← Book details Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 33

Sashe 11

Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta dube ni jiki a sanyaye." Ni fa Amina na fara zargin lamarin nan naki anya babu sa hannu a ciki, mutumin nan fa wallahi yana sonki ba zai iya sakinki cikin hayyacinsa ba wata'kila ana dan birkita masa tunani shiyasa ke din ma ya kasa aminta dake yake tsiro da abubuwa daban daban.
Shiru na yi ina nazarin maganarta. Zan iya gazgata maganarta tunda na gani da idona a lokacin da inna Uwani take yayyafin rubuta a wajan benansa. Amma idan ma da asirin to tabbas akwai hali da kuma dabi'a.
Ta shi ta yi zata fita duk ta ki'dime tana daf da kofa na kira ta a nutse na ce." Anti Yagana don Allah kada ki kira mutumin nan a waya dan Allah ki yi mini wannan alfarmar."
Ta ja ta tsaya tana dan kallo kafin a sanyaye ta ce." To ai yana da kyau a tambaye shi dalilinsa ko."
Na ce." Dalili da ba zai wuce abinda na gaya miki da farko ba. Kishi zargi giyar kud'i."
"Amma dole mahaifiyarsa ta san da abinda ya faru Amina, domin bahaushe yana cewa ta inda aka hau ta nan ake sauka."
Na ce." Itama din ba za ta ji daga bakinmu ba shi ya fad'a mata. Ni dai tsorona ma kada wata magana ta fita duniya ta ji na shiga bakin duniya kin san shi sha'aninsa a waje yake motsi kad'an manema labarai za su fara watsawa shine babbar damuwata kuma kin san yadda da dama mutane suke yi wa macan da take gudanar da harkokinta a internet ko da bata aikata komai halalinta take nema sai a juya mata manufa a yi ta jifanta da bakaken magana."
"Babu abinda zai faru in sha Allahu ma ina fatan kafin zuwa gobe ya mayar dake shikkenan babu wanda ya ji ya kuma ga ni." Tana gama maganarta ta fita daga d'akin a gaggauce.
Ban fita ba tukkuna sai da na yi wanka da yake da bandaki a cikin d'akin na kimtsa jikina abin yana ta sasakata a zuciyata ina dannewa idan takaici ya yun'kuro mini sai na ambaci Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
Da kyar na iya kurbar shayi ban iya hadawa da borodi ba saboda lami nake jin bakina. Anti Yagana ta fito cikin shiri zata fita na ce." Ina kuma za ki je"
Tana gyara gilashin da yake idonta da yake tana da dan matsalar Ido wanda yasa asibiti suka yi mata gilashi take amfani dashi idan zata fita ta ce. " Ba zan ji ma zan dawo kafin azuhur."
A cikin raina na ji cewa saboda matsalata zata fita.
Na ce." Anti Yagana ban san ki da biye biyen malamai ba don Allah kada ki fara akan wannan karamin dalilin, kada ki yi wasa da tunaninki, ni dake mu zauna mu tattauna abinda zai taimake mu. Nasan akan duk abinda ki ka tashi hankalinki, amma ki sani kowane bawa yana tafiya ne da kaddarsa, kuma mutumin nan bashi kadai ba ne namiji akwai su da yawa, idan Allah Ya kaddara mini sake wani auran nan gaba sai ya had'a ni da wanda ya fishi.
Jikinta a sa'bule ta ce." Da wai zuwa zan yi a yi mini istahara ta musulunci Amina, idan kuma da dan wani taimako ko rubutu ko hayakin da za a baki sai ki yi amfani dashi domin sake janyo hankalinsa tunda dai ni na tabbatar da cewa mijinki yana sonki."
Murmushin takaici na yi na ce." Anti Yagana ai maganar so da k'auna ta kare tunda har ya sake ni, ni dai abinda nake so ki samu nutsuwa don Allah mu barwa Allah."

Ta gyada tana dan nazari kamar ta d'auki maganata sai kuma a zabure ta daga labule zata fita take cewa." Bari dai na dawo ai na san irin malaman da zan je wurinsu.
[8/27, 5:50 PM] Aunty B: 68
Ina nan zaune ina sa'kawa da kwancewa Sahura ta kira ni a waya tana bin ba'asin kiran da na yi mata cikin dare kawai sai na ce mata mistake ne ni ban san ma na kira t ba sai yanzu da ta yi magana. Muka dan ta'ba hira kad'an kafin mu yi sallama. Na kira Yusi na tambayeshi akan kaiwa Sukairaju abin kari ya ce mini tun d'azu.
Na sauke ajiyar zuciya tare da bashi umarnin tafiya har ya juya kuma sai ya tsaya yana tambayata wai yaushe za mu tafi tunda yau kwananmu uku haka baba ya ce mu yi kwana uku.
Rashin amsar da zan bashi ya sanya na ce ya fita ya ban waje. Ya kama hanya ya fita jikinsa ba kuzari. Ni yadda ma zuciyarsa zata manta da shi kawai nake ji, na lura da irin wannan sha'kuwar ce take sanya mutum ya kwanta ciwo idan an rabu.
Wai saki ni abin ma mamaki yake ba ni, hakika lamarin ya kidima ni.

