← Book details Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 33

Sashe 20

Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

"Wace irin rigima kuma sis, ba na son fa sharri mutumin nan na ji labari fa an ce goyaki ne kawai baya yi kuma ba ke ki ke yi masa ladabi shine yake yi miki, har cewa aka yi kin mallaka shi da mahaifiyarsa sai abinda ki ka ce musu a gidan."
Tana dariya ta kai k'arshen maganarta da zolaya.
[9/4, 11:40 AM] Aunty B: 73
"Sahura duk wanda ya gaya miki haka ya zalince ni wallahi domin kuwa ni kadai nasan da wanda nake zaune, ba zan iya 'boye miki abinda yake faruwa ba sis, amma wallahi kallon kitse kuke yi rogo, da yawa mutane za su dinga ganin ai kakata ta yanke sa'ka saboda mafiakasari mutane sun amince da cewa kudi sune jin dad'i alhalin ba haka ba ne, na yarda da maganar nan da hausa ke fadi cewa ka auri mai zuciya ba mai dukiya ba, mutumin nan yana da tarin matsaloli wad'anda ya bi ya ninke abinsa ba wanda zai gansu sai wanda zama ya had'a mussaman ni dai da nake a matsayin matarsa. Akwai ci dasha kula da lafiya da biyan buk'ata ta aure duk akwai wannan to amma kin san wad'annan abubuwan da na zayyano miki idan babu kwanciyar hankali ba za su yi tasiri ba. Idan zan zaga kaf garin nan Ina sukar mutumin nan babu wanda zai yarda da maganata domin ya riga ya siye jama'a da alherinsa."
"Sis ki gaya mini abinda yake faruwa don wallahi ni gabad'aya kin kashe mini jiki, don Allah ki yi hakuri ki zauna a d'akinki."
Murmushi na yi Ina dubanta, itama magiya take yi mini na ha'kura na zauna ko bata fad'a ba na san dalilinta bai wuce irin na Anti Yagana ba.
Na ce." Sahura zaman bashi ne a wahala ba, abokin zaman shine matsala, ni idan ta ni ne wallahi ba ni da matsala dashi amma fa zan gaya miki abinda ba ki sani ba ya sake ni akan wani abu da yake hasashe kuma bashi da hujja akai."
Cikin kad'uwa da tashin hankali ta furta." Saki kamar yaya k'awata, yanzu kina so ki gaya mini cewa babu aure a tsakaninku?"
"Ya sake ni shekaran jiya saboda yana zargina. Duk na kwashe abubuwan da suke faruwa na gaya mata. Jikinta ya yi bala'in mutuwa har da 'yar k'walla a kwarmin idonta ta ce." Wato ita dai 'ya mace rayuwarta ta kan kasance cikin 'kalubale akoyaushe duk abinda ta yi ba zata tsira ba, sis na ga dai harkar social media nan da ki ka yi neman na kanki ki ka yi baki taba aikata wani abin assha ba wanda zai zama tambari na zubewar mutuncinki. Kuma mutumin nan ba yaro ba ne a ganina bai kamata ace yana yi miki munanan zargi irin wannan ba, wallahi a wannan zamanin sis da wasu 'yan matan har gwara zawarawa ban ce duka 'yan matan lalatattu ba ne, amma wasu mazan na yanzu sun gane gwara su auri bazawarar sun san ita suka aura akan su kashe kudi wurin auran budurwa daga baya su gane ba kamila ba ce, kuma mata nawa manzon Allah s.a.w ya aura a matsayin bazawara, ko wannan ya kamata a ce wasu mazan na d'agawa mata kafa. Amma abinda na fi fahimta ga mutumin nan yana da zafin kishi wanda dama haka aka ce na maza ya fi na mata, kuma idan ya yun'kuro masa yakan iya kasa sarrafa kansa, amma ai kishi ba hauka ba ne, zai lalata auransa ne kawai bai sani ba, a wannan ga'bar gaskiya ba na tare dashi."
Na ce." To kin fahimce ni ashe, Sahura a shirye nake akan wannan dalilin wallahi na tsinke auran nan, ban yi abu tunda kuruciya ba akan me yanzu zan yi, har wanda yake aurena ya gaza fahimtata, koyaushe addu'a nake yi Allah ya kare mu daga rudin zamani. Shekaran jiya ya yi sakin jiya da safe ya ce ya mayar da ni. Ai aure ba abin wasa ba ne, ko 'yar tsana ba za a yi mata wannan wulakancin ba, Sahura dole ne na nuna masa nasan abinda nake yi."
" 'Kawata ina bayanki, amma don Allah kada ki zafafa da yawa nasan halinki, ki dubi shekaru da kuma matsayinsa da wad'anda suke k'asansa, dan fa kuskure ya yi kuskure gaskiya."
Na ce." Shi me yasa bai duba shekaru da matsayinsa ba, ai gudun zubewar mutunci yake yi a gari to idan bai yi wasa ba sabuwar jarida zata fita a kansa."
"A a 'kawata kada ki yi abinda duniya zata san me kuke ciki, ki sakaya auranku don Allah, shi dai sannu a hankali ki hukuntashi amma kada ki fitar da sirrinku, ai dan Adam tara yake bai cika goma ba, bai kyauta miki ba amma ki dubi abubuwan alherinsa a gareki ki rangwanta masa.
'Kwafa na yi tare da cewa." Mu bar maganar nan Sahura ta ishe ni wallahi, yanzu ashe yawo ake yi da ni a gari ana cewa juya shi nake yi, mutane basa tsoron Allah."
'Yar dariya ta yi tana fad'in." Wallahi cikin unguwarmu na ji maganar tana yawo, kuma daga gidanku ta fito Ummansu Hadiza ce take gayawa ma'kota ai kin shiga kin fita akansa da Mamansa sai yadda ki ka yi dasu, Hadiza da ta zauna a gidan ta ga irin zaman da ku ke yi.
Chapter 20 · 0% Book details