Sashe 38
Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da ta huta, sannan ta yi gyatsa ta mike ta 'doro alwallah.
Ta kusa idarwa ya shigo. Ya zauna yana jan ledar gabansa dan shima ya ci, mamaki ya matu'kar kama shi, saboda ganin wanda ta rage.
Ya karasa cinyewa ya bude yoghurt ya sha.
Bata yi masa magana ba, ta sa hannu ta dauko robar ruwa ta bude ta kai bakinta.
Sai da ya kammala ya matsa kusa da ita sosai, ya ru'ko ta. Yana cewa "zo ki ji wata magana, na sani ba iya yunwar nama kike ji ba".
Ta fara ture shi tana cewa "Ni wallahi iyakacin yunwar kenan, kuma na koshi sosai".
"To ai ni ban koshi ba, tunda dai baki rage mini na kirki ba".
Ta 'ki tsayawa, shi kuma ya'ki sakinta, ganin da ya yi da gaske ba amincewar zata yi da shi cikin kwanciyar hankali ba, sai ya saketa.
Ya koma gefe ya na jin bacin rai sosai.
Jikinta ya yi sanyi, amma bata san me yasa take jin tsananin bacin rai idan ya nemi kusantarta ba.
Tsawon lokaci suna zaune ba um, ba um um, a tsakanin su.
Ta saci kallonsa ta ga yadda yake cikin fishi sosai, ta hadiye maganar da take son amayarwa.
Ya mike yana cewa "Tashi mu tafi"!
Ta 'ki yin ko da motsi, balle ta tashi.
Dan jim ka'dan! Ya nufi hanyar barin dakin yana cewa "ki same ni a mota".
Ta daga murya ta ce "Ba ka ce mini komai ba akan maganar da na yi maka 'dazu, kuma ka ce mu tafi?"
Ya dawo ya tsaya akanta fuska ba walwala ya ce "wacce magana ce? Tuna mini, dan ni na manta".
Takaici ya shaketa, amma hakanan sai ta daure ta ce "Tariyar Mana".
Kai-tsaye ya ce "Ban kammala shiri na ba, ba kuma ku'di a hannu na".
Ta fara kuka tana cewa "Ni ko ba ku'din zan tare, kar ka mini haka, so kake na kunyata?"
"To ki ta kunyata mana! Ina ruwana? idan kuma kina da yadda zaki yi da cikin dan ki tsallake kunyatar sai ki yi".
Ta dago a razane dan ta ga shine yake wannan maganar ko kuwa?. Ai kuwa suka ha'da ido, fuskarsa a matu'kar 'daure.
Ta Sanyaya murya, hawaye na zubo mata, ta ce "Haka ka ce mini?"
Take ya ji tausayinta! Ya zauna ya ce "Haka na fa'da miki Sa'adatu. Hakan kuma shine gaskiyar magana, ba zai yiwu kina wulakanta ni tun yanzu ba, sannan ki yi tunanin zan miki abin da kike so, bakya yarda da ni, na sani ko tariyar aka yi haka zaki cigaba da yi mini, dan haka ki zauna ki haihu a gida. Zuwa lokacin idan kin ji a ranki, kin shirya zama da ni bisa tsarin sharia sai na saka ranar tariyar".
Hawaye ya dinga zubo mata ba kakkautawa, a hankali ta ce "kar ka mini haka dan Allah".
Nan da nan ko ya ci laya da cewa "Wallahi ba zan yi abin da kike so alhalin har yau din nan bani da mutunci a idonki ba, inace dai jikina ne ba kya so ya rabe ki? To ba zan sake ba, zan ta siyo miki nama da yogurt da duk abin da kike son ci, nima kuma in sha Allah ba zaki ji, ko ki ga na mutu ba adalilin ba kya yarda da ni".
Ta dinga kuka sosai, ya dinga jin wani iri, ya sassauta ya ce "daina kukan haka! Ta shi mu tafi"
"Ni ba inda zani sai an tsayar da maganar nan".
"To ai na gama, sai dai tunda ni zan biki dole, sai ki tsara na ki, ki kuma sa ni biyayyar dole".
Ta goge hawayen ta ce "Na yarda ni zan bika".
Ya mi'ke ya ce "To tashi mu tafi, tunda Ni na zartar da nawa hukuncin, ba kuma zan canja ba, sai na tabbatar da gaske kin daina mini wulakanci".
Da rawar murya ta ce "Ai yanzu ma na yarda! Ba zan sake tureka ba".
Da'di ya yi matu'kar kamashi, dama abin da yake so kenan.
Da rawar jiki ya isa ya rungumeta.
Ya dinga jifa da Hijabinta da komai ma, haka ya dauki lokaci yana abin da ya ga dama da ita.
Yayin da itakuma ta ke share hawaye.
Har ya yi wanka ya fito bata bar kuka irin na sharbe ba.
Ya waske ya yi kamar bai gani ba.
Suna tafe a mota da rawar murya ta ce "Yanzu yaushe ne tariyar?"
A gajarce ya ce "sai kin daina mini kukan da babu dalili, sai na gamsu da gaske idan kin tare din zaki barni na dinga samu nutsuwa da ke".
