← Book details Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 45

Sashe 33

Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jikinsa ya yi sanyi, tabbas gaskiyar Baffah ne akwai abubuwa da yawa da Sa'a ba zata canja ba, domin a jininta ne, gashi dai a zahiri hankali ya shigeta, ilimi ya ratsata, Amma kishi yasa agabansa ta karyata shi, ba shayi ko shakka.

Wanda shi kuma ba zai ta'ba yarda ya sake daukan kaifin harshenta ba, a yanzu da take shekaru talatin da biyu.

Ya mike ya ce "Ni ne mai fa'dar tatsuniyar karya? Ni Kika karyata, nine makaryaci?"

Ta saci kallonsa, ta ga yadda ya bata rai sosai, ta yi shiru tana jin guiltiness na kamata, amma ta kasa bu'de baki ta ce masa sorry.

Ya kada kai ya ce "Tabdi jam ashe kuwa da sauran ki".

Dai dai lokacin Inna ta fito tsakar gida taga zogalen da ta ajiye wa Mk, yana gurin dan haka ta bude baki ta ce "Iyah zo ki daukar masa zogalen nan mana, nasan shi da son zogale".

Farin ciki ya mamaye Mk! Ba dan komai ba, sai dan sassaucin da yake gani tare da Innah.

Da azama ta amsa, ta kuma mike ta fita duk a kokarinta na kar Inna ta zargi wani abu.
Ta dauko ta ajiye masa a inda yake tsaye, kamshinta ya cika masa hanci, da ta sunkuya ajiye masa zogalen, ya ga yadda siket din jikinta ya matu'kar fito da taswirar mazaunanta, sai ya matu'kar kidima, ya dinga kokawa da zuciyarsa domin kuwa, ba zai sake kulata ba, har sai ta bashi ha'kuri.

A kausashe ya ce "juye mini a leda sai naje gida zan ci".

Ta sake juyawa ta fita! Tana jin tamkar ta bashi ha'kuri ya fasa tafiyar, ta sani badan maganar da ta fa'da ba, da sai anyi kiran sallar azahar da ya tafi, haka Kuma zai ta zama yana rarrashinta da son ya jagwalgwalata.

Amma yanzu zai tafi gurin matarsa, ya barta da kewa da bacin ran zuciya.

Ta hango shi ya zaunar da Farida a cinyarsa yana bata zogalen a baki, tunda ta san shi da son dora mace a kan cinyarsa.

Tana juye masa a ledar ta ri'ke, ta kasa bashi, kawai ta saka masa kuka.

Ya yi sakare yana kallonta, yana ayyana ko sai yaushe zata daina kukan banza marar dalili, ya sani tafiya gida da ya ce zai yi ne ya mata ciwo.
Tabbas kishinta ba zai bari su yi amarci mai da'di ba, ba zai bari su rayu cikin farin-ciki ba.

Shikuma ya riga ya kudire duk runtsi ba zai rabu da FARIDA ba, zai yi kuma dukkan kokarinsa ya ga bai tashi a sahun masu shanyewar barin jiki ranar gobe ba.

Wahala ne dai zasu dandana shi da ita tunda idan ranta ya baci, ko idan ya ganta cikin rashin nutsuwa shima hakan zai zama marar nutsuwar. Domin ya tabbatar itace jagorar farin-cikinsa.

Ya daure ya kore raunin da yake neman sawa ya fasa tafiyar, ya kalleta sosai ya ce "Zaki san kin ce mini makaryaci, na rantse miki sai na miki abin da gaba idan zaki mini magana, sai kin tauna harshen ki sosai. Godài godài da ke amma lafazinki na yara 'kananu, ko Farida ai ba ta mini irin wannan iyashegen".

