Sashe 17
Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
To alhamdulillahi yanayin yadda na ga jikin Gwaggon alhamdulillahi ya yi sau'ki sosai, mun d'an taba hira kad'an dukda ba sosai muryarta ke fita ba amma dai Ina fahimtar abinda take cewa. Bacci ya kara surarta. Likitan da yake kan duty a lokacin ya tabbatar mana da cewa hakan shine samun lafiya domin a hankali duk sai ta rama bashin baccin da ta ci.
Kai tsaye gidana na kuntau Hamusu ya wuce da ni bayan mun fito daga asibitin kenan. Na ji dad'in yadda na ga ya sake k'awata shagonmu ga kawunan keke nan na surfani da kuma na dinkin zare daban daban yara suna ta aiki ko'ina haske tare da decoration masu kyau ga hotonan jaruman film nan wad'anda suke tashe irinsu Mommy gombe Aisha Najamu Ruky Alim Maryam Yahaya Asma'u Gwarwashi Maryam Labarina da sauransu sun an yi banner dinsu cikin styles na d'inki daban daban. Ga kuma na mutane nan kala kala an gama a rataye
Akwai sabbi ido daga cikin yaran da suke aiki wad'anda na sani kad'an ne daga ciki. Na tsaya tare da cire nikab din fuskata domin mu gaisa. Gabad'aya suka mike wad'anda muka saba da su a can baya suka dinga dariya anti Amina ziyarar bazata."
Ina dariya na ce." Eh mana kuma na ji dad'in ganinku lafiya da yadda aka samu cigaba na gode muku sosai."
Kusan a tare suka ce." Mune da godiya anti Amina, Allah Ya sa a fi haka d'aukaka Ubangiji Allah Ya raya miki zuria." Na amsa da amin cikin jin dad'in addu'ar da suka yi mini na wuce ciki Hamusu ya biyo bayana da akwatin dana zubo kayana Yana sake jadadda mini irin yadda 'yan film ke kawo dinkunansu wurin.
[9/1, 5:22 PM] Aunty B: 71
Na ce." Wallahi na gani Hamusu an samu cigaba sosai, kana mutukar kokari kwarai da gaske, ai kyau da ingancin aiki ne ya sanya suke turereniyar zuwa shagon tabbas ya kamata a wannan shekarar kai da Usaini na kira ku ga gwarazana, domin shi ma ta b'angaransa alhmdullhi komai yana tafiya gashi dai bai kai shekarunka ba amma yana da fasaha da nasibi."
Ya ce." sosai kuwa anti Amina Usani yana k'okari don kwanaki ma dana je duba shagon na ga har da 'bangaran huluna da takalma bayan na atamfofi da leces wanda dasu aka 'bude shagon.
Na ce." Ba a fi wata uku ba ya kira ni da shawarar hakan da yake ya san ta kan huluna ya ce mini za a samu alheri sosai, na ce to shikkenan sai mu jarraba mu gani, cikin ikon Allah kuma ana ganin cigaba kasan da kad'an ake kai wa matsayin babba."
"Gaskiya ne anti, yanzu ki huta zan je bakin titi na sayo miki abinda za ki ci."
Na ce." Da kuwa ka kyauta Hamusu don wallahi wata irin yunwa nake ji, ka ga kunun da anti Yagana ta had'o ni dashi ko kad'an ban kurba ba."
Da sauri ya kama hanyar fita Yana fad'in." Ai dole anti ki ji yunwa bari yanzu zan dawo in sha Allahu
Ya fice a gaggauce. A tsanake na dubi ko'ina na gidan tsaf kamar mutum yana rayuwa a ciki har da sabon kafet Hamusu ya shimfida a tsakiyar falon domin dai na san kalar wanda na fita na bari ba irinsa ba ne.
Girgiza kaina na yi cikin zuciyata na furta abu ne mai mutukar wahala a wannan zamanin a samu mutane masu nagarta da kyawun zuciya kamar iyalin Gwaggwo. Yaya Aminu da d'an'uwansa Hamusu mutane masu hankali da sanin ya kamata.
Jakata na ajiye domin jin ana kiran sallar magriba da so samu ne na fara yin wanka amma ba hali saboda duhun magariba ya shigo sai an yi Ishai tukkuna.
Ko matsawa ban yi daga wajan ba kira ya shigo wayata dake cikin handbag dina.
Ina duba wanda ya kira na ajiye ban daga ba na nufi bandaki ina jin tana ta ringing ta katse wani kiran ya sake shigowa, babban abinda ya tsana shine ya kira waya ba a d'auka ba, ina jin ma ni kad'ai ce nake masa wannan shegantakar shiyasa yake ganin abin banbarakwai yake kuma yi masa zafi.
Ya kira ya fi sau shida ban dubi wayar ba. Sallolin da aka bini bashi na rama. Kafin na d'ora ta magriba da ta riske ni. Ina sallamewa ya sake kira idona akan wayar ta katse na cigaba da jan carbi mai lamba da yake cikin yatsana.
Koda Hamusu ya dawo shima sai da ya jira na kammala tukkuna. Ina dubansa ya ce." Anti ko kin kar'bi darika ne kina wazifa kema?"
Kai na girgiza na ce." Ko daya Hamusu ka'idata ce dama ina zama bayan magriba na yi wa Annabi salati dubu daya muddin kaga ban yi ba kuwa wani muhimmin abu ne ya rike ni."