Wajan shad'aya da rabi anti Yagana ta dawo a gajiye ta zauna a falo. Na zuba mata ido tausayinta na ji yana tsirga mini duk wannan fad'in tashin akaina take yi da kud'inta da ga'bobinta.
K'walla ta ciko kwarmin idona amma ban yarda ta zuba ba na yi c
'kok'arin mayar da ita Ina kallonta tana fito da kayan dake cikin jakarta ta ce." Ina hanya sai ga wayar Babanmu wallahi lokacin da ya kira ba ki ga yadda hankalina ya tashi ba domin na yi tunanin mijinki ne ya gaya masa abinda yake faruwa, wai ashe Hadiza ce za ta tafi dubai saro kaya shine ya ce wai na kira ta na yi mata magana domin shi fa idan da yawunsa ne bai amince a bar 'kasa da zummar neman kudi ba."

Cike da mamaki na ce." Dubai uban me zata saro a can din, a ina kuma ta ga jarin da har za ta yi visa ta d'unkule kudi ta tafi wata kasa."

Girzgiza kanta ta yi da takaici mai yawa a tare da ita ta ce." Ni ma tambayar da na yi masa kenan ya ce shi ma bai sani ba amma ya fara zargin mijinki ne ya bata domin Ummansu Saminu ta ji su suna maganar watarana bayan ta dawo daga unguwa suna d'aki ba su san ta shigo gidan ba. Bayan miliyan shidan da ta yi k'arya da rashin lafiyar Fati ta kuma tambayarsa kudi."

Takaici da b'akinciki ya hana ni cewa komai. Har da hadi'n gwiwar hadiza wajan ko'karin wulakani da mutumin nan yake yi.
Anti Yagana ta cigaba da cewa." Kwanaki da na yi mata magana akan me yasa suka shirya karyar ciwo don su kar'bi kudi wallahi ba ki ga rashin kunyar da ta yi mini ba, shiyasa ai na cewa Baban namu ba zan iya cewa komai ba akan Hadiza ba domin tana samun d'aurin gindin uwarta ne."
Zuciyata na zafi na ce." Anti Yagana yanzu dan Allah wannan shine daidai ne, Hadiza fa ta wulakanta ni a wurin mutumin nan, ta zubar mini da mutunci, me yasa ba zai nuna ni ba komai ba ce, ya san ba ma shiri har da sakamakon saki mai zai sanya ya tura mata kudi."
"Ni kaina raina ya 'baci to babu wata dama ta gyarawa ya riga ya faru kuma kin ce mini shine ya bata damar yin hakan baki da hujjar yin wata magana kud'insa ne."
Hawayen dai da nake dannewa suka zubo a kumatuna na ce." Amma dai ai bai dace ba, fad'a fa muke yi me yasa zai tura mata kudi, yadda yake jin haushina akan lefin da bashi da tabbas ya kamata ace ya k'yamaci duk abinda ya shafe ni."
Murmushi ta yi tana cewa." Wani sa'in fa maza sun fi mata kaidi Amina, ba ta yadda za a yi fa ki fito a yanzu ki nuna wannan bawan Allah ba ya kyauta miki mutane su yarda da maganarki, yana amfani da dukiyarsa ne wajan sayan al'umma bisa la'akari da yadda rabin mutane suka zama makwadaita. Babanmu da sauran 'yan uwansa ba zasu ta'ba yarda da maganarki ba wallahi. Ban 'ki ba Baban Sauden ni kaina yanzu na fara hasashen halayensa marasa kyau da yake b'oyewa mu kuma yana bayyana mana masu kyawu amma idan ba haka ba me zai sanya ya san da wannan rikicin a tsakaninku ya d'auki kudi masu yawa ya bawa 'yar uwarki, ya shirya kai ki kasa ne koda maganar ta fasu babu wanda zai aminta dake "

Hannu nasa na goge ragowar hawayen da yake fita daga idona yayin da nake jin wani irin zugi a kasan zuciyata. Mutumin nan karshen munafiki ne.
Ta ce." Kin ga ba wai naki yarda da abinda Allah ya kaddara ba ne, amma kin san istahara gaskiya ce Amina, an bincika mini sosai lamarin nan akwai sa hannu tunda ai farkon auranku ba haka yake ba, tunaninsa a rikitar ana so ma adasa masa kiyayyarki da zarginki a cikin zuciyarsa. Yanzu haka ma malamin ya ce mini yana can hankalinsa a tashe domin lokacin da ya yi sakin a tunzure yake k'wa'kwalwarsa tana ta gaya masa karya da gaskiya yanzu kuma da ya dawo nutsuwarsa ya fara nadama."

Murmushin takaici na yi na ce." Anti Yagana duk wata istahara ta bi bayan wadda kai za ka yi da kanka, idan kin ce akwai asiri ko farraku a tsakaninmu ba zan musanta miki ba, amma ban yarda da cewa yana can hankalinsa a tashe ba me yasa bai kira waya ba."
Ta ce.'' Ai yanzu akwai turaran da za ki yi wanda dolensa ya neme ki kafin nan kafi faduwar rana haka malamin ya ce."
Chapter 11 · 0% Book details