Sashe 24
Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read
d'ume da mashahurin zafi. Babban bargon da yake shimfid'e akan katifata na d'auko da matashin kai biyu na gyara mana shimfidar sosai sannan na tasheta ta je ta yi fitsari ta dawo ta kwanta . Yadda hadari ya had'o sosai na gabas da irin walkiyar da ake yi da wahala idan ba a yi ruwa ba domin hadarin gabas ba kokwanto yana zubar da ruwa. Na fita na gyara abinda zan gyara na leka shagon lokacin suna ta shirye shiryen tashi dan ma da yawa daga cikinsu gidajen iyayensu a unguwar suke wasu kuma a shagon suke kwana. Kofar ciki na rufe sannan na rufe ta falon na nemi waje na kwanta lokacin ruwan ya fara sauka kad'an kad'an. Sai Kuma na ji ana ta'ba kofar na tashi zaune da mamaki. Kira ya shigo wayata da take ajiye a gefena don ban kai ga kasheta ba tukkuna. Hamusu ne ya kira Cike da mamaki na daga wayar na ji shi yana fad'in." Anti har kin rufe gidan kenan Yallabai na yi wa jagora muna tare ki bud'e kofar.'' Da fargaba mai yawa a tare da ni na ce." Yallabai kuma?" Da sauri ya furta." Eh anti ki yi hanzarin bude kofar ruwan ya fara karfi." Na yun'kura na tashi tsaye gabana na dan bugawa na dubi lokaci a wayata goma da minti arba'in, ban san me ya kawo mutumin nan wajena ba a irin wannan lokacin ko zuciyarsa ce ta raya masa ya yi mini zuwan bazata domin ya kurewa 'karyata ko ya tsira ni. Idan na'ki bude kofar nan na d'auri kaina hasashensa zai tabbatar a kaina wannan dalilin ya sanya na fita cikin ruwan da ya fara karfi na bude kofar. Sune tsaye shi da Hamusu biyu kacal bai zo da kowa ba. Ruwan har ya fara jikasu. Hamusu ganin na bud'e kofar bai ce mini komai ba da sauri ya shige shago suka rufo kofa. Jikina babu kuzari na matsa masa hanya ya shiga na tsaya na rufe kofar kafin na biyo bayansa. A rumfa na iske shi yana bin wurin da kallo. Na tsaya kawai ina kallonsa jikinsa na dan d'igar da ruwa rigar jikinsa duk ta kwanta sakamakon ruwan da ya ta'ba shi. "Kin yi mamaki ko?" Maganar da ta fara fitowa daga bakinsa kenan. Na ce." Ban yi mamaki ba, ai hakan yana daya daga cikin halinka dana sani." "Wannan yarinyar fa?" Yafad'a yana duban wurin da Yusura take kwance. Na kalleta baccinta take yi sosai na ce." Yarinyar Sahura ce." Ya gyada kansa kafin ya furta." Ni a Ina za ki sauke ni, annabi ya ce ka girmama bakonka." "Ai ba ka gaya mini za ka zo ba, za ka iya zuwa shago ka kwana da yarana domin nan ne masaukin baki a gidana." Ya tsaya kawai yana kallona kafin ya yi dariya wadda har sautinta ya fita ya ce." Idan za su yarda na kwanta a cikinsu ni a wurina ba komai ba ne." Shiru na yi ban tanka masa ba. Sai ya dubi jikinsa da yake d'igar ruwa ya kalleni." Mu je d'akin naki, ki ba ni aron zani na d'aura." Na ce." Ai ban zo da wasu kaya da yawa ba gaskiya ba ni da zani sai siket." "Zan sanya siket din, ke da ki ke lukuta ma ki ka sanya balle ni." Ganin Yusura na motsi ya sanya da sauri na nufi dakin ya biyo bayana. Da sauri na tayar da katifar da take kwance na tsayar da ita sai kafet kawai a wurin. Muka yi cirko-cirko muna duban junanku kamar shekararrun zakarun da suke matsananciyar gaba da junansu." "Ba za ki girmama ni kamar yadda Annabi ya fad'a ba kenan." Ya fadi hakan kafatanin hankalinsa a kaina. Na ce." Ai ba ka kira ni ka sanar da ni zuwanka ba ballantana na baka masauki." "To ke din a karkashin wa ki ke, ko ni kin gaya mini za ki zo nan?" Shiru na yi ban tanka masa ba sai ya tunkaro wurin da nake tsaye ban ja da baya ba amma Ina cikin matsananciyar fargaba. Gabad'aya ya danneni da kirjinsa har sai da na fadi a kasan wajan. Ya tsuguna yana fad'in." Ki ba ni abinda zan sakaye jikina na cire wannan jikakkun idan na kwanta ciwo kuma ke ce sanadi domin zan iya rantse miki na fi karfin shekara talatin rabon da ruwan sama ya dake ni." Muryata na d'an rawa na ce." Wannan kuma abinda ya shafeka ne. Sai ya tsirawa fuskata ido yana kallo, na kawar da kaina domin yanayin kallon da yake yi mini ya fara sa'bata. Yun'kurin tashi na fara yi ya mayar da ni ya zaunar ." Ban zo gidanki domin ki wulakanta ni ba da zummar sasanci na zo, na yarda na yi lefi ki yi hakuri." Har cikin zuciyata na ji dad'in karayarsa wanda da wahala a irin wannan zamani namiji karabiti ya yi wa mace lefi ya bata ha'kuri ballantana irin nawa mijin. Àmma ban nuna masa hucewata ba, na sake daure fuska tamau na furta." Amma kasan abinda ka ke yi mini kuskure ne?" "Na sani, dalilin da ya sanya ma kenan na ji zan iya jure duk wani cin kashi da za ki yi mini, kuma ba na so kowa ya ji na sake ki, mussaman Hajja." "Ai na gaya maka tun farko yadda ita ta kulla auran yana da kyau da ta san abinda yake faruwa, ni a wurina babu lefi don ta ji cewa igiya daya ta samu tangard'a." "Ban amince ba, ba zai yiwu hakurin dana baki ya tafi a banza ba, na gaya mini wannan lamari ya zama sirri a tsakaninmu na yi miki alkawarin in sha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba." Na yi shiru ban ce komai ba. Sai ya riko hannuna a hankali." Kin yi alkawari ko?" Kai na girgiza na ce." Ni fa mutum ce mai zuciya ya ba zan ji zafi da takaici ba a duk lokacin da wanda nake aure ya gaza fahimtata. Saboda kawai bai samu budurcina ba, ya aureni ina sana'a domin rufawa kaina asiri sai kawai saboda son zuciya da rashin adalci ya dinga yi mini mummunan kazafi."