← Book details Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 33

Sashe 15

Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Cikin nutsuwa kamar bai ji zafin maganganuna ba ya ce.'' Ai na mayar dake dama na yi ne domin ya zama gargadi a gare ki. Kuma ba don ke nake tsaye akan abinda ya shafeki ba, saboda wasu dalilai ne, ke ki ka haifi Yusuf amma ya fi ki hankali, kuma saboda shi din na shiga lamarin, ai na san kakarsa ce ko ba itace ta haifi Aminu Salihi ba."
Cikin takaici da b'akinciki na furta." Ban mayu ba, wallahi ban mayu ba na saku har abada ni dakai dama can ba a son raina aka yi ba, ba zaka tozartani ba wallahi ko maza sun kare a duniya ba zan zauna da kai ba, kuma ko mutuwa Gwaggwo ta yi menene abinda ya dame ka, babu ruwanka ba na son munafurci." Na sake maimaita kalmar munafurci domin na tunzurashi.
Bai tunzuru ba a tsanake ya ce." Sai ki yi kuma ni dai na mayar dake shekaran jiya na yi sakin jiya da safe kuma na kudire a raina na mayar dake yanzu kuma na sanar miki, don haka har yanzu kina karkashin ikona."
Da sauri ya yanke wayar kamar ya san abinda yake bakina mai muni ne tabbas da bai kashe wayarsa ba sai dai ya ji ruwan ashar a kunnansa saboda yadda zuciyata take a tunzure. Na kasa motsi daga inda nake gumi na yanko mini tsabar tashin hankali kamar yadda ya fad'a a musulunce na mayu tunda ko jini daya ban yi ba kuma ka'idar musulunci jini uku ne na fita daga idda.
Hawaye masu zafi suka fara karakaina a kumatuna. Anti Yagana ta shigo d'akin da karsashinta ganin yanayin da nake ciki ya sanya ta d'an yi sanyi ta tsaya tana fuskantata..."Menene kuma?" Tambayar da ta yi mini kenan.
Cikin k'unci da takaici na ce." Anti Yagana a wannan karon dole ki yi hakuri na d'auki mataki da kaina domin siyarwa kaina mutunci. Yadda na lura da mutumin nan bashi da mutunci ko kad'an kuma yana yi wa mata kallon wulakantattu idan ba haka ba me zai sanya ka saki mace haka kawai babu hujja mai karfi saboda kawai jin dadi gobe kuma ka ce ka mayar da ita addinin bai ce haka ba Anti Yagana ki zauna ke kanki ki dubi lamarin nan a tsanake kada soyayyar da kike masa ta sanya ki danne lefinsa ba fa daidai ba ne abinda ya aikata mini."
Jiki a mace ta ce." Na sani wallahi Amina, kuma bayan ke wallahi tallahi babu wanda ya kai ni jin ciwon sakin da ya yi miki, ni yadda na fahimta kamar bashi da ilimin addini mai zurfi boko ce kawai take dawainiya dashi shiyasa yake ganin kamar abinda ya aikata ba wani lefi ba ne. Abu na gaba kuma kin san shi, abinda ba na sha'awar ya kasance da ni a rayuwata wallahi kema ba na sha'awar ya faru dake, ba na yi miki sha'awar zawarci da lissafin aure don ma Allah Ya takaita gidan alhji Muntari ba ki haihu ba, wannan dalilin ya sanya nake ta dannarki ki yi hakuri ki zauna kowace mace tana da kalubale."
Na ce." Anti Yagana kada ki ce na ki jin maganarki wallahi ba fahimci abinda kike gudu, amma dai don girman Allah wannan karon ki kyale ni da mutumin nan kada ki shiga ciki ki ja bakinki ki yi shiru kawai ki zuba mini ido."
"To wane shiri za ki yi akansa kin san dai shi namiji ne ke kuma mace tunda kuma ya ce ya mayar dake bafa yadda za ki yi dole ha'kuri ne naki."
Na sani anti Yagana ba shirin da zan yi akansa amma ba zan koma ba kamar yadda yake tsammani wallahi sai ya tako kafarsa garin nan."
Ta gyada tanà d'an murmushi ta ce." Abu me sau'ki ai tunda yana sonki za ki gan shi kuwa.
Ban ce mata komai ba har ta kama hanya ta fice daga dakin.
[8/31, 4:42 PM] Aunty B: 70
Tun cikin dare na kammala shirye shirye na don haka gari yana wayewa na fito a kintse da zummar d'aukar hanya tunda d'akin da nake yana da bandaki ban fito ba sai da na shirya tsaf tukkuna. Gabad'aya suna falon ana shirin karyawa hadda maigidan a zaune bai fita ba dama ba kasafai yake fita da wuri ba idan juma'a ce.
