← Book details Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 33

Sashe 33

Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

To har na gama aikin zuciyata ba ta daina tsalle ba. Nasan idan na tunkare shi da maganar tutsiyar da ya yi wa Hamusu cibi ne zai zama 'kari dama mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki sai kawai na share shi ban nuna masa cewa nasan abinda ya yi ba.
Sai da na hada masa komai tukkuna na sauko daga saman na samu Yusura ta yi wanka ta shirya tsaf na ce taje ta d'ebi abinci wanka zan yi tukkuna.
Na shirya cikin doguwar riga ta atamfa duka kala shida na zo dasu hud'u sun yi datti saura biyu kacal itama Yusuran nata sun yi datti na ce da safe sai ta wanke mana tunda akwai na'uwarar wanki a gidan.
Sai komawa na yi saman a karon da ba zai lissafu ban ji matsalar hawa tunda kamar ina motsa jikina ne shiyasa hakan baya damuna.
Na sake samunsa yana waya amma cikin fushi da kuma kausasan maganganu da harshen nasara ya canza harshe sosai na yi tsam Ina kallonsa gabad'aya baya hayyacinsa gumi sai yanko masa yake yi na b'acin rai da kuma saukar zazzabin da yake damunsa
Fankar da ya umarceni da na kashe a d'azu da safe ita na kunna masa domin ita kanta rigar da take jikinsa daga baya ta jike da gumi.
Turanci yake yi tsantsa har yana hadawa da yaran chanis wanda ban ta'ba jinsa a bakinsa ba ashe komai dalili yake yi. Na d'an fahimci wasu abubuwan amma kasancewar ban ji farkon maganar sai na gaza fahimtar mai yake faruwa. Ba wai dukiyar ba irin wannan kalubalen da farautar rayuwar mutum shine abin damuwa.
Ya kai karshen maganar da bada umarni a rufe kamfanin gabad'aya na fi tsammanin wata matsalar ce kuma take shirin kutso masa bayan ga wata ba a kashe ba. Wannan kadai sun isa su hargitsa masa lissafi..
Ya kira Sukairaju a waya minti biyar ya shigo ya ce masa maza ya je Danbatta gidan Hajja ya debo masa kayansa na sanyawa da ya zo da su da laptop d'insa ya bashi key din d'akin.
Bayan fitarsa ya dube ni Yana fad'in." Ki sama mini ruwa na yi wanka na samu sau'ki."
Na ce." Ai wanka ba naka ba ne yanzu koda kuwa da ruwan d'umi ne saboda kada kuma zazzabin ya dawo."
Cike da tsawa ya furta." Sai na yi ta zama cikin zuffa ina tsami kenan malama ki yi abinda na ce ko na tashi na yi da kaina, ai Allah Ya hore mini hannu."
Tashi na yi na sauka kasa ina mamakin abin daga shawara sai masifa da bakar magana.
Sai dana sauka kasan sannan na tuna akwai bandaki a cikin d'akin da yake na sake komawa sai na same shi a toilet din yana kwance shaya wadda ni a tunanina ma kwata kwata bata aiki sai naga ruwa ya kashe ya fara ko'karin cire rigar jikinsa. Shiga na yi bandakin na bude shayar ruwan da yake zuba bai cika sanyi ba da yawa zai yi daidai wanka a yanayin tunda ba zafi ake yi ka'in da na'in ba kuma ba sanyi ake yi ba.
Ban ce masa komai ba na fice daga bandakin domin zuciyata ta fara yin zafi akan abinda yake yi mini duk kuwa da ko'karin da nake yi akansa
Ban sake hawa saman ba domin ina ganin yin nesa dashi din zai fi mini kwanciyar hankali muddin bashi ya neme ni ba.
Yusura tana falo a kwance cikin kujera tana kallo a wayata ashe finafinan da Yusi ya uzzura a tura a wayar za su yi rana.
Na kar'bi wayar domin Ina son kiran anti Yagana dalilin damuwar da take damuna. Komai na tibin dake falon a hade yake sai na kunna mata tunda na lura ma'abociyar son finafinan indiyace na kamo mata tashar da suke yin fassarar hausa. Ta kuwa gyara zamanta sai kace mai d'aukar darashi.
