← Book details Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 33

Sashe 26

Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Cikin hukuncin Allah kuwa bacci mai nauyi ya kwashe shi. A hankali na zame jikina na dan kwanta a gefansa Ina kallonsa yana sauke numfashi mai tafe da sarkewa daga kirjinsa. Har yanzu ina jin d'umin jikinsa a jikina da gaske zazzabi da mura ne suka kama shi da gaske.
Zannuwan na gyara sosai ya rufe har kafafunsa amma ban da fuskarsa saboda fitar numfashi.
Na yi amfani da wani karamin mafici na roba Ina dan kore masa sauron da yake ta zarya a d'akin.
idona biyu asuba ta yi. Masallatai ana ta kiraye kirayen sallah.
Na tashi zaune a hankali ina dubansa lokacin ya motsa da wani irin tari wanda yake nuna alamun kirjinsa a cushe yake da majina.
Cike da zullumi cikin zuciyata na kama salati domin ni a ganina wannan dan dukan ruwan bai kai ace ya lafke irin haka ba.
Ya tashi zaune yana cigaba da tarin na zuba masa ido har ya lafa a hankali na furta."Sannu."
Ya amsa can kasa kafin ya ce." Ya zan yi na yi sallah ne, ni kaina na fara nadamar zuwa gidan nan naki."
Na dubi rijar jikinsa duk ya yi wata kala ya firgice na dan ji tausayinsa kad'an domin da gaske baya jin dadin jikinsa.
Na ce." Ni ban san yadda za ka yi ba. Ga kayanka nan duk sun jike har gajeran wandon da singilitin."
Ya yi shiru yana dubana kafin ya furta "Zan yi sallah a haka ai akwai uzuri ki zuba mini ruwa." Ban ce komai ba na tashi na shiga bandakin da yake jikin d'akin na zuba masa ruwa a buta Na fito lokacin har ya sauko daga katifar na bashi hanya ya shige bandakin.
Dadduma na shimfida masa na jira shi ya fito tukkuna ni ma na shiga na dauro alwalar....
Koda ya idar da sallar katifar ya koma ya kwanta bai ce mini komai ba a wannan karon tarin shi yafi matsa masa.
Ni ma ban ce dashi komai ba na kwashi kayansa na fita dasu. Na samu Yusura tana motsi na dan bubbigi kafarta ta tashi da sauri na ce." Taso ki yi alwala."
Na fita tsakar gidan da kayan a hannuna wanke su na yi tas na shanya cikin ikon Allah rana ta fito mai haske sai na mayar da kayan idonta domin su yi saurin bushewa.
Yusura ta fito tana fad'in." Mommy ina kwana mun yi baki ne?"
A takaice na bata amsa da cewa." E jiya kina bacci ba."
Ba ta sake cewa komai ba ta nufi kicin tana cewa." Dame zan fara mommy."
Na ce." Ki dora ruwan shayi ki sanya kayan kamshi sosai ki dan sanya barkono a ciki ko uku ne."
Ta amsa da sauri kafin ta bude kicin din ta shiga.
Na sake komawa d'akin na kwashe takalmansa na shige masa dasu ciki. Na dube shi har yanzu bacci yake yi lakadan.
Wayata na d'auka na fito falon na nemi Hamusu yana d'agawa na ce." Ka tafi asibitin ne baka shigo mun gaisa ba."
Da sauri ya ce." Haba dai anti na ce bari na dan jira gari ya kara yin haske sai na shigo mu gaisa kafin na wuce ko kina bukatar wani abu ne.
Na ce." Sosai kuwa wai d'an dukan da ruwa ya yi muku jiya fa Yallabai na kwance kashir'bar mura da zazzabi har da tari sun kwantar dashi."
Cike da damuwa ya furta." Subahanallahi! ai anti shiyasa nake ta ce miki ki bude kofar kin san akwai yanayi na girma da shekaru bayan haka kuma jikin bai saba ba, ni kin ga lami lafiya na kwana kuma na tashi garau da ni, ba na jin wani sauyi.
"Hakane yanzu nan babu wani chamis da suka bude tunda yanzu gari ya waye kana da abun hawa ka je can asibitin wurin masu sayar da magunguña ka samo masa maganin mura da tari amma mai kyau."
Da sauri ya furta." Anti ba ma sai na je har zan ba Ina fita babban titi zan samu."
Na ce." Shikkenan sai ka dawo.'' Shi ya riga ni kashe wayar kafin na ce me na ji tashin karar babur d'insa Hamusu kenan.
D'akin na koma ina jin Yusura na ta aikace aikace sosai yarinyar ta horu da aiki gashi nan babu abinda ba ta iya ba na rayuwa.