Ya gyada yana fad'in." Allah Ya ba mu ikon yin ko yi daku anti."
Na amsa da Amin Ina duban uban ledojin da ya lodo. Na ce." Wannan duk abincin ne Hamusu."
Ya ce." A a anti akwai kayan shayi da wasu abubuwan da na san lallai za ki bu'kace su."
Na ce." Sannu na kuwa gode wallahi."
Yana bud'e ledojin ya ce." Af anti kin ga zan manta ko ina kan hanya Yallabai ya kira ni a waya yake tambayata muna tare na ce masa e ba ki jima da sauka ba, na fito sayo miki abinci ne, shine ya ce idan na dawo na kira shi zai yi magana dake na ce ko wayarki ta mutu a cikin jakata baki sani ba."
Na ce." A a ina da caji wata'kila kawai matsalar network ne."
Ya fara laluban wayarsa wanda ya tabbatar mini da cewa shi din zai kira ban ce masa komai ba yana jin wayar ta fara shiga ya miko mini cikin nutsuwa kuma ya tashi ya fita.
Yana d'agawa na ji sautin muryarsa ya fito sosai tunda handsfree wayar take. Tsigar jikina ce ta motsa jin maganarsa sautari dama hakan tana faruwa da ni muddin zan ji ko na kalli wani bangare na jikinsa sai jikina ya motsa ban san menene dalilin da ya sanya motsinsa ko maganarsa ko wani abu da ya danganci jikinsa ke tayar mini da hankali ba, kuma duk mazan dana aura akansa kawai nake jin hakan.
Na d'an samu nutsuwa tukkuna a nutse na ce." Ba shi ba ne ni ce ina yini."
Bai amsa mini ba ya furta." Abinda ki ka yi a ganinki shine daidai ko? Kin shirya wulakanta ni a idon mutane da abokaina, kina so ki nunawa duniya kin fi karfin kowa ciki har da ni mijinki da wad'anda suke gaba dake ko Amina."
A nutse na ce." Me na yi maka yanzu?"
'Kwafa ya yi ya cigaba da cewa." Sukairaju ya gaya mini yadda kuka yi dashi, idan ba ki shirya wani abun ba me zai sanya ki guje masa harda yaron da ki ka haifa kin bar shi a can me hakan yake nufi?"
Shiru na yi masa ban ce uffan ba. Yadda dai yake maganar a kufule shi ya tabbatar mini da cewa yana cike da b'acin raina wanda ni dama hakan nake so, na lura kuma zargi yana daya daga cikin d'abiunsa wanda kafin ya daina sai an yara.
Jin ban ce masa komai ba sai ya kara hasala." Na gaya miki dai kaga ki kuskura ki gaya Hajja wata maganar da zata daga mata hankali kin fi kowa sanin yadda ta d'auki lamarinki jin wata magana ka iya janyowa ciwonta ya tashi."
Na ce." Kasan da hakan me ya sanya ka aikata, ai kai ya kamata ka kiyaye abinda zai sanya har ciwon nata ya tashi ba ni ba, ba zan munafurceka ba na gaya maka ko ban gayawa kowa cewa ka sake ni ba ita da ta had'a auran dole ta sani yanzu babu aure a tsakaninmu."
Cikin inda-inda tare da diriricewa ya furta." In ji uban waye ya ce miki babu aure a tsakanina dake, na gaya miki tun jiya na mayar dake kuma wallahi kin mayu, ko kin so ko kin ki."
Na yi shiru ban ce masa komai ba. Ya sake sakin ajiyar zuciya duk Ina jinsa ya ce." Yanzu kina ina, a gidanku ki ka sauka dai ko.
Babu wata damuwa na ce." Ina gidana na kuntau a can na sauka dan zan fi sakewa."
Cikin tsananin tashin hankali ya ce."Ki ka sauka a gidanki hakan me yake nufi kenan, ba ki da gidan iyaye ne?"
Na ce." Ni nasan kaina haka zalika ma wadda ta aura maka ni ta san wacece ni, mahaifina ya san wacece Amina, idan zan bar gari na tafi wajan da babu idon wanda na sani sai bare wallahi tallahi na tabbatar da cewa mahaifina ba zai zarge ni ba to balle kuma anti Yagana data saki nono ta ba ni, amma ina mamakin yadda aka yi kai kake yi mini mummunan zargi irin wannan, motsi kad'an zan yi a tuhuma yake kayi maza ka ya'ki zuciyar da take kawo maka illolina dan na rantse maka da Allah idan kana biye mata daf take da ta tarwatsa maka rayuwa."
Shiru ya yi bai yi magana ba na ce." Zan bashi wayarsa idan baka da abin fad'i."
Gyaran murya ya yi ya dan ayi amfani da sanyayyiyar muryar da ya arota a lokacin yana fad'in." Zan shigo kanon gobe ki zauna a shirye zamu koma tare."
Na ce." Nan fa daya ai ko zan koma auranka to fa ba zan koma legos ba wallahi, zan zauna anan din ba ni da damuwa duk lokacin da ka yi ra'ayi ka zo kawai."
Ya ce." Hakan da ki ke yi shi yake sanyawa zuciyata wasiwasi akanki. Nafi kowa sanin cewa ba ki da hakuri ta fannin jima'i, me yasa zan barki a wani wajan ni kuma ina can uwa duniya ki cire ranki ba ni da ra'ayin raba gidana.