← Book details Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 45

Sashe 23

Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ta nemi shi ta rasa amma ta kudiri aniyar yau sai ta masa dukan kawo wuka, gobe idan akace ya sake wulakanta ba'kinta zai ji shakka. Ta rasa irin wannan rashin tarbiyar da ya tsira a yan kwanakin nan.
Shikuma yana can ya buya a boys quarters.
Sai yamma lis ya fito, ai kuwa ta hango shi ta windo ta dauki wayar wuta ta fita domin ta san bata isa dukansa a gaban Sumayya ba, cewa zata yi rainata ta yi shiyasa zata doke shi akan idonta.
Cikin Sa'a Jawad ya ankara da
yadda ta tunkare shi a fusace, ai kuwa ya kwasa ya yi gate a guje, ba'kin ciki yasa ta bishi itama.
Suna fita suka yi kicibus da Mk a waje zuwan sa kenan parking ya gama yi.
Ai kuwa ya ruga ya buya bayan Babansa.
Mk ya ri'ke shi yana fa'din "menene?"
Ya kalli Sa'adah da take hawayen takaici, tana rantsuwar sai ta dake shi.
Jawad ya ce " yau zan bika mu tafi Malam kar bar ni anan duka na zata yi"
Mk ya daure fuska ya ce " me ka yi mata?"
Jawad ya turo baki gaba irin na gado ya ce " wani gajeran mutum ta ce na gaisar shine na ce ai ba uba na bane.
Shikenan zata doke ni, Ni kuma bana sonsa ne, haushi yake bani, I hate him so much".
Ya fa'da da karfi tare da buga kafa.
"Kar ka bari ta doke ni Malam domin ni sonsa ne bana yi, ba laifi na yi mata ba".
Cikin mintina kadan Mk ya fahimci dalilin wannan takaddamar tsakanin Jawad da uwar da yake mata wani irin so marar misaltuwa.
Kishin Babansa da yake yi ne sanadin da zai iya yin fito na fito da ita.
Da'di ya yi matu'kar kama Mk ashe dai soasai Jawad ke sonsa, ba uwarsa yake so ba kawai, ya lura bai son kowa ya ratsa tsakanin su, ya fi son ya gansu a tare muddin rai.
Ya ja numfashi ya kalli Sa'adah da idonta ya kuje dan tsananin bacin rai, ya yi jah tabbacin ba yanzu kawai ta yi kukan ba.
Cikin rarrashi ya ce "Wai sai yaushe zaki girma ne? Yau kuma a koke koken na ki har Jawad zaki yiwa?"
Da kuka sosai ta ce "Ai kaine ka ke hure masa kunne ka ke so ya raina Ni. Dama na san da biyu ka tattaro mini shi, to burinka ya cika. Sai dai duk abin da ya mini har zuciyata ta baci, na yafe masa, in Sha Allah ba abin da zai same shi, amma tabbas sai na zane shi, domin ai wannan ba tarbiyar kwarai ya dauka ba, ya dinga yiwa manya rashin mutunci".
Kafin Mk ya yi magana Jawad dake ri'ke da Babansa ya ce "Ni bana raina manya, ba haka kawai na ki gaishe shi ba, sonsa ne bana yi, bakon jiya da na ga mai farin gemu ne ai na gaishe shi saboda ana yawan fa'da mana mu girmama tsofaffi masu farin gashi".
Sa'a ta kai masa wawura amma ya zille, da taimkon Mk.
Mk ya shanye dukkan dariyarsa ya ce yanzu a gabana sai ki doke shi? Kin san dai bana so ko?".
Cike da shagwabar da ba ta yi zaton zata sake yiwa Mk ba ta ce " Billahillazi sai na doke shi, zaman ka lafiya ka miko mini shi".
Ta fa'da cikin dire 'kafa da goge hawayen idonta.
Ta sake cewa "Baka son na dake shi. Amma ka 'ki yi masa fa'da".
Ya ce "cool down Ummu Jawad"!
Ta katse shi da cewa "kar ka kuma ambata mini wannan sunan, ka 'Kira wadda take maka alkunya da shi".
Ya ce "To Na ji".
Amma abin da nake so da ke, ki yi hakuri, yaro ne ai, tunda dai kin rantse, to zan kubutar da ke daga yin kaffara, zaki doke shi, amma ba da wannan wayar ba".
