Sashe 3
Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Ban iya rintsawa ba a daran ranar raba dare na yi ina duba comments din mutane dangane da abinda yake faruwa wasu sai zagina suke yi suna fad'in dama ba ni da kunya sannan kuma butulu ci na yi masa ban kuma san alheri ba. Tsirarun wad'anda suke goyon bayansa sune suke fad'in wannan maganganun. Amma dai masu zaginsa sun fi rinjaye.
A daran dai na shiga fege dina na fece book din a karo na biyu zan sake yin rubutu akansa wannan karon rubutuna yana d'auke da sa'kon godiya da yabawa, jinjinawa da sadaukarwa a gare shi, na kuma fito na gayawa duniya cewa babu yawuna dangane da rubutun da yake ta yawo a kafar sadarwa asalima ban san me pege din ba, na rufe da yi masa kyawawan addu'oi tare da samun cigaba da d'aukaka da kuma gamawa da duniya lafiya.
Washe gari da safe ban fita da wuri ba sai wajan takwas da rabi. Hajja kawai na samu a falo ita kad'ai.
A nutse na kàrasa wajan da take na tsuguna na gaisheta kamar koyaushe ta amsa tana d'an bina da kallo, matar tana da saurin fahimtar mutum ko yaya ta ga can ji a tare dani sai ta nemi ba'a si, a nutse ta ce." Zo zauna kusa da ni, na ji me yake faruwa Amina wannan kumburin na Idonki ba na lafiya ba ne."
Na zauna gefanta ina dan murmushi wanda sam babu nishadi a cikinkisa.
Ta ce." Menene yake faruwa?
Cikin rauni da damuwa na ce." Wallahi Hajja wani abu ne ya faru wanda bai yi mini dadi ba ko kad'an, wani rubutu ne ya fita da sunana a ciki wai ina neman hakkin yarana a hannun maigidan nan, mai rubutun kuma yana jadaddawa duniya cewa da yawuna ya fito yake sanarwa mutane."
Ta ce." Assha to shine ai me kuma? Idan ma kin fito kin yi magana ai ba lefi ba ne, abinda dai nake so na fahimta shine dama Babansu Yusi din ya yi aiki a karkashin Tajo ko kuwa?"
Na goge hawayen da ya dan zubo mini na ce." E, ya yi aiki dashi kafin rasuwarsa."
Sai ta girgiza kanta cikin alhini ta ce." Allah Ya gafarta masa, ki samu nutsuwa kuma ki daina damuwa da hakan in sha Allah babu abinda zai faru."
Na ce." Na gode Hajja Allah ya kara girma." Ta dafa kafadata tana cewa." Ina ganin umarar nan tare zamuje ki d'an samu nutsuwa ki kuma yi addu'oi, Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu."
Na kalleta hawayen da nake ta dannewa suka fara zuba, na rasa wane irin so da k'auna baiwar Allah nan take yi mini, tana gudun b'acin raina sosai, tana kuma so koyaushe ta gan ni, cikin farinciki da walwala. Na ce." To shikkenan Hajja sai mu tafi taren in sha Allahu."
Hauwa ce take saukowa daga bene tana sanye da kanun kaya amma ta dora after dressing akai ta yi kwalliya sosai a fuskarta kuma ta yi kyau daidai gwargwado.
Ta iso wajan da muke zaune ni da Hajja ta zauna saman kujera tana fad'in." Hajja Ina kwana an tashi lafiya?"
Ta amsa da "Lafiya lau tana dan dubanta."
Ta d'an kalleni kafin ta ce." Ina kwana." Na amsa babu yabo babu fallasa."
Hajja ta ce." Tajo bai tashi ba ne?"
Babu kunya balle tsoron Allah ta ce." Bai tashi ba jiya bai kwanta da wuri ba."
Hajja ta yi shiru tare da kawar da kanta gefe. Ni kam maganar ta dan dake ni sai nake ganin kamar da gayya ta fad'eta."
Tashi na yi na nufi wajan cin abinci ina fadin." Hajja kin karya ne?"
Sai ta ce." Kin manta yau litinin ina Azimi."
Na ce." Wallahi na manta, Ina gyara kujerun wajan na dubeta." Hauwa ki zo mu karya."
Ta d'an yatsune baki tana cewa." Ina ga sai an jima ba na karyawa da wuri."
"Okey kawai na ce na gyara kujera na zauna a nutse na dan d'ibi abinda zan iya ci na hada tea na fara sha domin ya d'umama mini cikina.
Saukowarsa ta d'auki hankalinmu gabad'aya duk muka zuba masa ido yanayinsa kawai nake kallo kamar ba shi wanda ya shiga damuwa mai tsanani jiya ba. Ban d'auka zai wayi gari da karsashi irin haka ba. Kwalliya ma ya sheka sosai cikin wani irin yadi irin na manya babbar riga da yar ciki da uban aiki a gaban rigar. Tun kafin ya k'araso wajan da muke kuwa kamshinsa ya karad'e mu.
Ya risina yana gaishe da Hajja ta amsa tana cewa." Ban jima da tambayar Hauwa ba ta ce wa ai baka tashi ba."
Yana dan gyara agogon hannunsa ya furta." Eh yau na dan so na makara ne wallahi, ina da baki a waje zan fita wurinsu yanzu za mu interview."
Ta ce." To babu damuwa." Ya nufi hanyar fita bai dube ni ba. Abin ya sosa mini rai 'kwarai da gaske amma ban kawo komai ba illa iyaka azijanci irin na d'an adam, domin yadda ya sauko a gurguje wata'kila bakin masu muhimmanci ne. Ni kadai nake wannan hasashen a cikin raina. Ko minti biyar bai yi da fita ba Hauwa ta tashi ta haye sama ta bar mu a wajan ni da Hajja.
'Danjaridar ya ce.
"Da farko Allah ya taimake ka muna so mu ji daga bakinka dangane da jita jitar da take yawo a gari mussaman a kafafan sadarwa, inda kowa yake tofa albarkacin da yake bakinsa dangane da mutuwar wani ma'aikacinka da iyalinsa suka fito suna kuka akan cewa ka yi amfani da lafiya da kuruciyarsa a lokacin da yake raye domin neman dukiya karshe ajalinsa ya sauka a karkashin aikinka, ba ka je ka yi wa iyaye da iyalinsa ta'aziya ba, sannan kuma babu ihsani a tsakani, mutane da dama suna zarginka akan son zuciya da ko'karin tara dukiya domin ka gina kanka."
'Dan jaridar ya nisa kafin ya cigaba da cewa." To ana cikin wannan turka-turka a gari da sauran kafafan sadawarsa sai ga wata majiya mai toshe ta yi sanarwa kan cewa Matarka ta yanzu wadda a can baya ta ta'ba auran wani Aminu Salihi wanda ya kowa ya shaida cewa ya wahalta maka k'warai da gaske dalilin lalurarsa yana da ala'ka da abinda ya shafeka, ya kwanta jiyya ba ka duba shi ba, ba kuma ka aika wakili ba, ya fadi ya mutu ba ka je ta'aziya ba sannan ba ka yi ihsani ga iyalinsa ba. Wannan dalilin ya sanya itama matarka ta yanzu ta fito take nemawa yaranta hakkinsu a wurinka, Allah Ya k'ara lafiya ko za a yi mana karin bayani dangane da zargin da jama'a da masu hakki suke yi maka.