Fitowata ta d'auki hankalinsu gabad'aya na gyara yanayina don ba na so ta dakatar da ni daga kudirin da na yi. A tsanake na ce." Anti Yagana na shirya fa zan tafi kamar yadda muka yi magana jiya wallahi da Gwaggwo na kwana a cikin raina."
Tana kallona ta ce." To kin gayawa mijin naki ko dai ?"
Eh kawai na ce mata a takaice. Yadda ta zuba mini ido shi ya tabbatar mini da cewa ba ta yarda da amsar dana bata bata
Yusi yana gefe a zaune ya yi nairainarai da ido saura kiris ya fashe da kuka dan tun jiyan nan dana mare shi bai zo wajan da nake ba. Kallo d'aya na yi masa na kawar da kaina daga kansa domin Ina so na horar dashi akan abinda ya aikata ko don gaba ya kiyaye furta abinda ba shikkenan ba.
Cikin sigar zolaya Babansu Fadila ya ce." Madam ba gaisuwa ne ko na yi wani lefin ne kuma."
Cike da jin nauyi na ce." Yi hakuri wallahi na d'auka dana fito na gaisheka, gabad'aya hankalina ne baya jikina."
Ya ce." Amma dai kya bari ki karya tukkuna sai ki tafi, da za ki bari ma akwai motar da zata tashi karfe goma sha daya na safe sai na kira direban yanzu."
Na ce." Anya kuwa zan bari ai ka barshi kawai zan iya shatar motar ma gabad'aya babu damuwa.
Cikin dai zolayar dai da ya saba da sigar wasa ya ce." Au na manta Hajiya ce fa uwargidan a wurin Yallabai."
Murmushi kawai na yi na dubu anti Yagana tana tambayata yaushe zan dawo.'
Na ce." Nan da sati guda in sha Allahu zan dai kira ki idan zan taho din."
Ba ta ce komai ba ta fara tsiyaya kunun gyadar cikin wani madaidaicin fulas tana fad'in." Ki tafi dashi ko a mota sai ki kurba kina dai sauka ki kira ni."
Na ce." To shikkenan in sha Allahu."
Hanyar fita na kama na ji muryarsa har tana rawa yana cewa." Mama ki gaishe mini da Gwaggwon."
A takaice na ce." Za ta ji in sha Allahu. Na yi saurin ficewa addu'a d'auke a bakina.
Ina fita harabar gidan na ci karo da Sukairaju zaune a bakin kofar masaukinsa yana waya. dauke kaina na yi, na sake hade raina sosai. Ido ya zubo mini Ina kallonsa ta gefan idona. Ban tanka masa ba na kama hanyar fita sai ya taso da sauri ya biyo bayana da wayar a kunnansa da maigidansa yake waya saboda yadda yake yin kasa da murya cikin ladabi kamar yana kusa dashi.
"Ranki ya dad'e barka da asuba."
Muryarsa na ji a daf da ni, na juya ina dubansa yana biyo bayana da wayar a hannunsa..
A takaice na ce" Barka kadai Sukairaju ya kake?"
Ya ce." Alhamdulillahi, idan ba matsala Ina iya yi miki rakiya don yanzu muka gama magana da oga ya ce na biyo bayanki."
Cikin jin haushi na ce." Makauniyace ni, da za ka biyo bayana ko kuwa ban san gari ba."
Ya girgiza kai cikin ladabi ya ce." Ko daya kulawa ce da kuma bin umarnin maigida."
Na ce." To ka kira shi ka gaya masa na ce ba na son kulawar wannan wace irin masifa ce ne ."
Sai ya tsaya ya yi sararo. Na ja tsaki na fara tsayar da abin hawa shi kuma ya fara laluban wayarsa da sauri ya kara a kunne yana cewa." E to ga mu nan ni da ita atare a bakin titi tana tsayar da mashing tana tare da k'aramar akwati."
Ina jin sautin muryarsa amma ban ji abinda yake cewa ba. Daidai lokacin adaidaita sahun dana tsayar ta yi parking na yi saurin shiga. Shi ma da sauri ya zagaya ya zauna kusa da direban shi kuwa ya ja babur din ya hau titi.
Takaici kamar ya kasheni, ni wulakata mutum ba dabi'ata ba ce, kuma ba na so na fara akan mutumin nan tunda na lura shi ma yana gyara hanyar abincinsa ne, kuma duk umarnin da aka bashi dole ya bi.
