Sashe 21
Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read
"Ita Ummansu Hadiza tana d'auka yadda take bin malamai kowa ma haka yake, kin san mai yin abu sai ya dinga zaton wani ma yana yi, ai na gaya miki Sahura wallahi ban ta'ba tsugunawa agaban wani da zummar ya taimaka mini akan mutumin nan ba, kin fi kowa sanin halina. Anti Yagana ce ma da taga abin ya rincabe ta fara biye biye na ce mata ba na so, duk abinda ya tunkaro bawa kawai ya nemi sau'ki a wajan Allah."
"Wannan shine gaskiya 'kawata domin babu wani abu da wani mahaluki zai yi maka face ya kara jefaka a masifa, kuma na ji labarin ma an ce Hadizan bata kasar wai ta tafi dubai saro kaya." Ta kare maganar tana dariya.
Na ce." Ni ma haka na ji Sahura na ce me Hadiza take so ta zama ne, ai mutumin nawa shi ta kira ya bata jarin kudi zaman da ta yi a wajena ta samu kofa a gabana ya ce mata duk lokacin da wata buk'ata ta tashi ta nemeshi. Wallahi Sahura ashe had'a baki suka yi da Ummansu suka shirya karya ciwo ga Fati wai tana da cancer za a yi mata aiki, duk suka daga mana hankali ni dashi a lokacin ya ba su miliyan shida ya kuma bata kofar tambayarsa duk abinda suke so shi ya d'auka da gaske ne sai da anti Yagana ta bincika ta tabbatar da cewa k'arya suke yi. Kuma maganar fa da nake yi miki lokacin da ya tura mata kudin zuwa Dubai din rikici muke yi don har ya yi sakin ma, bai gaya mini ba itama Hadizan ba ta gaya mini ba sai da Babanmu ya kira anti Yagana yana gaya mata.
Girgiza kanta ta yi tare da cewa." Amina Hadiza 'yar uwarki ce, duk inda aka je aka dawo babu wanda ya isa ya raba tsakaninku tunda uba daya ba wasa ba ne, amma wallahi ki yi hankali da ita dan ta gurgud'e miki auren nan ba wani abu ba ne a wurinta, nasan ta fi ni kusanci dake amma kin san wani abu da ban gaya miki ba tun lokacin da abin nan ya faru da aka dinga yawo da sunanki a social media cewa kin ce ke ma a baki hakkin yaranki da Yallabai ya take, na dinga bibiyar lamarin wallahi har acct din da ya fitar da magana na dinga bibiya na kwafo lambar da aka bude acct din na ajiye, wallahi Koda na tsananta bincike akai sai na gano lambar Hadiza ce amma ba kowa ya san tana da ita ba, kuma yanzu ki shiga fece book ki yi sarcin din acct din za ki ga babu shi ta goge, dama ta bud'e ne domin ta 'bata ki."
Da mamaki mai yawa a tare da ni na ce." Anya kuwa Sahura Hadiza fa bata da wani boko akanta ina ganin azancinta ba zai iya b'ata damar bude fece book ba har ta yi wannan rubutun."
"Itace fa na gaya miki, idan ba ta iya ba zata iya biyan kudi a bude mata ta yi amfani dashi a lokacin wanda ya bude mata ya goge shi gabad'aya."
Na ce." To idan na fahimta ta yi amfani da boyayyiyar lambata ne don kada a gane ita ce, tunda ai ina da lambata ko a fece book din ma ina ganin gilmarwarta."
"Shine ai abinda na gaya miki da wata wayar ta yi amfani amma da an tabbatar mini da cewa layinta ne kuma tana amfani dashi sa'i da lokaci."
Dariya na yi na ce." Lallai Hadiza abin har ya kai haka, to Allah Ya kyauta ke kuma Sahura sannuki da k'okari, na rantse miki da Allah ban ta'ba kawowa zuciyata ita ce ba."
Ta ce." Ke dai Allah Ya kyauta a wannan zamanin duk mutumin da Allah Ya rufawa asiri ai yana ganin hassada da bita da kulli na mutane."
Wayata na d'auka na duba lokaci sha biyu saura na ce." Sahura kinga sha biyu har ta kusa muna luguden lebe." Na kwalawa Salima kira dake can tana aiki, ta shigo na ce." Kawo mana shayin nasan kin gama dashi."
Ta ce." E Mama abincin ma na kusa."
Na ce." Sannunki diyar albarka ranar bikinki ban san wane shagali zamu sha ba."
Uwar ta fashe da dariya tana kallonta ta ce." 'Kugu za ki daure da gyalenki ki shiga filin rawa kawai Hajiya."
Ina dariya na ce." Sai kin fad'a ma, ai rawa zan yi hadda juyi."
Gabad'aya muka fashe da dariya. Yarinyar ta yi saurin fita tana sinne kai.
Ta dube ni tana cewa." Kin san fa wani yaro dan gidan yayar babanta yana nan yana naci a kanta wai ya kama don Allah kada a bawa kowa shine fa uban ya zo yana gaya mini na ce to guda nawa Yusuran take da har za a fara wannan maganar shekara sha hud'u fa kawai don an ganta da tsayi shi yasa ake bata girma."
Na ce.'' Ai girman 'ya mace ba wahala Sahura Kuma ta isa fa, ai tana da san girma, amma dai da Idiris zai d'auki shawarata da na ce masa kada ya yi mata auran nan na gaggawa ya bari ta damu koda diploma ce."
Ta ce." Ya bari kuwa, ai shi idan magana ta 'yan uwansa ce baya wasa da ita, ni ma nafiso ta dan yi karatu ko yaya ne zai taimaketa anan gaba."
Na ce." Gaskiya hakan zai fi dacewa." Wayata na d'auka na kira Hamusu yana d'agawa na ce." Kana asibitin ne?"
Ya ce." E, anti Amina jikin Gwaggon kam alhmdullhi."
Na ce." To haka ake so, ko za ka zo ka d'aukar muku abinci gashi nan Yusura ta kusa kammalawa kafin mu zo din."
Ya ce." Ai yanzu nan ma Baba Zulai kanwar Babanmu suka zo da abinci dama kullum tana zuwa sai dare take tafiya wani lokacin ma da safe kafin na je ta riga ni, tunda sun hana kwana."
Na ce." To shikkenan Hamusu ka gaishe mini da Gwaggon da ita inna Zulai din kafin mu k'araso."
"In sha Allahu rabbi anti." Yafad'a cikin kulawa da girmamawa.