← Book details Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 33

Sashe 9

Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muna komawa anti Yagana ko ta bari mu huta ta fara surutai. " Idan Babandi ya zugaki kike kashe auranki Amina bai wuce shi din ya aureki ba tunda na gane dama tuntuni yana sonki bai fad'a ba ne sai yanzu, to me na sama ya ci balle ya bawa na k'asa. A yadda kike Amina ai sai irin su Alhajin Tajon din, shi din ma sai dai Allah ya k'wace shi, amma muddin Babandi ya aureki sai ya gane shayi ruwa ne shege yana yawo da bakar fuska.
Duk da kuncin da nake cikin sai da na yi dariya na ce." Anti Yagana ina da wani mugun hali ne da za ki ce haka, ni fa abinda kike zargi ba shi ba ne, kin san dai Babandi mutumina ne ko?"
Ta share ni ba ta ce mini komai ba, amma motsi kad'an za ta yi kwafa ta girgiza kanta tabbacin abin yana damunta. Sai ta ba ni tausayi domin na gama fahimtarta ita dai kokarinta ta danne ni na zauna saboda kada duniya ta zage ni, a kuma yi mini lissafin aure shine kawai abinda take gudu.
Da daddare misalin goma da wani abu ya kira ni a waya. Dama tunda na sauka a garin sau d'aya mukayi waya kuma shi ya kira ni. Ina sane na ki d'agawa har sai da ta katse ya sake kira ta katse a k'alla sai da ya kira sau hud'u na daga ina sallama.
Ya ce." Wanene Babandi?"
Gabana ya buga da karfin gaske! jin sunan Babandi a bakinsa. Da kyar na daure na ce." 'Dan uwana ne."
"Shine kuka 'keba a wajan da babu gilmawar mutane? idan dan'uwanki ne me zai sanya ba za ku tsaya a bainar jama'a ba."
Na daidaita nutsuwa sosai domin yin hakan shi kadai zai kwace ni daga mummunar zarginsa. Shin a ina ma ya san na yi hira da Babandi.

"Anan din ma sai ka tuhume ni akan abinda baka da hujja wai dan girman Allah a gidan karuwai ka auro ni Baba, ko kuma dai ka fara tu'ammalli da muggan kwayoyi da suke fad'a maka karya."

"Kina mamaki ne don na tuhume ki, ki ba ni amsar tambayata kawai idan har Babandi dan'uwanki ne na jini me zai sanya ki 'kebe dashi shi kadai."

"Saboda akwai muhimiyar maganar da muka tattauna, Babandi Kuma d'an'uwana ne na jini tunda iyayenmu cikinsu d'aya, kuma tun kafin na sanka nake tare dashi wannan shine bayanin kawai da zan iya yi maka a kansa."

Kashe wayarsa ya yi ba tare da ya sake yin wata magana ba. Jikina a mace na ajiye tawa wayar ina tunanin yadda aka yi ya san na ke'be da Babandi. Sukairaju anan gidan anti Yagana na bar shi. Na san kuma ko giyar wake anti Yagana tasha ba zata gaya masa ba tunda ita kokarinta ma na koma gidana na cigaba da zama.
Yusi ya shigo d'akin da nake da yaran 'yan uwa dana anti Yagana na ce su je waje domin lokacin k'wa'kwalwata tana buk'atar hutu.
Suka juya zasu fita na kira shi ya dawo shi kadai na ce." Kun yi waya da Baba ne a wayar Sukairaju?"
Da sauri ya ce." Eh d'azu da na zo kawo masa abinci na same shi suna waya shine na ce ya ba ni shi mu gaisa."
Gabana na dan bugawa ba ce." Kai ne kenan ka ce masa ka gan ni tare da Babandi ko?"
Ya gyada kansa yana cewa." E tambayata ya yi kina Ina shine na gaya masa kina can tare da Babandi a storoom."
Na zuba masa ido ina ji kamar na gaggaura masa mari saboda takaici!
Ganin irin kallon da nake yi masa ne ya sanya jikinsa mutuwa sai ya sunkuyar da kansa da kyar na ce.'' Jeka ku kwanta dare ya yi."Ya kama hanya ya fita ba karsashi.
Cikin baccin da ya fara fizgata na ji tana kirana na tashi zaune da sauri Ina kallonta
Tana cikin kayan bacci don wata'kila ma daga turakar mijinta take ta kufto ta fito saboda rashin ha'kuri ganinta a hargitse ya tabbatar mini da cewa ta san abinda ya faru wata'kila ma shi ya kira ta ya gaya mata.

"Kina ganin abinda kuka yanke da Babandi shine mafita a rayuwarki Amina."
Na dube ta a tsanake na ce.'" Anti Yagana me muka yanke ban fahimci inda maganarki ta dosa ba."
Ta gyada kanta cikin takaici da jin haushi ta furta." Yanzu Amina a ce kamar Babandi shi ki ka bawa lasisi da ragamar auranki saboda kin zama mara mafadi babu wanda ya isa ya gaya miki ki ji, a ce wai Babandi shine zai tsara miki yadda za ki yi, Kuma ki bashi kwarin guiwa da hadin kai ya kira mijinki mutum kamar wannan da yake da kima da dattako da shekaru ya gaya masa maganganu masu kaushi, ashe Amina ni ban isa na gaya miki magana ba ko?"
Sai kawai naga kwalla ta ciko a kwarmin idonta.
Hankalina ya tashi sosai na ce." Wallahi tallahi anti Yagana ban yi haka da Babandi ba, ya takura mini da tambaya ne shine na dan tsakura masa abinda yake damuna, kuma na gargadeshi akan kada ya gayawa kowa, ban taba tsammanin ma zai iya kiransa da wata magana ba, a Ina ma ya samu lambarsa mutumin da ba kowa ya san lambarsa ba.
Hawaye suka keto kumatunta suka fara d'iga.
Sai na ji duk gwiwata ta sanyi me ya yi zafi Anti Yagana take kuka irin haka.
Hawaye suka silalo mini na ri'ke hannunta ina fad'in." Wallahi tallahi anti Yagana ban sa shi ba, ban san a inda ya samu lambar wayarsa ba, ki gaya mini abinda ya fad'a masa domin tunda naga kina kuka na san abin babba ne."

