Sashe 13
Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kotu ta 'dage sauraren shari'ar Alh Ibrahim Hassan zuwa 28/6 a shekarar da muke ciki, wattanni biyu masu zuwa. Duk da adalilin Khalil ta rasa aurenta ta kudiri aniyar tsayawa mahaifinsa da dukkan iyawarta ko dan ta nunawa Khalil martanin kaunar da ya da'de yana yi mata da tarin hidimar da ya mata a rayuwa, ta tuno sadda suke FGC Kano ku'din break din Khalil akanta yake karewa, ta sake tuno sadda zai kwaso abaya da lace tsadaddu da mahaifiyarsa take siyarwa ya kawo mata. Har gate ta bisu ta gaisa da iyayensa tana jaddada musu su kwantar da hankalin su zasu yi aiki tukuru har komai ya zama tarihi. Suka yi musayen lamba da Khalil. A gajiye ta isa gidan Sumayya, amma haka ta yi wanka ta Fara shirin tarbar Anwar da zai kawo mata ziyara. Anwar bashi da mace amma ba saurayi bane, ya yi aure wata sha'daya da auren matar ta zo haihuwa ta rasu ta bar yaro yana hannun kakarsa wadda ta haifi marigayiya. Shekaru hudu kenan, tun akanta kuma bai sake kula kowacce mace ba, sai SA'ADAH da yake sonta sosai, duk da dai har yanzu bai samu cikakken hadin kai daga gareta ba, amma dai yana ganin cigaba. Anwar Ma'aikacine a ma'aikatar zabe(INEC). *Bayan wata Daya* Zuwa wannan lokacin Mk ya kasa gane manufar Sa'adah domin tun ranar da Baffah ya sa ya kaita gidan, Sumayya bai sake ganinta ba, a rana yana kiran layinta kamar sau biyar amma bata 'dagawa wani lokacin ma zai kira ya ji tana waya, amma da za'a jima ya sake kiran sai dai ta gama ringing ta katse, tun baya jin damuwa sosai har ya fara ji har cikin ransa. Ranar Talata yana zaune a bakin shagonsa kawai ya hango wata dalleliyar mota ba zato yaga Iyah ta fito sanye cikin shigar lauyoyi, kyau iya kyau ta yi daga nesa ya hangota amma ba karamin kwarjini ta yi masa ba. Bai gama hasashen da wa suke tafe ba, kawai sai ya ganin wani matashin namiji y fito cikin fararen kaya kal, ba shi da gajarta amma sa Mk zai jera da shi sai aga gajartar tasa tunda Mk dogone mai cikakken jiki. Ganin da ya yi matashin yana nuku nukun shiga gidan sai ya gane bazawarinta ne, domin sai da ta Fara shigewa sannan ya bita a baya, Mk bai san ya akayi ba sai ganin sa ya yi, ya tsallako titi yana leka gidan su Iyah, Bai gansu a zaure ba, kenan ciki suka shiga wani irin azabben kishi ya mamaye masa kalbinsa, ya matsa ya zauna a shagon faci na jikin gidansu, jikinsa ya dinga shaking wato har fa'da masa ta yi tana son namiji cikin fararen kaya? Shiyasa ya mata kwalliya da su. Duk addu'ar da ta zo bakinsa sai ya yi amma baya iya yinta cikakkiya, Karin tashin hankalinsa da Baffa ba ya nan yana Gogel, tunda daminace, shiyasa garin yake da dan sanyi, amma Mk sai zufa yake yi. Mintina goma ya ji fitowarsu ya yi maza ya juya gefe daya, yana kallon kyakkawan matashin da ba zai nuna masa komai ba sai tsayi da shekaru, a kiyasin Mk zai iya bawa Anwar shekaru talatin da bakwai, shikuwa shekaransu arbain har da biyu kawai dan yana yawan motsa jiki ne ake ganinsa tamkar Yana cikin early 30th ne. Ba bata lokaci Anwar ya ja motarsa ya tafi, Mk ya na zaune yana jin tamkar ya bi wannan matashi ya masa dukan kawo wuka, Sai ya ga wani saurayi da ba zai wuce sa'an Ahamad ba, ya zo akan mashin. Ya kafe mashin din ya fito da wayarsa Jim kadan ya Kara a kunne, ya ce "na iso". Ba jimawa ya ga Sa'adah ta fito cikin dogon hijab har kasa, ta karbi ledar ta mi'ka masa kudi, kafin ta juyo Mk ya yi wuf ya mi'ke ya isa kofar zauren nasu, tana juyawa ta ganshi, zuciyarta ta buga ta rasa gane wanne irin abu ne duk sadda zata ganshi sai ta ji wannan bugun zuciyar. Kai tsaye zata shige ba tare da ta nuna ta ganshi ba, ya jah Hijabinta tare da cewa " kina nufin Baki ganni bane?" Ranta ya baci sosai ta fincike, cikin gatsali ta ce " Mukhtar bana son wula'kanci ko da nake bin maza nake Ballagazaci, ai ba cikin gidan da ubana ya samar da ni nake yinsa ba, kar kuma ta'ba ni, iskancin da nake yi ba da irin ka bane, da yara ne sa'anina wato matasa irin Ahamad dinka". Ya kai mata wani irin bahagon mari, ta yi maza ta goce ta bar shi da marin iska, a kufule ta daga ido ta zuba masa nata, ta tsorata da yaddda ta ga idonsa ya yi jawur, zuciyarta ta sake bugawa Amma duk da hakan sai da ta yi jarumtar cewa "A da ne ka dake ni ka kwana kalau Mukhtar amma a yau ina rantse maka da Allah da ka mare ni da ka