Sashe 10
Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Kamar yadda ta ce mini na kira shi na bashi ha'kuri bayan wanda ta bashi ban ce to dan na yaudareta ba na yi aniyar kiran nasa sai dai fargabata ban san irin martanin da zai mayar mini ba tunda na gama fahimtarsa bai iya b'acin rai ba.
Sha biyu da wani abu idona biyu na kasa rintsawa saboda fargaba da tunanin d'anyan kan da Babandi ya yi mini, kawai don ina jin nauyinsa ne ya sanya ni dannewa amma tabbas da wani ne ba zamu wanye lafiya ba. Wayata na d'auka wadda har na kashe na ajiye zuciyata ta kasa nutsuwar barin gari ya waye na kira shi, na san yanzu da wahala idan ya kwanta ya kan kai karfe daya yana aiki da computer kafin ya kwanta.
Da fargaba na lalubi lambarsa na kira hannuna na dan karkarwa karon farko kenan da nake jin fargaba da tashin hankalin wani raddi daga wajansa.
Sai dai kuma daga zarar wayar ta fara shiga sai ta katse. Na tashi na fita falo wai ko network ne nan ma ta dinga yankewa, ni ce dai har farfajiyar gidan amma ta'ki tafiya.
Babu kuzari na koma daki na zauna da wayar a hannuna na rasa wane nazari zan yi. Kai tsaye dai ba zan yanke masa hukunci ba, amma ai ban ta'ba kiran layinsa ya yi mini haka ba.
Ban ha'kura ba na jarraba kiran Sahura sai gashi ta shiga har ta fara ringing na katse da sauri na sake nemo lambartasa a karon da babu adadi ta sake katsewa. A lokacin na gazgata hasashena a busy ya sanya ni. Bai d'auki waya ba na san ko text na tura masa ba zai duba ba tunda dama can ya kan tara messages na mutane kafin ya samu damar dubawa.
Na kwanta cikin zullumi da tunani lallai akwai maganganun da Babandi ya gaya masa dama ai mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awakai yanzu shawo kansa sai na kusa zama k'aramar mahaukaciya.
Ban ta'ba kawowa zuciyata saki a cikin irin hukuncin da yake ganin zai yi mini ba, domin ni kallon da nake yi masa ma kome zan yi masa na takaici ba zai d'auki matakin sakina ba sai gashi na wayi gari da ganin text dinsa na saki d'aya Inda ya rubuta a takaice da kuma babban hafarai "NI ALHAJI TAJUDDEN IBRAHIMU NA SAKI MATATA AMINA SALISU SAKI DAYA." Na yi bala'in kad'uwa daganin sakon gabana ya dinga bugawa da mugun karfi yayin da wani irin yawu ya tsinke mini a bakina.
Da kyar bakina ya kar'bi abinda zuciyata take amayowa na dinga nanata Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
Zuciyata na harbawa da mugun karfi. To da yake babu abinda ya fi ambaton Allah samun sasaauci a lokacin dadi da b'akinciki, cikin kan'kani lokaci na dan shiga nutsuwata na fara tunanin yadda zan yi na shawo kansa ya mayar da ni ba tare da kowa ya ji ba.
Babbar damuwata Anti Yagana da alkawarin da na yi mata jiya kafin ta je ta kwanta, amma ni idan ta ni ce zan iya jurewa tunda ba shine karo na farko ba. Har yanzu zuciyata ta'ki aminta da cewar da sanin mahaifiyarsa ya sake ni. Ya yi mini hakan ne saboda ya nuna mini ni din ba komai ba ce. Kishi ba hauka ba ne yana da kyau ya ji ta bakina kafin ya d'auki d'amarar tozartani.
Hawaye masu zafi suka kece mini suka fara kasa tsere a dakalin fuskata.
Na yi kasa'ke da waya a hannuna gwiwata ta sage tamkar an buga mini guduma, komai ya dagule mini na rasa ma abinda zan yi.