Cike da mamaki da zullumi anti Yagana ta furta." Hamusu ba zai aikata wannan d'anyan aikin ba Amina, a dai kara bincike da kyau a jikina nake jin hakan akwai dai makarkashiya amma ki bi komai sannu a hankali kuma don Allah ki dinga tausar zuciyarki akan mutumin nan ki yi duba da yanayinsa da al'amuransa na yau da gobe wasu abubuwan dole a yi masa uzuri ki bari ya samu nutsuwa ta bangaranki koda ya yi miki abinda ranki bai so ba ki tuna alherinsa ki yafe masa, ki yi kokarin ri'ke auranki domin a yanzu dai samun makamancinsa zai yi wahala Amina kuma mazan duk haka suke wallahi kwaryaar sama ce take dukan ta kasa kusan duk haka halinsu yake."
Maganganun anti Yagana sun sanya mini kwarin zuciya na aminta cewa babu wata nasara a rayuwa face ba a ci karo da kalubale ba. Sannan kuma babu yadda za a yi a ce zaman aure ba a samu wata tangard'a ba.
Wannan dalilin ne ma ya sanya ban turje masa ba da ya nemi inda nake hakan da na yi sai ya siya mini mutunci tun bayan tsawar da ya yi mini dazu akan maganar wanka ban sake nemansa ba wata'kila ganin haka ya sanya ya gane rashin kyautuwar abinda ya yi. Ai kowa rai ya yi wa dadi barin me shine iyakacin bakin kokarina ina yi akansa Allah ya sani da don ta ni ce da tuni ba wannan zancen ake yi ba domin a ganina tunda auran ba farilla ba ne sai na yi kokarin ri'ke kaina da sha'awata na tsira daga takaicin d'anamiji.
Ya shigo Yana gaya mini an bar tibi a kunne na je na tashi Yusura ta je ta kwanta bacci ya dauketa a kujera. Ban ce komai ba na tashi na fita falon na sameta tana bacci sosai na kashe tibin sannan na tashe domin ta shiga daya daga cikin dakunan dake cikin falon ta kwanta ta kafe itafa a falon zata kwanta kan kujera. Ba na son matsa mata sai na kyaleta ta koma ta kwanta kan kujerar tana layin bacci. Ban kashe mata fitila ba saboda kada ta farka taga duhu ta ji tsoro tunda na lura zabuwa ce itama ba lefi.
Na same shi zaune a gefan gado bai kwanta ba amma ya cire jallabiyar jikinsa yana zaune da k'ananu na ciki. Jigum din da ya yi ya d'an ta'ba ni kadan ko zazzabin ne ya ji dare yake so ya dawo. Na daure na ce." Ya jikin fatan dai zazzabi ya gudu."
Lumshe idonsa ya yi a hankali ya ce." Na ji sauki alhmdullhi Doctor Saleh ai ba karamin likita ba ne, Allah Ya hore masa, ke ma na gode da kokarinki."
Na ce.'' Kokari akan me?"
Yana kallona ya furta." akan dawainiya da jinyar da na sanya ki."
Murmushi na yi na ce." Ba komai Baba."
Ya tsira mini ido yana kallo na haye gado ina fad'in.'' Ka kwanta ka samu hutu sosai da safe na san za ka sake samun kwarjin jiki."
Ya nisa kafin ya ce." Duniyar gabad'aya ta yi mini zafi Amina ina jin wani yanayi a jikina mara dad'i, d'aukaka ko wata rigar arziki sukan zamewa wanda Allah ya ratayawa matsala babba."
Hankalina na mayar kansa a nutse na ce." Kuma haka Allah Ya tsameka daga cikin dubban mutane ya rataya maka, ai wata ni'ima ce babba muddin ka yi amfani da umarinsa yadda ya ce shi kuma zai kare ka daga kariyarsa amma ina so ka sani dole ba zaka yi ta zama ba tare da jarrabawa daga Ubangiji ba. Kuma ba zaka hana mutane yin abinda zuciyarsu ke so ba, kawai ka yi ta addu'a da neman kariya."
Ajiyar zuciya ya sauke a nutse ya furta."Allah Ya kyauta na gode miki ina jin kunyar Hamusu bisa titsiyar da na yi masa d'azu a yanzu kunyar yaron nan nake ji wallahi ni kaina nasan ban kyauta ba yanzu da gaskiya ta bayyana Alhaji Sammani babban yarona da muka sha gwagwarmaya a baya shine ya shirya kashe ni dalilin tonuwar asininsa bayan take hakkin marayu she ya jima yana cutar da ni ta karkashin kasa ya kuma yi mini asarar wasu muhimman kadarorina gabad'aya ma ni ba wannan ne abinda ya dame ni ba sai mamakin halin d'an adam ban san me Sammani yake nema a wannan duniyar da ba madawwamiya ba.
Chapter 33 · 0% Book details