ga 'kwanjina domin kuwa sai na gurfanar da kai gaban Human Right". Ya juya tamkar tafiya zai yi, sai kuwa ya juyo ya kaiwa bakinta damka ya murde da iyakacin karfinsa, yana fa'din ai tunda kin riga kin tsufa ba zai yiwu ki dinga mini kaifin harshe ba, jikin ki ne zai fa'da miki. Cikin kishi mai yawa ya ce "ki je ki kai ni court of appeal, ko kuma ki sakaye ni a gidan gyaran hali na muddin Rai karshe dai na san ba komai ya saki hakan ba sai kishin na auri first love Dina". Hawaye ya goce mata ta ce "Me zan yi wa kishin, ina abin kishin ya ke?" Ya make kafada ya ce "kin fi kowa sanin inda abin kishin ya ke? wato har kin yi ilimin da za ki kai ni Human Right ko? Ina rantse miki da Allah sai na raba ki da wannan damar". Ta yi tsaki ta ce "Bismillah". Gaba'daya ya damkota ya jijigata idonsa ya ka'da da wani irin karfi saboda yadda taga idonsa ya juye nan kuwa wani irin tsumin kishi ke huda masa zuciya. Ya ce " Ni Kika yiwa tsaki? ta yi kasa da kanta ta kasa magana saboda yadda ta razana, ta san baya son tsaki. Ganin da ya yi ta dan risina sai ya saketa ya ce "Wa ye wannan da ya kawo ki a mota? Anya Sa'adatu ba zaki bar zuciyata ta huta ba? Na fa'da miki ban son na gan ki da kowa shine kika dauko wani gajeran yaro kika zo da shi, kuma kin san zan iya ganin ku?" Nan ma shiru ta masa tana jin haushin yadda ta kasa tafiya ta barshi, zuciyarta tana bada ita da yawa. Zuciyarsa ta dinga zogi tamkar ya curo ta, ya daure ya ce "Baffah na dawowa zance a daura auren nan tun ban janye komen da zan yi da ke ba, na san dai sadaki kawai za'a ce na kawo, ko yanzu na ruga shago zan hado dubu ashirin dan baki wuce hakan ba". Hawaye ya balle mata ta ce "Dan Allah ka janye komen dan kuwa ba sonka nake yi ba, maganar ban wuce dubu ashirin ba kuma, idan ka so ka ce sadaka ce ta dace da Ni, ina ce kai kana da wadda ta cancanci kudade masu nauyi?" Ya saki murmushin da Babu nisha'di ya ce "kwarai kuwa, kin san dai fari da tsayin amaryata kadai ya isa namiji ya biya kowanne irin farashi domin irin sune na shiga gaban mota, idan kuma kana gida a maka kwalliya da gashi yala yala kana jin ka tamkar kana tare da balarabiyar Yemen". Hawaye ya balle mata, har da shesshekar kukanta, shi kuma ya dinga jin dadi, domin ya san har abada shi da Sa'a suna son juna dan haka dole su ji kishin junansu, akan dole yake yin hakan dan sai yafi samun lagonta a maimakon ya yi ta rarrashi tunda ya san bata biyuwa ta da'din rai. Kafin ya yi magana ta ce "idan ma Balarabiyar Saudiya ce ina ruwana, sai dai kuma na san banbancin jikinta da zagarniyar dabino kawai numfashi ne, ta fa'da hawaye ya na sake zuba". Jikinsa ya yi sanyi ya ce "very sorry my sweet Sa'adah". Haka kawai ya fa'da kukan ya zo mata gaba'daya ta dinga yinsa saboda yadda ta ji kishin maganganun da ya yaba mata "Yi hakuri mana tunda na bata miki Rai ki yi ha'kuri, shiga ki dauko mani abin zama, zance na zo, ai ba maganar kuka tunda dai kin san nafi son ina kamo halittu suna cika mini hannu, zangarniyar dabino ai kawai ta fashion ce". Ta goge fuskarta ta ce "da wa zaka yi zancen?". Kai tsaye ya ce "Sa'ade". Ta ce "bani da muradin ka, je ka dauwama da ta shiga mota, ni ma ubangiji ya bani rabona". Da sauri ya ce " zuciyata ta gama yarda tunda kika shafe wannan lokacin wani bai yi mini shigar sauri ba, to kuwa tabbas ni ka'dai ne zai mallake ki, ada na kudire idan na dawo na tarar kin yi aure zan nemo Safina na aureta, amma tunda kin cigaba da jirana to na fasa da Safina, dan haka ki ajiye duk wani borin da kike da nufin yi mini yanzu da sunan jana a kasa, ki adana idan an shafa fatiha sai ki ta yin su ni kuma zan ta lallashinki da allurorin kauna kala kala". Kawai sai ganin ta ya yi ta zube a kasa tana kuka sosai tana tirza kafa ya dinga kallon ta yana murmushin ashe dai har yanzu bata girma ba, zai mata komai ta shanye amma idan ya jingina kansa da wasu matan sai yaga gazawarta da rauninta, bata iya jan aji akan kishinsa, ya yi amanna ba macen da take son sa kamar Sa'adah. Da wata irin murya da sai suna cikin mayafi guda daya yake yinta ya ce " Yi shirun ki Ummu Jawad ai na fasa, kuma ma wasa nake miki ai na san karatu kika tsaya yi, ba Mukhtar kike jirah ba". Ya sake cewa duk girman laifin da kika mini ai dai bana kin daukar wayar ki, na ro'ke ki ki dinga amsa kirana, idan kuma kin ki jin rokona Ina tabbatar