Shi din zan nema domin na ji ba'asi akan abinda ya yi mini, har yanzu ban yarda da cewa abinda na aikata na cancanci hukuncin saki ba, ai ba rufe kofa na yi da Babandi ba, sannan kuma duk abinda zuciyarsa zata kitsa masa a kaina bai gani da idonsa ba, ni ba mazinaciya ba ce, idan ma yana hasashen hakan a kaina.
Na kira shi ya fi sau goma sha biyu bata shiga. Hawayen nadama da tausayin kaina suka dinga gudana a kumatuna. Ba zan kira mahaifiyarsa na na gaya mata ba, domin na tabbatar da cewa ba ta san abinda ya faru ba domin da yawunta ba zata bashi goyan bayan yi mini wannan tozarcin ba. Sannan bata da koshin lafiya Ina ganin jin wannan labarin zai iya daga mata hankali har ciwonta ya tashi.
Garin Allah ya waye sosai haske ya fito ban fita ba asalima ban tashi daga kan daddumar da na yi sallar asubahi ba. A hakan anti Yagana ta shigo ta same ni ganina a rikice ya sanya ta zo ta tsaya a kaina tana tambayata.
Koda na dubeta sai wani sabon hawayen ya k'wace mini. Na d'auki wayata dake ajiye a gefe na mik'a mata.
Tana dubawa tana salati sai ta silale rigijib ta zauna a gefena. Na rufe fuskata da hannuna ina kuka na furta." Anti Yagana ko me na yi wa mutumin nan ban cancanci wannan cin zarafin ba. Wallahi tallahi ba da hannuna Babandi ya kira shi ba, kuma dana san abinda zai faru kenan dashi kansa Babandi ban gaya masa komai ba. Anti Yagana ki duba lamarin nan a tsanake akwai izza da iko da nuna kowa ba komai ba ne a cikin sha'anin wannan mutumin ya iya taku ne shiyasa ba kowane zai fahimci hakan ba, amma menene lefi don an ce gyara kayanka, abinda fa yake aikata mini kuskure ne, na tabbata ko giyar wake Babandi yasha ba zai zage shi ba karshen dai rashin kunya kenan, magana ce ake yi akan dabi'ar da yake yi ba mai kyau ba ce, kuma duk wanda ya san ciwon kansa ya kuma san illar zargi a sha'ani na aure ya san hakan ba daidai ba ne, menene abin saki a nan anti Yagana don yana da wata alfarma wallahi ba zan bari ya wulakanta ni ba."
Anti Yagana ta ja hanci idonta da sauran hawayen da ta gama gogewa ta ce.''Wallahi tallahi sai da na ji haka a jikina Amina, shiyasa fa jiya kafin na fita na umarceki da ki kira shi ki bashi ha'kuri Kuma ki shanye duk b'acin ran da zai k'unsha miki, dan kyautawa ke da Babandi baku kyauta ba, kuma tun a jiyan na kira Babandi na tambayashi yadda suka yi dashi ya ce ya yi masa magana ne akan abinda ki ka fad'a masa har ya kara da cewa dashi bai auro ki a gidan karuwai balle ya yi togaciya da kiranki da wata kalma ya kara da ce masa harkar social media da ki ka yi kin yi ne domin rufawa kanki asiri da yaranki, ni dai iyakacin abinda ya fad'a mini kenan ban sani ba ko ya rufe wata maganar wadda ya gaya masa ta fusata shi ni bai gaya mini ba.
Kuma ko jiyan da muka yi waya dashi wallahi ha'kuri na bashi akan hakan kuma ya nuna mini ya ha'kura magana ta wuce amma hukuncin da ya yanke ya yi tsauri bai kai ga a ce an yi saki ba.
Na ce." Anti Yagana ki kyale shi kawai dan Allah dan annabi kada ki kira shi akan neman hujjar da ya sake ni. Na san bashi da ita zai bata miki lokaci ne kawai hujja dai ita shi mai kudi ne, kuma ni ba kowa ba ce a wajansa a yanzu."