Ai kuwa ta fàdi kan shimfidarta ta fashe da kuka, tana cewa "Na gode da cin fuska, kullum sai ka mini gorin na tsufa, saboda kawai na haifar maka Jawad! to wadda kake yiwa kallon 'kuruciya saboda Ubangiji ya jinkirta mata haihuwar ta girme ni da shekara guda, domin ina Sha bakwai na kammala sakandire, ita kuwa Sha takwas cif. Amma saboda son sai ka nuna itace mai daraja shiyasa kake bata kuruciya, ni ka maida ni tsohuwar mace, to koma menene dai, kai ka zuke mini komai, sannan daga kai har ita dukkanku kun girme mini".

Ya Galla mata harara tare da cewa "Sokuwa marar wayo kawai, wacce ba abin da ta iya sai kaifin harshe da kukan banza".

Ya juya ya fice, bayan ya dauki wayarsa a inda ya tashi, ya barta tana kukan banza nata.

Sai da ya yiwa Innah sallamah, sannan ya fita.

Ya fito ya bu'de but din, ya samu almajirai biyu, ya dinga basu kayan suna shiga da shi. Sai da suka kammala ya basu dari biyar ya ja motar sa ya yi gidan Hajiyar Bichi.

Ya isa ya tarar da Hajiya cikin Shirin fita unguwa, ya zauna ya gaisheta, ta amsa da murmushin da ya jima bai ga ta yi masa irinsa ba.

Ya murtsike kunya ya ce "Hajiya ki yiwa 'yarki magana, tana nemana da jidali, ta fa'dawa Baban Na'ibawa ba yanzu, zata tare ba, saboda Allah wanne shiri zata yi? Tunda tana jin maganar ki, ki mata magana, wannan ai tsokanar shari'a ne, an daura aure mace ta cigaba da zaman a gidansu".

Hajiya ta daure fuska sosai! Ta zuba masa ido na tsawon lokaci, shikuma ya sunkuyar da kansa kasa, ba dan ya yarda ya yi laifin da take masa kallon tuhuma akansa ba.

Ta nisa ta Nuna kanta ta ce " Ni ka zo kana fa'dawa wannan maganar? Shi Babanku kana jin nauyinsa, kana ganin mutuncinsa shiyasa ka kasa cewa komai a gabansa, sai ni da ka raina zaka zo ka yiwa rashin ta ido?"

Ya kuwa maze ya ce "To ni ya zanyi ne? ni wallahi ki yi magana, bana so a kaini bango, ban so na fusata, dan kuwa komai yana iya faruwa".

Mamaki ya kamata, ko da yake a halittar maza ne, idan suna son abu idonsu rufewa yake, ta yadda zasu iya murje kunya su yi abin da za'a dauki shekaru ana Jin nauyin abin da suka yi din".

Ta rasa inda zata sa ranta don kunya, domin kuwa ta gama gane tsananin zakuwar da ya yi ya kebe da Sa'a.

Amma sai ta ce "To tashi ka fitar mini, ai kaga fita zan yi".

"Kwanciya zan yi, na huta, ki je ki dawo, bana Jin da'di ne da na Kai ki, ko ki zauna na Kira Abbas ya kai ki".

"Wallahi ba zaka kwanta mini a gado ka mini sake sake ba, ko kunya ba ka ji, ko Jawad idan yana kwance wataran takura nake yi, bare kai, baka tashi zuwa mini sai ka yiwa yarinyar arziki rashin kyautatawa. Dan kawai kasa na ga bekenta, to nikam har yau banga laifin Sa'a ba, sai nauyinta da nake ji".

Ya mata shiru ya dauki ledar zogalensa ya fice, tunda ta riga ta rantse ba zai kwanta ba.

Ya fita yana fa'din "Na tafi Hajiya, Sa'a ta ri'ke ki gam, ta tattare komai a gunki, ai shikenan, nima sai na hada kai da Farida baiwar Allah".

"Komai zaka fa'da, ka fa'da ni Farida bana ganin laifinta, bata mini komai na laifi ba, Nima kuma na sani bata kuka da Ni, sai dai kuma ko kai wallahi baka fi mini Sa'a ba".

