Sashe 1
Halin Yau Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*HALIN YAU*!
3
*Na*
*SURAYYA DAHIRU GWARAM
(Mrs Mukhtar Nashe.)
*Bismillahir Rahmanir Rahim*
*Ina farawa da sunan Allah, ina neman tsari da rubuta 'Barna! Ina rokon na yi rubutun da za'a 'karu , ayi amfani da shi.Tsira da aminci ga shugaba Annabi(S.A.W.).*
* JAN KUNNE*
*Gaba'daya Wannan labarin kirkirarsa aka yi(Fiction)!haka sunaye da garuruwan da ke ciki bana kowa bane, an zabe sune kawai dan 'kawata labarin, dan haka duk wadda yaci karo da abin da ya yi kamacanceceniya da rayuwar sa bada shi ake ba, arashi ne kawai*
*GARGADI*
*Ban yarda a canja mini labarina ba, haka ban yarda a sarrafa mini littafi ta hanyar karanta shi a kowacce kafar sadarwa ba tare da izinina ba, duk wadda ya yi hakan na bar shi da ubangijin da ya hana zalinci*.
*SADAUKARWA LITTAFIN GABA'DAYA GA IYAYENA GUDA HUDU*
ALH MUHD TUKUR
HAJ FATIMA LADI ALI.
ALH DAHIRU ALI
HAJ MARYAM HAMISU KANO.
INA FATAN ALJANNAH MAKOMA A GAREKU, UBANGIJI YA JIQAN KU, YA SHIRYYA MUKU ZURI'A, DÀ DUKKAN IYAYENA DA ALUMMAR MUSULMAI.
*TUKUICIN KAUNA GA MIJINA*
*ALH MUKHTAR NASHE*.
FATAN ALHERI GA SHUGABAN KUNGIYAR LAFAZEE ONLINE WRITERS.
SADIQ ABUBAKAR.
GAISUWAR GIRMA GA HAJ RABI SANI MADAKIN GINI.
HAJ SALIHA A A ZARIA.
Bisa taimakon ku da addu'oinku gareni Ubangiji ya
Mugun fatan da Sa'a ta masa na ba zai gama da Hajiya lafiya ba, ya Fado masa, ya hassalo sosai.
Cike da ladabi ya ce "Ciwonta ba matsala ba ce ina sonta a haka, zan kuma kula da ita da iyakacin iyawata".
Da'di ya cika zuciyar Alhaji ya ce "Ubangiji ya maka albarka, ya rufa maka asiri duniya da lahira, Allah ya zaunar da ku lafiya"
"Iyayenta mata suna son zuwa yin jere na dakatar da su, akan sai mun tattauna, nasan baka shirya komai na auren ba, dan haka na gyara maka wani karamin gidana da ke LAMIDO crescent"
Ya ajiye mukulli tare da takardun gidan kusa da Mk.
A nutse Mk ya ce " Na gode sosai Alhaji amma ba zan karba ba, domin zan dinga jin tamkar Ina gidan mace ne, ina fatan kalamina ba zai zama laifi ba".
Sosai Alh Nasir ke nazarin Mk, yana jinjina masa, domin samun irin su da zuciyar su bata zarme ba, zai yi wahalar gaske, saboda yau muna cikin wani irin zamani da ake auren jari.
Da murmushi a fuskarsa ya ce "Mukhtar ina da tabbacin ko a gaban Farida na baka wannan gidan ba zai zame maka na'kasu ba, ba a shaidar 'dan Yau amma na shaidi Farida. Balle ma ni a satin nan na siye shi, ba kuma wadda yasan na siya, da sunanka na siye shi, Dan haka mallaka maka na yi ba aro ba".
"Na gode sosai, Allah ya kara arziki, amma ba zan karba ba, abawa masu son zuwa jere ha'kuri, ba zata tare ba, zamu tafi Uk ne, idan ubangiji ya kaddara mun dawo lafiya, Ina da 'karamin gida a gadon kaya sai ayi komai".
Ganin da mahaifin Farida ya yi da gaske Mk yake yi ba zai karba ba, sai ya bar maganar gida yana 'kudire dole ya masa wani abu na alheri komin dadewa.
Ya ce "idan nace ina son na dauki nauyin tafiyar iyalin naka fa, ko shima baka so?"
Kunya ta kama Mk ya sake yin kasa da kansa domin ya gaji da yin musu ya ce "Na gode sosai, Allah ya kara arziki".
Alh Nasir ya mike yana ta musu addu'a da fatan alheri, tare da cewa "Bari na turo maka ita".
Ba a dauki lokaci ba, ta iso cikin tsadaddiyar abaya baka sai walainiya take yi daga hannun rigar an masa ado da shudin duwatsu, dan haka ta yi anfani da shudin mayafi a maimakon na abayar, ba kwalliya a fuskarta tunda ita ba ma'abociyar adon fuska bace, kawai powder ta shafa sai wet lips sai tsadadden turaren ta na amour amour.
Soasai ta masa yi kyau, sai ya dinga tuno sadda yake zuwa zance wurin Iyah yana ce mata ta yi kyau tamkar balabiyar Habasha.
Ya zuba mata idon da suka yi jah tamkar mai fama da ciwon afolo, alhalin bacin ran da Sa'a ta jefa shi ne yake neman kassara shi.
