← Book details Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 33

Sashe 29

Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 3 min read

To ashe da ya fita daga nan mutumin nan wurin Babanmu ya je. Ban san abinda ya gaya masa ba, ni wajejen tara da rabi gama wayarmu da Sahura da kadan Babanmu ya kira ni ya rufe ni da fad'a har muryarsa tana rawa yana fad'in idan na janyo masa zagi a gari sai ya yi mini Allah ya isa tunda hakki na uba ya sauke mini amma ina nema lallai sai na guji aure na yi zaman kaina, muddin wannan hanyar zan bi to zai zare hannunsa daga kaina.
Ban yarda na yi jayayya dashi ba na dinga bashi ha'kuri har sai da ya huci na kuma yi masa alkawarin bin umarinsa.
Na jima ina jajanta lamarin yadda babanmu ya hasala yana nema ya yi mini baki shine abinda ya fi daure mini kai, Ina ganin da ya tsaya mun gama magana a tsakanimu zai fi ba wai ya yi yun'kurin had'a ni mahaifina ba.
Ba ni da lokacin tambayarsa akan dalilin da ya sanya ya yi mini haka hujjarsa kawai bukatarsa ta biya ta kowace hanya bai yarda da abinda ya aikata zai bata mini rai ba.
Da takaicin hakan na kwana a raina don har na yanke shawarar kiransa a waya na tambayi jikinsa amma hakan da ya yi mini yasa na share shi ban neme shi ba.
Da safe ya kira waya na d'auka muka gaisa ya fara tambaya ina maganarmu ta kwana. Na nuna masa ban san maganar da yake nufi ba.
Ya ce." Maganar barin ki daga wannan gidan naki." Na ce." Yadda ka ce haka za a yi."
Ina ji ya sauke ajiyar zuciya tabbacin maganata ta faranta masa ya furta." Zan zo da daddare saboda gudun idanun jama'a, kamar yadda na fad'a sai mu je ki za'bi gidan da za ki tare."
A takaice na ce." Sai ka zo?"
Ya ce." Na gayawa Hajja tare muke dake kina can gidanku idan na zo sai mu je can ku gaisa ko?"
"To, kawai na ce masa.
Na kasa daurewa dai na furta." Na gaya maka duk irin abinda za mu yi ni da kai ka daina had'a ni da mahaifina menene ribarka ta yin hakan, ai ni ba na gayawa mahaifiyarka abinda zai daga mata hankali."
"Ni ma na gaya masa ne domin na rasa yadda zan yi dake, nasan shi kadai ne zai tursasaki ki bi umarina tunda ni kin raina ni, Amina ai ba zalinci a zamantakewar auranmu, to ni ma don Allah kada ki zalince ni, sakin da na yi miki kuskure ne da zafin kishi ba zan boye miki ba ina mutukar sonki wallahi akwai kuma wani bakin kishi da yake damuna akanki idan ya motsa mini ni kaina tsanar kaina nake yi balle wanda zai kusance ni. Maganar nan ta mutu haka kada wanda ya ji, in sha Allahu hakan ba zata sake faruwa muddin kin kiyaye faruwar hakan anan gaba.
Maganganunsa suka kashe mini jiki, tabbas kowane dan adam yana da dabi'a, kuma yana kuskure babu wanda ya cika cif kuma ha'kuri a rayuwar duniya ya zama dole mussaman a zama na aure.
Dukda namiji ba a cika yarda dashi dari bisa dari ba, amma a wannan karon na dan ji tausayinsa kad'an kuma kalamansa sun yi tasiri a gangar jikina ya gaji zaman lafiya yake nema.

Sahura duk da ba mu rabu da annashuwa ba jiya sai da ta turo mini mai k'unshin da kwatance ta zo har gidan tunda bashi da wahala a bakin titi yake.
Yarinyar ta iya kunshi sosai ta yi mini kafafu da hannuwa ja da baki wanda rabona da lallai tun na haihuwar baby Khadija. Sosai na fito kamar wata amarya na bata dubu goma Yusura ta je ta rakata bakin titi.
Chapter 29 · 0% Book details