← Book details Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 45

Sashe 26

Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ya zuba mata ido yana kallon yadda ta ke cika tana batsewa ya saki ajiyar zuciya mai zafi ya ce "A gaban kowa kike fadin ba kya sona, Ni kike wulakantawa haka? Kada kishi yasa ki manta ke ce kika mini laifi?"
Da kuka ta ce "Ni na maka laifi tabbas, ka kuma hukutan ni, to menene kuma ba sai a barshi a hakan ba, gaskiya kun matsa mini, tsakani da Allah kun shiga rayuwata, sau nawa zan fa'da maka bana sha'awar sake rayuwa da Kai? Na ha'kura, na bar mata, Ni ma ka bar ni, Dan Allah".
Kafin ya yi magana ta sake cewa "kafin ka aure Ni ka kira ni Ballagaza, na yi hakuri saboda ina ta'kama da Budurci, yanzu kuma ka ce ina ha'intarka, fa'da mini dame zan kare kaina, tunda ba ni da Budurci a yanzu?"
Da sauri Mk ya karaso kujerar da take zaune, ya zauna a hannun kujerar ya sassauta ya ce " Na da'de ina fada miki, bacin rai ne, ba ina nufin haka har zuciyata ba, ki yi hakuri. Na janye kalamina, wallahi tallahi ke din katangaggiya ce, ki bar wannan maganar, ko tunawa bana so, hankali na tashi yake yi. Na janye! Na janye! Na janye Dan Allah a rufe wannan maganar har abada".
Ta dinga kuka sosai mai cin rai, ta kasa cewa komai.
Ya nisa ya ce" kukan ya isa haka, ki yi hakuri ina fatan wannan ne kukan ki na karshe akan wannan matsalar".
Ta kifa kanta a dayan hannun kujerar tana sake tsananta kukan sosai, Ta ce "indai baka rabu da ni ba, na tabbatar zan dauwama ina kuka ne, domin zan rayu ina raba ka da wata ne, Ni kuwa da haka gara na auri me mata uku na zama ta hudu".
Mk ya rasa mai zai yi, ko ya ce, gaba'daya tunaninsa gaba'daya ya kulle.
Ya tabbatar auren Farida ne cikas dinsa a gurinta, shine yasa ta kasa amincewa da shi.
Ba yadda zai yi akan Farida kuwa domin bai aureta dan ya saketa akan wani 'karamin dalili ba.

Ya sassauta ya ce "Yarda da 'kaddara na cikin sharuddan cikar imani, ki ture komai, ki kalle ni har yanzu ba abin da ya canja na soyayyar ki a tare ni, ki bani amanar kan ki wallahi ba zaki yi nadama ba".
"Ko yanzu kika amince mini, wallahi na sha wahala, na azabtu, yanzu haka ina daf da kamuwa da ciwon zuciya, ba komai bane ya janyo mini ba, illah ganin ki da wasu mazan".
Ya sauko ya dur'kusa a gabanta karon farko ya ce "Ga ni akan guiwata, ki yi hakuri, ki yafe mini, ki sake bani wata damar, ni na san kina so na. Plz Sa'adah let Gone by gone, ba zan iya wannan rikicin ba, na horu hakanan, ki fa'dawa Baffa mun shirya, na kuma kawo miki Baba Isa gaban ki, ki fa'da masa mun shirya, kin yafe mini, Ni kuma na miki al'kawarin zaki rayu cikin soyayya mai wuyar samu a Yau".
Ta dago ta kalle shi a durkushe a gabanta, da'di ya kamata, amma sai ta waske ta ce "Ni fa ba zan yafe ba, matu'kar ba wani ne ya aure ni ya ta'ba ni kamar yadda kake ta'ba wata macen ba".
Ya mike da sauri ya ce "shikenan, dama ke ai ba'a taba rarrashin ki, kin gamsu cikin da'din rai ba, kaddara ce ta hau kaina ban kuma isa na kauce ba, tunda kin kasa fahimta shikenan, amma ki sani idan fa 'kaddara ta gwada iko akan ki, kika dawo mini, ba zan gamsu kin mini uzziri ba".
Ta tura baki gaba sosai ta ce " Da ikon ubangiji ma ba zata faado kaina ba".
Ya koma ya zauna a inda yake zaune tun farko yana tunanin mai kuma zai yiwa wannan yar darun ta fahimce shi, shi tashin hankalinsa daya ya ganta da wani, ba dan haka ba, da ya daure ya kyale wannan yarinyar da take neman manna masa ciwon zuciya.
Sun Jima a zaune ba um bare um um.
Ya mike ya ce "zan tafi ina fatan idan na kira wayar ki, ki dauka.
Allah ya huci zuciyarki".