Ido a bud'e na same shi yana numfashi da baki. gabana ya bada wani irin sauti yadda ya tsayar da idanuwansa a saman rufin dakin sai naga kamar wanda ba a jima da zare masa rai ba.
A sukwane na nufe shi kafafuna na kyarma. duban da ya yi mini shi ya dan sassauta fargabata. Na zauna kusa dashi ina fad'in ." Ka tashi ga tea na dafa maka mai kayan kamshi zai taimaka maka sosai muryarka ta bude yanzu Hamusu zai kawo magani sai kasha, amma ni ba na tsammanin wannan dukan ruwan ne ya haddasa maka wannan murar saboda ka fa yi tafiyar mota."
"A jirgi na zo ni malama." Ya fad'a yana lumshe idonsa. Na ce.'' Na sani amma ai ka ninka dambatta sau biyu wannan iskar daka sha'ka ta isa sanya maka lalurara.
"Ke a tunaninki a wace irin mota nake irin wannan tafiyar?"
Shiru na yi ina nazari. Gaskiya ne a irin motocinsa babu wata kafa da iska zata shiga har ta janyo masa toshewar hanci manyan motoci ne masu tsaro.
Ya furta." Ko kin so ko kin ki kece sila, ni ai ban zo da niyyar kwana ba ruwan da ya ritsa dani ne, kuma na gaya miki sulhu na zo wurinki ba wani abu ba."
"Ai sulhu ya k'are tsakaninmu na gaya maka ba zan koma can ba gaskiya abinda yake zuciyata kenan."
Na fad'a tare da kawar da kaina gefe.
Ya nisa kafin ya ce." Na ji amma kin san kema ba ki da hujjar da za ki ce sai a nan za ki zauna ko ba zai yiwu ba, muddin na amince miki akan bukatarki dole ni ma ki bi ra'ayina ki zabi daya daga cikin gidajen da nake da su anan ki zauna."
"Menene da nan din?"
Bai kai ga magana ba attishawa ta tare shi ya dinga yi har sai da na tashi na nemo masa tissue ya dinga fyace majinar data tsinke. Ya tara tissue din a wuri d'aya na kwashe na je na zuba ashara na dawo na same shi har yanzu yana ta attishawar dai.
[9/10, 9:27 AM] Aunty B: 77
Lallai a yau na sake tabbatar da cewa mura tana daya daga cikin manyan laluran da suke galabaitar da jikin dan adam, daga jiya zuwa yau gabad'aya kamminsa sun canza fuskarsa har ta dan kumbura ga dukkan alamu ma dai yana da matsalar sanyi a jikinsa shiyasa da aka motsa shi ya tashi gabad'aya.
Fita na sake yi daga d'akin na samu Yusura tana soya indomi da kwai na ce ta miko mini fulas din shayin da yake gefanta ta had'o mini da kofuna biyu masu dan girma na gilas.
Na sake komawa d'akin yana kashingide attishawar ta lafa.
Ya bi ni da kallo a lokacin da na kàrasa wurin da yake har na tsiyaya masa shayin da yake ta tiriri da k'amshin kayan shayi bai d'auke idonsa daga kaina ba. Ni ma ban ce masa komai ba na fara motsa masa shayin har sai da ya yi daidai yadda zai yi dadi sha. Na mika masa babu jayayya ya kar'ba har da godiya.
Gefe na zauna ina d'an sauke ajiyar zuciya. Na ji yana cewa." Har yanzu ban gayawa Hajja kina garin nan ba, haka zalika ma na gargadi Yusuf akan kada ya sanar mata Ina so ni dake mu gama magana yanzu da daddare na d'auke ki a mota domin ki duba gidan da za ki zauna."
Ba tare da na kalleshi ba na ce.'' Wai me yasa ba ka so Hajja ta san abinda ya shafe mu ne, kada fa ka manta mahaifiyarka ce, baka da hurumin boye mata abinda yake faruwa da rayuwarka."
"Wannan ai ba abin alheri ba ne shiyasa nake lullube mata."
Na ce.'' Yanzu ka amince kana kuskure ko?"
Ya d'aga mini kai alamar E.
Girgiza kaina kawai na yi ban kuma yi mamakinsa ba domin duk abinda yake yi mini a yanzu yana yi domin ya samu kaina, shiyasa duk abinda na ce ya yi kai tsaye yake amsawa babu ja'inja, a ganina kuma hakan ba zai hana shi watarana idan na ha'kura ya sake kuntuka mini ba."
"Na ji dadin shayin nan sosai na gode miki."
Maganarsa ta dawo ni da hayyacina. Na dube shi sai na ga yana kallona shima kafin a hankali ya ce." Kin kasa samun nutsuwa ballantana ni ma na samu nutsuwar da zamu cigaba da gudanar da rayuwarmu, akwai abinda nake so na gaya miki wanda ya shafe mu ne gabad'aya da duk wani makusancina amma ina fargabar ki juya mini magana ko ki ji kamar da gayya na gaya miki."