Ya fita yana cewa "ai shikenan sai ta zuba ruwa a kasa ta sha, ta nema ta samu fitinanniyar yarinya kawai".

****

Sai da ta aka yi sallar la'asar sannan suka bude kayayyakin da Mk ya jido Mata, wadda kayan shayi, da sabualan wanka mai tsananin gyara fata na *OLAY* *(quench)* ya hado mata setin su har da bath gel dinsa, da mayukansu.
Sai kayan ciye ciye na gwangwani kala kala tamkar zata bude kanti.
Indomie da kwai suma ga su nan birjik.

Inna ta yi galala ta ce " ban gane wannan siyayyar ba, kuna nufin haka zaku zauna, ba za ki tare ba? Dan na ga wannan kayayyakin yana nuna cewa ba yanzu zaki tare ba".

"Eh Innah ni na ce ba yanzu ba, domin ai ban shirya komai ba".

Ta nisa ta ce " Kika yanke hukunci babu shawarata, ko ta Yayarki saboda kawai kin zama uwar kanki! Ki sani to ba dabara kika yi ba, tunda an riga an daura aure, ai ba abin da shari'a bata bashi dmaa ba, bijirewar umarninsa kuwa ai kin san yana nufin tsinuwar mala'iku ne akan ki.
Haka kawai sai kin janyowa kanki ya gama zumudin ki, a titi, ke dai naga sadda zaki yi aiki da lura".

Kunya ta kama Sa'adah! Amma ta waske da cewa."To yanzu Inna sai a sake kai ni ba kayan d'aki alhalin yanzu Ina da kishiya?"

Ta fa'da a shagwabe.

Dake Innar mace ce nan da nan ta yarda da ra'ayin Sa'a na bai kamata ta je babu kayan d'aki ba alhalin tana da kishiya diyar masu kambun susa.

Ta nisa ta ce " Bari Baffan ku ya zo sai a siyar da dayan filin da ya rage, sai ki hada da albashinki na watan nan tunda ya raba tsakiya, ki yi abida ya sauwaka ayi tariyar nan cikin girma da arziki".

Ta turo baki gaba Inna ki bari dai nan da wata uku, kinsan ai na ce na barwa Baffah kyautar filin, yanzu kuwa ai ba zan koma na ce na fasa ba".

To kayan Baffanki ai naki ne, Ina jiye miki tsiyar namiji Iyah! Muutar din nan fa na riga da na gane shi bashi da kunya ko ka'dan, ba abu mai wahala bane a gidan nan ma, ya yi abin da ya ga dama tunda Baffanku ya daukake shi ba ka'dan ba".

****
Kwanakin mako da zuwan Mk wurin Sa'a har yau bai sake zuwa ba, bai kuna yi mata waya ba, abin da yake ta cin ranta kenan, ya sake tunzurota, idan bata tare ba, ai dai tana da hakkin ya duba lafiyarta, wato ya kawo mata kayan abinci saboda ita ci kawai ta sani da kwalliya.

A na cikin haka wata waki'ar ta kunno a jahar Sokoto inda aka samu matasa sun kasa ha'kurin hukuma ta dauki doka, saboda an tabowa musulmi inda basa iya ha'kuri matu'kar aka tabo wannan matsayin.

Dukkan hankalin musulmai a tashe yake an zuba ido, an kasa kunne domin aga irin hukuncin da za'a yiwa wadannan matasa.

Kungiyoyin musulmai kashi daban daban sai kiraye kiraye ake yi akan akaiwa matasan nan dauki.

Kungiyar lauyoyi musulmai reshen jihar Kano ta bawa wadanan matasa lauyoyi hamsin da suje su harci zaman kotun da za'a yi a gata, su kuma basu kariya.

Cikin wadanda aka tura har da Sa'adah.
Chapter 33 · 0% Book details