****
A cikin wannan yanayin shari'ar Sanata Ibrahim Hassan ta sake zagayowa, bayan doguwar muhawara da tarin hujjojin lauyoyinsa, kotu ta wanke shi daga dukkan tuhumomin da ake yi masa.
Sa'aadah ta bukaci a bashi naira miliyan hamsin a matsayin diyyar bata masa suna da lokaci.
Jajircewar da Sa'a ta yi a wannan shari'ar yasa sunan ta ya shahara, ta yi farin jini.
Har gida Mai girma Sanata ya aiko mata da dankareriyar mota kirar Toyota Camry new modern.
Direbansa da wasu yaransa ne suka kawo, suka danka a hannun Baffah. Bayan sun yi godiya a madadin Sanata.
Washagari asabar Khalil ya mata wayar zai zo ya mata godiya tare da ban gajiya.
Saboda jidalin Mk ta masa kwatancen gidan Sumayya dan kar ya zo shago ya hango ta da Khalil, duk da a gidansu ta kwana. Sai bayan azahar ta tafi gidan Sumayyan tunda ya ce sai bayan la'asar zai zo.
Aikuwa ana idar da Sallar la'asar ba jimawa ya iso, sosai suka sha Hira, wani lokacin kuma suyi ta jifan junansu da kallon kauna sai kuma a waske da murmushi, tabbas soyayya bata tsufa sai dai masoyan su tsufa.
Amma Sa'a ta 'kudire ba zata auri Khalil ba, domin ta san komai na iya faruwa da Mk a sanadin hakan.

Da zai tafi ya ajie mata envelope mai dauke da dalar amurka, wanda idan a kiyasin naira zasu iya kaiwa dubu dari biyar.

Ya yi ta mata godiya tare da cewa "Na so kwarai ace na aure ki, sai dai jiya Mum 'dina ta tabbatar mini Yar kanwarta ta zaba mini, bijirewa ta kuma na nufin lalacewar al'amurana, na sani har na mutu ba zan daina son ki ba, sannan tsayiwar ki, kadai kan mahaifina ya tabbatar mini da cewa tabbas baki manta ba, duk irin kaini 'kasa da Mk yake ko wa, da ya yi"
Tana dariyar wai ya manta sunan Mk ta rako shi har wajen da ya ajiye motarsa, Suka sake tsayuwa a wajen adalilin ya ce zai shiga gidan Madugu wurin abokin karatunsa a Egypt.
Suna tsaye motar Mahmoud ta tunkaro su, zuciyar Sa'a ta buga, kafafuwanta suka dinga barazanar kada ita. Mk dake gaban motar ya ji tamkar ya sume, mussaman da ya tabbatar Khalil ne wannan zabgegen saurayin ya girma sosai.
Suka hada ido amma Khalil sai ya dauke kai bayan ya galla masa kallon raini tamkar shekarun baya. Har zuwa yau bai ji zai iya kallon Mk a matsayin malamin sa ba, sai dai a matsayin dan fashi a soyayya.
Wannan kallon ya sake rikita Mk, domin yasan na rainine tsantsa. Yayin da Sa'a bugun zuciyarta ya tsananta, tana raya ina ma motar Mahmoud ce mai tint?
Mai gadi ya bude musu gate Mahmoud ya ja suka shiga, ya juya ya ga Mk yana wani irin numfarfashi, tamkar ya samu attack na asthma.
A farko 'karfi ya dauka abin Wasa ne sai da ya ga Mk ya sume sai kawai ya ja motar a kidime zuwa asibiti.

*
Suna tsaye suka ga mai gadi ya bude musu kofa, Mahamud ya fito a guje kana ganin tukin da yake yi kasan babu sukuni a tare da shi.

Hankalin Sa'a idan ya yi dubu ya tashi, Khalil ya kula da yanayinta ya ce, ina son ki sosai, ke kuma kina son wanccan wicked man din.
Ya'ke kawai ta yi, ba tare da ta ce komai ba.
Ya juya ya fara tafiya yana cewa" sai wani lokaci, muna godiya, kwarai da gaske".
Da azama ta juya itama tana jin tamkar ta yi ta zunduma ihu, ya ya zata yi ne?
Ta san ganin Khalil tare da ita means alot a wurin Mk.

* **
Suna isa Asibiti aka shiga da shi dakin agajin gaggawa wato (emergency). Likitoci suka rufu akansa ana kokarin shawo kan matsalar, tsawon lokaci kafin a samu numfashin sa ya dawo, sai dai ba dai dai ba, Dan haka dole aka saka masa na'urar sau'ka'ka zukar numfashi (oxygen).
Sai dare 'karfi ya sanar da Farida da Abbas halin da ake ciki.
Dukkansu sun yi jigum jigum a asibiti suna kallon Mk a kwance bai san wanda yake kansa ba.
Farida sai fama take da tissue tana goge hawayen da ya kasa tsayuwa a idonta, ta dade da sanin mijinta bashi da lafiya, ta Dade tana jiye masa shiga irin wannan halin, adalilin kullum yana cikin rashin sukuni, ta dinga jin haushin Sa'adah na kamata, ta tabbatar ita take son kaishi barzaku dan kawai ta musu biyu babu.
Hajiya kuwa sai da gari ya waye aka sanar mata, ta isa asibitin cikin tashin hankali, ta kalli yadda ya ke shimfide akan gadon asibiti, ya zabge sosai, dama ya dade a rame Amma yanzu ramar ta bayyana karara.
Haka suka tasa shi a gaba masu addu'a na yi, masu share hawaye na yi.
Chapter 26 · 0% Book details