta yi.
Ya dinga rarrashinta.
Ta ce "shikenan Farida ta haihu, ta sami 'da Kamar Jawad! Sai ka daina takura shi sai ya je wajenta ya kwana, sai ka daina wannan tausayinta da yake neman zame mini barazana".
Ya sake rungumeta tsantsan yana gasgata dinbin sonsa take yi, ya sani ba macen da take sonsa a doron 'kasa irin Sa'adah, idan aka cire Hajiya.
Ya sani saboda tausayin Farida da yake yawan yi ne, ya sanya ta bada abin da yasan ba kowacce mace ce zata iya yin hakan ba.
A fili ya dinga "cewa Madallah da ke Sa'adatu, a yau na sake ganewa ke din jarumace, mai kuma 'kaunata ce, zan sake maimata miki abin da na ce ba zan sake fa'da ba.
Wallahi ban taba son wani abu a duniyata kamar ke da 'Yay'anki ba, Wallahi kune farin-cikina, kune duniyata, har na daina numfashi kece jagorar zuciyata.
Ya rasa mai zai yi mata, sai ya ce ki shirya Gobe na kai ki gida, ki yi sati uku Inna ta sake gyara mini ke, kafin ba'di ina fatan ki haifo na ki wadda zaki ri'ke a hannun ki, a dakinki".
*Wattanni shida a gaba*
Zuwa lokacin Sa'a na dauke da wani cikin na wata biyar, yayin da yaron Farida mai sunan Mahaifinta Nasir(Amir) ta yi masa alkunya, yake wattanni shida.
Yaron ya yi wani irin girma gashi fari kwal saboda farin Mk ya yi, sannan yana shan nonon farar mace, sai ya sake zama tamkar dan larabawa, irin ku'din da Farida take narkawa akan yaron abin tamkar a littafi, albashinta akan yaron yake karewa, haka Mahaifanta duk fitar da zasu yi sai anyi masa akwati guda, hatta Sa'a dalleliyar mota mahaifin Farida ya aiko mata a matsayin tukuicin sanya farin-ciki a zuciyar diyarsa.
Shayarwa ba karamin karabar Farida ya yi ba, idan Sa'a tana ganin status din Farida da 'danta wani lokacin har kusan shidewa take yi tsabar kishin yadda suke daukar ido, domin komai designer take masa amfani da shi, yaron ya zama one in town.
Haka fita goma shiga goma zata ganshi a kafadar Mk.
Idan ya shigo da shi ta mika masa hannu sai ya ki, 'kiwa yake yi mata ba 'yar ka'dan ba, tunda ko wurin aiki da shi Farida take tafiya da mai rainonsa.
A wannan lokacin Mk ya kalallame Sa'a ta ajiye aikinta, ta zama lauya mai zaman kanta, a lokacin kuma tafiya zuwa kasar Amurka ta taso masa inda zai yi kwas na wattanni shida.
Ya tisa Sa'adah ya tafi da ita.
A can ta haihu still dai boy, ta saka rai girl zata samu sai dai Ubangiji ba hakan ya so ba.
Sun more sosai a a zamansu na wattanni shida a U.S, ta gasgata Mk ba macen da ta fita a wajensa.Ta dawo da d'anta mai kama da ita wadda Baffah(Bashir) aka yiwa takwara Jawad ya ce *Jadid* za'a dinga ce masa.
*Shekaru biyu a gaba*.
Hankali kowa ya kwanta arziki da cigaba sai sauka yake yi a gidan Mk! Mussaman da ba'a yi masa tashin hankali, duk da kuma basa shiri.
Dan hatta Amir har yau bai wani sake da Sa'a ba, idan Mk ya zo da shi baya yarda ya ajiye shi, ya dinga kuka yana cewa "Malam dauke ni"
Ba zai yi shiru ba sai ya dauke shi, ko ya mayar da shi wurin uwarsa.
A lokacin Sa'a ta yaye Jadid ta haifi mai sunan Mahmoud, da suke 'Kira da Junior, ta Kuma je asibiti ta sanya loop da amincewar Mk, tana addu'ar ta yi auta kenan, duk da tana tsananin son Baby girl, mussaman da ta lura Mk ma ya matsu ta haifi yar budurwa, amma itakam ta gaji ta fahimci ita da Sumayya basu da rabon haihuwar girls har gara ma Sumayya ta samu Khairat itama kuma sai a karshe domin itace ta biyar kuma autarta.
A lokacin Ubangiji ya sua'kar da ayarsa Farida ta samu juna biyu, murnar da mk ya yi ba yar kadan bace, sosai yake tattalin ta har Ubangiji ya sa ta haihu lafiya duk da dai c.s aka yi mata, yarinyarta mace mai kama da su Jawad kwabo da kwabo mai tsananin gashi irin nata.
Bidirin da akayi ba kadan bane, tun akan Amir farida ta gane jama'a na sonta na tausayinta, haka a wannan ma aka sake nuna mata kauna.