A tsanake na ce." Ni babu irin wannan gilin a zuciyata me zai sanya ka sanar da ni alheri kuma na ji b'akinciki idan ba ka sanya ni daya daga cikin masoyanka ba to na tabbatar zan zo a ta biyu don haka ina yi maka fatan alheri akan duk abinda ya sami rayuwarka."
"Na gode sosai, Allah Ya yi miki albarka."
D'akin ya yi shiru ni ina ta jiran na ji ya gaya mini abin alheri ya yi shiru yana ta kurbar shayin yana lumshe ido da gaske ya yi masa dadi. Na ce.'' Idan bai isheka ba akwai sai na tsiyaya maka."
"A a, ya isa wannan din an jima dai kafin na tafi zan kara shan wani."
Na kar'bi kofin daga hannunsa na ajiye sai na ji ya ce." Kin cire key din motata cikin aljihun rigata ko?"
Ban ce komai na janyo handbag d'ita na d'auko masa mukkulin .
"Ina Hamusu ba shi ya bude motar ya debo mini wayoyinsa.
Rufe bakinsa ke da wuya Hamusu ya shigo gidan na tashi da sauri na fita na same shi suna magana da Yusura hannunsa ri'ke da ledar magungunan na kar'ba tare da mika masa key din motar na ce." Yallabai ya ce ka debo masa wayoyinsa a mota."
Ya kar'ba ya fita da sauri
Allah Ya sa jiya da ya yi mini sayayya ya sayo rowan roba swan na d'auki daya na sake komawa d'akin.
Na ce." Ga magunguñan wayoyin kuma yanzu zai kawo."
Ya kar'bi ruwan da maganin Ina daga tsaye duk Ina kallonsa ya 'balli maganin ya sha. Na ce." Ko na dan dafa maka wani abu mai dan nauyi kafin ka tashi nasan maganin mura da kashe jiki wata'kila ma bacci ya d'auke ka yanzu."
Ya ce." Da kuwa kin kyauta amma towo na garin dawa, miyar kuka kuma."
Na ji shigowar Hamusu a karo na biyu muryarsa a falo Yana fad'in." Anti ga wayoyin." Fita na yi da sauri na amso masa shi kuma ya juya zai fita na ce." Akwai abin kari Yusura ta yi Hamusu ka zauna ka karya zata had'a maka komai sannan don Allah idan ka shiga cikin gari ka hado mini kayan towon dawa."
Ya ce." In sha Allahu anti."
K'aramar wayar a kashe take babbar ce a kunne na mik'a masa ya kar'ba cikin nutsuwa ya fara dubawa, ganin haka sai na juya zan fita hankalinsa na kan wayar ya ce." Ina za ki je kuma ke da ki ke jinya."
Dawowa na yi na zauna ban ce komai ba.
Ya d'an duba abinda zai duba kafin ya dube ni a nutse ba tare da nuna nishad'i ba ban dai sani ba ko b'oyewa ya yi ya furta." Kin san da cewa Hauwa tana da juna biyu?"
Gabana ne ya buga da karfi sakamakon jin maganar da ta yi tsalle ta fito daga bakinsa ban kuma tsammaceta anan kusa ba.
Sai da na yi namijin ko'karin daidaita kaina don gudun kada ya gane kid'imewata na kar'bi maganar da ya dumfare ni da ita da annashuwar da ban shirya yinta ba na ce." Kai ma sha Allah ko shine dama abinda ka ke cewa za ka gaya mini?"
Ya gyada kansa da kwarin gwiwa ya furta." Kwarai kuwa na so na gaya miki tun kwanakin da suka shige to ban san yadda za ki ji a ranki ba, sai kuma wannan rikicin ya b'alle a tsakanimu zan fi so ki samu nutsuwa mu daidaita a tsakaninmu ke ma ki samu na ki cikin zan ji dad'i na ga kuna yi mini jereran haihuwa."
Na danne abinda yake yun'kuro mini na tsantsar kishi da tausayin kaina na furta." Na taya ku murna sosai, Ubangiji Allah Ya raba lafiya ya kuma raya abinda za a samu. Maganar na samu ciki na haihu ina ga abu ne mai wahala domin ba abin wasa ba ne d'aukar ciki da rainonsa balle a zo kan k'adami na haihuwa. Tunda har jininmu bai hadu ba ina ganin mu ha'kura kawai da haihuwar nan Yallabai ai kai baka da matsala ni ce ma abin tausayi."
Na kare maganata idona a tsakiyar nasa idon.
Chapter 26 · 0% Book details