Da kuka ta ce "kawai na gane yawo kake mini da hankali! Dan kasan ka gama da ni, inace yanzun ba abin da baka yi da ni ba, amma yanzu kana wata magana".
"Tabbas na yi, amma mai na tsinta ban da bacin rai, dame kika taimake ni? inace zama kika yi tamkar ruwa, sannan kina ta Kuka".
A matu'kar gajiye ta ce "To ai ba zan sake yi maka kukan ba".
"To zame mini tamkar gawa fa?"
Da sauri ta ce "Na daina".
"To ki bari sai na tabbatar da gaske kin daina din har zuciyarki".
Cikin kwantar da murya ta ce "yaushe to zaka tabbatar din?"
Ya dauke kai ya ce mu barshi nan da wata daya, idan yanayin biyayyar da kike mini ya gamsar da ni, shikenan sai ki tare abin ki".
Da rawar murya ta ce "idan na kara wata Innah zata gane halin da nake ciki".
"To wai ke wannan boye boyen da kike yi na menene? Abin kunya ne, Inace an daura auren?"
"Ni dai bana so a sani ne kawai".
Ya murmusa ya ce "ai dole ki ji kunya, kin gama fadin ba kya sona a gabansu, sai gashi daga dan ta'ba ki ka'dan, kin yi ciki, ai dole ki ji kunya, ina kika kai 'kiyayyar?"
Ta kasa bashi amsa.
To mu barshi sati biyu nan gaba, amma sai na tabbatar fah".
Tunda ga wannan ranar Mk ya mayar da Sa'a tamkar ya tare da ita ne, domin kullum sai ya fita da ita, ya yi abin da zai yi sannan su dawo.
Har satin biyun ta cika amma baice komai ba, a lokacin cikinta yana shirin shiga wata na uku.
Rannan suna gidan da suke yini, zuwansu kenan, ta kalle shi, ta ce na gane so kake dai sai na kunyata dole. Banda haka menene bana yi maka Kullum sai ka fita da ni, amma ka dage akan bana yi maka yadda kake so?
Fa'da mini me zan yi maka kuma?"
Cikin rashin damuwa ya ce "ba Kya mayar mini da martani kamar da can, sannan kullum na kusance ki da kuka ake karewa, ke yarinyace? Sannan ba har zuciyarki kike amincewa ba, kina yarda ne akan dole, sai dan kina son ki tare kar agane kina da ciki.
Abin da baki gane ba, ni ba abin kunya na yi ba, tunda na yi hakuri sai da aka 'daura aure, ke kika ce ba zaki tare ba da bakin ki. Babana ya goya miki baya, yanzu kuma sai ki dame ni da maganar tariya alhalin kin san inda zaki fa'di kin matsu ki tare, asa ni dole, ko bana so".
Ya nisa ya ce "ki kira Baba da bakinki kice zaki tare".
Idonta ya ciko da kwalla ta ce "Kaine zaka kira ka ce ka shawo kaina na amince, idan ya nemi jin ta bakina sai na yi shiru alamun kunya, shikenan sai ya gane ina bu'katar tarewar da gaske".
Ya tsura mata ido ya murmusa ya ce "Sannu Sa'adah! Ke idan kina son abu, kin iya shirya zance".
Daga haka ya janyota jikinsa yana kissing dinta.
Sai dai yau yana kammalawa ta dinga kelaya amai tana kuka.
Sosai ta yi, sai da ta kammala ta koma gefe ta cigaba da kukanta.
Haka Mk ya kwashe Aman nan, ya sa tissue ya goge.
Ya kalleta ya ce "je ki yi wanka".
Bata Musa ba ta mike ta shiga toilet.
Ta fito ta same shi ya yi tagumi da hannuwa biyu.
Ta zauna a sanyaye.
Ya kalleta ya ce "Anya kuwa Sa'adatu kina jin tsoron ubangiji? Anya kuwa baki kafirta ba?"
Da saurinta ta dago ya ce "kwarai kuwa! Na sani kishi ne yake son halaka ki! Amma ki sani ubangiji ne ya halasta, sannan shine ya bada umarnin a auri bibbiyu ko uku ko hudu. Aaya ce sukutum cikin al'kura'ani mai girma.
'Kin amincewa da hukuncin Allah kuwa tamkar ka kafirta ne".
Ya yi shiru yana nazarinta.
Ya nisa ya cigaba da cewa "ina jiye miki kada ki halaka kanki, ki halaka ni, Ina jiye miki tsoron kada na samu aljannah adalilin ba'kin cikin da kike ta 'kunsa mini, ke kuma ki tsince kanki a wuta.
Annabi ya ce akwai mazan da suke rabauta da aljannah adalilin hakuri da taurin kan matayensu da kaifin harshensu.
Ina jiye miki na shiga aljannah, na hadu da Farida ba da ke ba".
Dai-dai nan ta rushe da wani irin kuka, fiye da kukan da ta yi ranar da ya saketa.
Da sauri ya matso ya rungumeta, domin ya tabbatar wannan kukan ba na shagwaba ko iyashege bane, na tsantsar damuwa ne.
Bai hanata ba, ya barta ta yi, iya yinta, ganin yana neman wuce ka'ida ya sanya ya fara lallashinta da gwalagwalan kalmomin da suke nuna kololuwar matsayinta a zuciyarsa.