Ta goge hawayen tana cewa." Ni babbar damuwata shine duk rintsi duk wahala ki yi hakuri ki zauna a dakinki Amina, ba wai na kafe akan don mutumin nan yana da wata suttura ba a a ke nake dubawa da kuma yaranki, matsalarsa ba mai muni ba ce a ganina tsananin so ne yake janyo kishi shi kuma na fahimci duk lokacin da zai tuna maza biyu sun taba ki kafin shi yakan kasa sarrafa kansa. Kishin maza fa daban yake dana mata wallahi maza sun fi mata kishi, mu hauka muka fi su. Kada wani ya rudaki akan ki fito ki yi hakuri ki zauna domin Babandi ba zai ta'ba iyawa da bukatunki da na yaranki ba. Karshe dai ki kara famtsama harkokin da ki ka bari a baya."
Ina kuka na ce." Na ji batunki anti Yagana Kuma na fahimci duk abinda kike nufi, ni kaina ba na so ace na fito daga d'akina, amma abinda nake so ki fahimta shine, bayan wannan matsalarfa akwai wata a kwance nasan baki manta da cewa samun haihuwa zai yi mana mutukar wahala a tsakaninmu ba duba da sakamakon gwaji da abinda ya faru a baya na rasuwar abinda muka haifa.
Akan iya samun matsalar haihuwar yara marasa lafiya tunda har jini ya nuna anti Yagana kuma kinga ni duka yarana biyu a duniya, shi kuma a yanzu ne yake da buk'atar tara zuria. Haihuwa da wahala tun daga samuwar cikin raino da nakud'a. Ba fata nake yi ba duk na gama shan wannan wahalar Kuma na zo na haifi da mai lalura daga karshe ya mutu, anti Yagana akwai ciwo da damuwa wata ta zo daga bayanka kana kallo ta yi ta haihuwa kai kana zaune."

Ta girgiza kanta cikin damuwa ta furta." Na gaya miki tun farkon lamarin nan ki k'adaita Allah, domin su kansu turawan da suka kirkiro abin nan hasashe kawai suke yi, babu fa wani mahaluki da ya isa ya canzawa Allah manufa duk abinda ya wanzar shine daidai. Ki saki zuciyarki ki zauna a dakinki, idan za ki haifi yara goma su mutu dama haka Allah ya nufa, idan kuma zaki haifi yara goma su rayu haka Allah ya nufa. Ai Kinga da za ki auri Aminu ba a yi gwaji ba, kuma gashi kin haifi yara masu lafiya kwarai da gaske, to wannan ma kadai ya isa ki barwa Allah abinda ya tsara miki"
[8/24, 9:26 AM] Aunty B: 67
Ni kukan da take yi shi ya fi daga mini hankali domin na jima ban ganta cikin yanayi na damuwa da tashin hankali ba, kukanta yana da ala'ka da abu biyu domin yau yini aka yi a gidan bikin nan ana hirar Mamanmu har wasu daga cikin 'yan uwanta suka dinga kuka, a ganina matsalata kadai ba za ta sanyata zubar da hawaye irin haka ba, tashin zancen Mamanmu da 'yan uwanta suka yi shi ya kara dagula mata lissafi sai ni ce na yi namijin ko'karin tsayar da nawa hawayen na dinga rarrashinta akan ta yi shiru ban samu hakan ba kuwa sai da na yi mata al'kawarin duk rintsi da wahala zan ha'kura na zauna a d'akin mijina
Da wannan alkawarin ta tashi ta fita ta barni cikin tunani da zullumi. Ni dai nasan anti Yagana ba makwadaiciya ba ce balle na ce mutumin nan siyanta ya yi da kudi. Na fi zargin dai abin a jininsa yake domin na fahimta duk wanda zai yi mu'amula dashi da wahala ya hangi kuskuransa. Ni a karan kaina na san shi din mutum ne domin kuwa duk inda ake neman dattako da nagarta taimako da tausayi ya kai a jinjina masa. Amma a dabi'a da halayya irin ta dan adam dole a same shi da wani nakasu wanda sai mu da muke zaune dashi za mu tabbatar.
Baya ga mummunan zarginsa babu komai a tsakanina dashi face alheri domin har yau har gobe ina kallonsa da hakan, amma ina ji a cikin raina zamanmu ba zai yi dad'i irin yadda anti Yagana take so ba muddin bai canza dabi'a ba, ni kaina ba wai so nake a ce mun rabu ba domin duk abinda take yi mini hange ni ma ina yin hagen haka, to amma ai zaman ba zai yi tasiri ba idan da cin zarafi a ciki.
Chapter 9 · 0% Book details