Ban ce masa komai ba har muka isa tasha na fito, shima ya fito da kudi ya biya direban ya zo yana ko'karin kar'bar akwatin hannuna.
Na ce." Kira mini ogan naka a wayarka."
Da sauri kuwa ya fito da wayar daga gaban aljihunsa ya kira shi ya miko mini wayar kafin ya daga na matsa can gefe wajan da babu hayaniya sosai duk da safiya ce amma tashar cike take da jama'a.
Yana d'agawa ya fara da cewa." Sukairaju ya aka yi, na gaya maka duk inda ta sanya kafarta ka ajiye taka anan ka kula sosai da ka ji ko?"
Na ce." Bashi ba ne ni ce Amina."
Ajiyar zuciya ya sauke ya furta a Ina ki ka ajiye wayarki ina kira baki daga ba." Lokacin da ya kira tana cikin handbag d'ina kuma na ji kiran ina sane ban daga ba.
Na ce." Tana hannuna wayar ba ni da lokacin d'agawa ne."
"Okey na ji, ina za ki je da sanyi safiya haka harda akwati kin san duk inda ki ka nufa ba ki tsira ba tunda da aurena a wuyanki."
"Shiyasa kenan ka bada tsarona saboda kada na gudu yawon bin maza ko."
Shiru ya yi bai tanka mini ba. Na ce." Idan kana kan layi to don Allah ka umarci wannan gardin da yake bina a baya ya koma, ko kuma ya tattaro ya dawo karkashin aikinka dan banga amfanin zamansa a gidan mutane ba face dora musu nauyi da ya yi, domin ni na gaya maka ban mayu ba har abada zama ya kare a tsakaninmu."
Hankalinsa a kwance ya ce" mutan gidan ne suka ce miki sun gaji dashi saboda yana dora musu nauyi ko kuma sharri ki ka yi musu."
Da sauri na tari numfashinsa ." Sai sun fad'a sannan za a gane yanayin rayuwa ya za a yi baligin mutum kamar wannan ka zo ka ajiye shi a gidan mutane da sunan bada tsaro akwai wani tsaro ne wanda ya wuce wanda Allah yake ba ni tun kafin a haife ni."
"Zan kira anti Yaganar na ji shin cewa da yawunta ne ki ke fad'in hakan, na san halinta da karamci ba za ta ci zarafin bako ba."
Jin abinda ya ce sai jikina ya d'an yi sanyi nasan halinsa tsaf zai iya kiranta ya tambayeta.
Kashe wayar na yi ban tsaya saurarar abinda yake cewa ba.
Kafin na mikawa masa abarsa ya kara kira na daga wannan karon cikin tsare gira da kaurarriyar muryar da babu wasa ya furta." Ki gaya mini Ina ki ka nufa yanzu domin na ji hayaniya da karar ababan hawa hala kina cikin tasha ko?"
Na ce." Eh ina tasha zan nufi kano domin duba jikin Gwaggwo da izinin Allah, zan kuma biya na gaishe da Hajja."
Ya sassauta yana fad'in." Na amince dai ki je ki duba Gwaggwon amma ban amince miki zuwa wurin Hajja ba, ke kwata kwata ma ba na so asan kin shiga garin, ki zauna a gidanku kawai kwanaki biyu zan gama yi muku shiri sai ku biyo jirgi ku dawo gida ga'badaya."
Na ce." Gaskiya ba zan iya shiga garin kano ban je wajan Hajja ba sai da ka yi hakuri.'' Kai tsaye na fadi hakan domin a karon farko na fahimci akwai abinda yake b'oyewa dama na san duk abinda yake faruwa ba ta sani ba."
Ya sake sassauta murya cikin sigar rarrashi ya ce." Na ji kije amma kada ki gaya mata duk abinda ya faru tsakaninmu sanin kan ki ne bata da lafiya."
Na ce." Ai ta inda aka hau ta nan ake sauka Yallabai, ai ba auran 'yar tsana muka yi ba sai da waliyyai da shedu suka shaida to me zai sanya kuma a boye musu saki yana da kyau ta sani yanzu saura igiya biyu."
Diriricewa ya yi ya fara fad'in." Ki saurare ni ki ji, na gaya miki wallahi muddin ki ka sanar da Hajja wani abu sai na sa'ba miki, kin ji na gay......Datse wayar na yi Ina jin wasai a cikin raina na tabbata ta wannan hanyar ma kadai zan hukunta abina.
Chapter 15 · 0% Book details