A hankali cikin sanyin muryar ta gaishe shi ya amsa da karsashi.
Ya zuba mata ido sosai, kanta a kasa tana jin yadda kallon ke ratsata.
A hankali ya ce "ya jikin ki? Ko da yake kin warware, irin wannan kyau da kika 'kara yi tamkar balabiyar Yemen"
Kanta na 'kasan ta murmusa tana jin kunyar sa sosai.
Ya dinga janta da hira, har ta dan sake da shi.
"Na fadawa Dadi ba zaki tare ba, Ni Kinga nan da kwanaki biyar zan wuce, ke kuma da zarar visar ki ta fito, sai ki bini, abar maganar jere tukun yanzu".
"Allah ya nuna mana"
Ta fada a hankali.
Suka yi shiru. Na dan gajeran lokaci, Farida ce ta katse shirun ta hanyar cewa "Dadi ya baka aure ba tare da ka ce kana so ba anya ba'a takura ka ba?".
Tausayinta ya sake shiga jikinsa sosai! a hankali ya kira sunanta ta dago suka zubawa juna ido tsawon sakwanni, Farida ce ta yi karfin halin janye idanuwan ta saboda yadda take jin sonsa na sake dafa duk ilahirin jikinta, yadda idanuwansa suke a jirkice da kuma yadda suka yi ja sun sake jefata cikin matsanancin so.
Murya ba amo sosai ya ce "Na yi mamakin da kika yi tunanin aurenki zai zamo mini takura!
Tun yaushe muke soyayya da zaki ce na takura?"
Ta sunkuyar da kai kasa ta ce "kafin shigowar Gogel cikin rayuwar ka nasan muna soyayya, amma bayan ta shigo sai ta kashe tawa soyayyar".
Ta fa'da cike da rauni sosai.
Idan gaskiya zai fa'da yasan ba 'karya ta yi ba, amma dan ya faranta mata sai ya ce "Ba mutuwa ta yi ba dogon suma kawai ta yi, saboda ina ganin bani da halin da zan zo neman aure wannan gidan, Amma da yake ubangiji yasan yadda na ke sonki sai ya 'kaddara mini samun ki a lokacin da na cire rai, idan kinsan farin-cikin da nake ciki da baki yi wannan tunanin ba".
Ya nisa ya ce "tunda da bakinki kika sako maganar Sa'adah bari na fa'da miki wani Abu, kin san yanzu bama tare, amma idan ubangiji bai karar da zaman mu ba, zan dawo da ita, kar hakan ta faru a gaba ki ji a ranki kin gaza ne, sosai nake sonki Farida, sannan ba zan boye miki ba itama ina sonta, kaddara ce ta rabamu, Ina fatan wannan ya zama na karshe da za ki sako mini maganarta mussaman akan ina sonta ko saboda ita na rabu da ke a farko, an 'kadddara mini sai na fara aurenta ne kawai".
Sosai ta fahimice shi ta kuma gasgata shi, duk da ta ji fargabar da ya ce zai dawo da ita, ba dan ba ta so ba, sai dan kishin da kowacce mace ke da shi akan abin da take so, dan ma ta yi sa'ar na ta kishin mai sauki ne saosai.
Ta katse maganar da cewa
"Ya Hajiya da Jawad?"
Ya amsa mata suna lafiya.
Ta sake fa'din"kun je anyi masa passport din?"
"Anyi masa sai dai da alamu visar ki zata riga tasa samuwa, kawai idan ta ki ta zaama ready, zaki taho ne, shikuma Mahmoud zai taho da shi nan da wattanni uku".
Yana rufewa ta ce "wallahi ba zan iya ba, kafata, kafarsa, sai dai nima na jira shi, ka riga kasa masa rai, sai kuma ya ga shiru, Ni bama zan iya zama da kai babu shi a tsakanin mu ba, ni ka'dai nasan yadda nake jin yaron nan a zuciyata".
Dadin kalaman ta suka kama Mk ya ce "wato saboda Jawad sai ki barni ni ka'dai, baki damu da halin da zan shiga adalilin rashin ki kusa ba?"
"To idan hakane sai ka yi kokari mu samu visa tare da shi".
Sosai suka sha hira mai cike da 'doki.
A ranar ta nuna masa yatsun kafarta guda biyu da suke a tankware , dan kar sai daga baya ya gano ya ji an yaudare shi, sosai ya sake jin tausayin ta, bai san me yasa yake jin tausayin ta ba tun fil'azal, ya yi ammana wannan tausayin ba zai barshi ya zalunce ta ba.
Har wajen harabar Adana motoci ta rako shi, anan ma sun sake bata lokaci suna hira.
Sai da ya koma gida ya kwanta tunanin ciwon Farida ya zo masa menene (Arthritis?).
Da tunanin ciwon barci ya yi awon gaba da shi, yana karyawa kuwa bai zame ko ina ba sai asibitin kwararru na Murtala, ya samu Dr Babangida Bojuwa abokin kaninsa ne Akil, suka gaisa sannan ya nemi alfarmar ya masa bayanin menene ainihin ciwon Arthritics da hanyar da za'a bi a kula da mai fama da wannan ciwon.
Dr Bojuwa ya yi murmushi sannan ya cire gilashin idonsa wadda yake taimaka masa wurin gani sosai sabanin da mutane suke kallon tamkar na ado ne.