Sashe 45
Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read
"Menene dalilin 'Kara auren tunda ka ce Mai dakinka mai kishi ce?"
Ina so ne bayan haka kuma Kausar 'karfi Yar wajen Baba Mahmoud ne, mutumin da a tsawon rayuwata banga mai yin abota da sadaukawar irinsa ba"
Idonsa ya ciko da hawaye.
Amma ya cigaba da cewa "Akwai lokacin dana bukaci akwatin 'karfe mai alamar zanen tsaka, na rasa, saboda ya yi wahala ashe shi yana da shi tun na sakandirensa, ya manta da wani rubutu a cikinsa, Ni kuma na karanta takardar sai na fahimci son da yake yiwa mahaifana mai girma ne, sai na yi nufin cika wannan soyayyar mussaman kasancewar Iyah ce ta haife ni"
"Yau shekaru goma da ganin wannan takarda, tun a lokacin kuma na ce ina son Kausar duk da maganata da Khairat ta bayyana. Zuwa yanzu Kausar ta kammala degree dinta na farko watan jibi ne bikin mu".
Iyah da Mk da suke kallon hirar a katafaren falonta da ya shirya mata tamkar aljannar duniya ya janyota ya ce "Na lalla'ba Jawad ya fa'da mini abin da ya gani a rubutun 'karfi, sai dai ban yi mamaki don ya soki ba, domin ni da shi zuciyar mu na son abu mai daraja, na sani kuma 'karfi ba abin da ba zai mini ba, tamkar marigayi Baban Na'ibawa haka yake da alheri.
Na sake yanke shawarar ranar auren Jawad da Kausar! zan aurar da Amira, ga Dady 'Karfi, na sani Jawad saboda ke zai auri Kausar, ni kuma na bawa Dady Amira, dan Mahmoud ya gane mun san alheri kan alheri abotarsa da sadaukawarsa bata tafi a banza ba, domin ina mana fatan mu tashi a karkashin masu yi dan Allah."
Guntun hawaye ya 'balle mata tana sake fahimtar ba abu mai da'di irin hakuri a rayuwar mace mussaman akan sha'anin aure, yau da take cikin shekaru na girma, ta gane ba komai a cikin rayuwa irin hakuri da kawaici da yiwa miji biyayya a kowanne hali, ta tuna lokacin da ta yi hakurin akan zamanta da Farida mussaman sadda Mk ya bata umarnin ajiye aiki, da kuma tafiyarsa Abuja da Farida, da kyautar Amir irin habaici da 'kananun maganganun da ta sha. Tabbatas ba dan ta yi hakuri ba, da bata cimma burikanta ba, idan ta kalli Jawad kadai sai ta tsananta yin godiya ga Ubangiji! balle ga su Jadid da Junior da suke karatun likitanci a Jami'ar Heverd ta Amurka, inda kowa da bangaren da yake karanta.
Amir ne yake kartunsa a Jami'ar Bayero adalilin baya son yin nisa da Farida saboda yanayinta na rashin lafiya saosai, sannan Mk din ma yafi son sa a kusa da shi, domin har yau din nan Jawad ne kawai ya fi Amir a zuciyarsa, a duk sadda ya tuna zazzafan rabo ne Amir a wajensa shi da Sa'a sai ya yi ta godiya ga Ubangiji da ya rufa musu asiri suka haife shi a karkashin aure.
Haka aka yi shagalin auren Kausar da Amira, Mk da Mahmoud suna jin tamkar Dan su kawai aka halicci farin-ciki.
Sosai Sa'a take yi yiwa surukanta soyayya da adalci irin yadda Hajiyar Bichi ta yi mata, dama Kuma Khairat yarta ce da Sumayya ta haifa Mata, ga kuma Khausar diyar Mahmoud.
Ba a fi sati biyu ba ya wuce da amaryarsa America, inda gida kowacce daban, duk da dai compund dinsu daya.
Adalci yake yi musu tamkar Mk, duk da shi Jawad Yana rasa gane wa ya fi so domin kowacce ta yi masa, tana daukar hankalisa.
Mk da Sa'adah zaune gaban Hajiyar Bichi da ta tsufa sosai, sai dai da'di da gata ya hana tsufan galabaitar da ita, ta ce "Na kan yi mamaki idan ina tuna kamar yau nake muku shari'ar rikicin da kika dinga yi akan kishi, sai kuma Ubangiji ya 'kaddara sai an yi miki din, amma da kika yi hakuri, Kika zama adalar uwargida mai sadaurkar irin Hajiya Babba! sai Kika cigaba da jan ragamar mijinki, da uwarsa har da gidan gaba'daya, dukkan wani haske da ni'imomi ba wadda Ubangiji bai miki ba, har yau din nan kuma ke ce jagora a wajensa, Ni shaida ce, akan bai so wata a duniya irin ki ba, yake kuma kan sonki.
Madallah da mata masu hakuri, madallah da adalar uwargida, madallah da miji adali, Ubangiji ya tsare ku, ya tsare zuri'arku, Ubangiji ya sa 'ya'yanku su ri'ke ku kamar yadda kuka ri'ke mu".
Suna murmushi, suka amsa da
"Ameen"
ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH.
*UBANGIJI YA SAKE HADA MU CIKIN WANI LABARIN, DA NAKE FATAN KU KAR'BE SHI TAMKAR HALIN YAU.*
*ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAHI WA BARAKATUHU*
GAISUWAR SADA ZUMUNTA DA MARUBUTA
*HAJ SALIHA A A ZARIA
HAJ HAFSATU SODANGI.
HAJ ZULAIHATU KAGARA.
SUMAYYA TAKORI.
FADILA LAMIDO.
BINTA ABBALE.
HASSANA 'DANLARABAWA
ZAINAB MAZAWAJE.
RABI'ATU SHITU.
*SURAYYA DAHIRU GWARAM*
Mrs
*Mukhtar Nashe*.