"Ni kuwa da ita zan dake shi" ta fada da sauri.
Mk Yana so ya ce to shi ta dake shi da ita, Yana jin tsoron kar ta zabga masa ta rashin tausayi tamkar ta 'KARFI.
Ya ce "A a Sa'adah kin so ki yi rikici ne kawai, yaushe zaki dake shi da wannan uwar wayar da alamun ta suka nuna ta A.c ce. Zo ki ga yadda za'ayi".
Bata san ya akayi ba, shauki ya kwashe ta, ta isa kusa da su, domin ganin da ta yi Jawad na rungume da shi, sai ta ji tamkar ta tabbata tana ganin su a haka, sune cikon farin cikin ta, ta yarda.
Mk ya rungume Jawad sosai ya ce "Dan yi masa dundu amma ba wadda ya zarta 'kwarin 'kashinsa ba, duka duka ma yaushe kika haifo mana shine?"
Ai kuwa kamar sokuwa ta yar da bulalar ta yi masa dundu har uku, za ta yi na hudu ya ce " oh sorry ya isa haka nan, ni ma zan yi masa fa'da ai".
Ta koma gefe tana harara tamkar idon zai fa'do.
Mk ya saki Jawad da suka kankame juna tamkar zasu zama halitta guda, ya ce " shiga ciki muna zuwa".
Ai kuwa ya tafi da gudu ya na dariya. Abin da ya sake kular da Sa'adah.
Ya kalleta ya ce "wannan ka'dai ya isa ki gane shima yana dandanar azabar da nake sha idan na ganki da wani".
Ta tabe baki ta ce "Allah ya bawa wadanda aka 'ki su, ake zaune da makiyansu ha'kuri".
Ya kasa cewa komai.
Ya saki maganar da cewa "ina son azo nema mini auren ki, jiya Baffa ya ce mini wai Gogel za'a je domin Yayansa dan wan Babansa ya ce wannan karon can za'a je".
Ta murmusa sosai ta ce "Ashe duk wasa ka dauki maganata? Wallahi bana fatan zaman aure ya sake hadamu, na riga da na yarda kaddarar haihuwar Jawad da kanwarsa ya sanya na yi muku kutse cikin soyayyarka da Yar mutanen Yemen".
A sanyaye Mk ya ce"Amma ai na sha fa'da miki sunan kanwar Jawad Aisha ko? Tunda ta zo da ranta, ko bata zo da rai ba matu'kar yaro ya yi motsi a ciki to a sanya musu suna saboda zasu tashi da sunan su ranar Gobe, dan haka sunan Hajiya Babba ta ci, Nana Aisha ce ina fatan ta zame mana sanadin shiga aljannah babu Hisabi".
Sa'a ta amsa da Amin a zuciyar ta.
Ya nisa ya ce "ke yanzu da gaske kike yi ba kya so na?"
Yana rufe baki ta ce "Wallahi ina sonka Mukhtar! amma bana sonka da aure, ina neman tsari da kaddarar da zata sake hadamu. Ka sani sarai, ina da kishi, idan na dawo ma ba abin da zan tarar sai bacin rai, na ro'ke ka mu rufe wannan maganar tun da sauran mutunci a tsakanin mu".
Ya matsa sosai kusa da ita murya a dakushe ya ce "Na miki tanadin farin ciki marar yankewa, kin sani Ina son ki, son da ya zarce kwatance, kin sani har zuciyarki ban zalunce ki ba, ke ce kika musguna mini, amma ina tabbatar miki Sa'adah zan sake ninka miki soyayya akan wadda na miki ta baya, zan sake tausaya miki, zan kuma yi iyakacin kokarina ban yi abin da zai yawaita motsa miki kishi ba, na dade ina roka miki sau'kin kishi a wurin ubangijin da yake sarrafa zuciya. Ko baki dawo dan ni ba, ki dawo dan Jawad, ki dawo ko ubangiji zai azurta mu, da sama masa yan'uwa".
Jikinta ya yi sanyi sosai da kalamansa, wadanda ta tabbatar babu yaudara ko da'din baki a cikin su.
Amma sai ta waske da cewa "Ina yiwa Jawad fatan samun yan'uwa ta bangaren Farida. Domin kuwa ni dai ba da kai zan samar masa ba".
Chapter 23 · 0% Book details