Sashe 13
Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Tsakaninsa da Allah yake gaya mini babu wasa a cikin maganar. Ganin haka ya sanya ni ma na shiga nutsuwata na ce." Aikuwa ban san kana buk'ata ba wallahi tabbas watannin baya na ji yana maganar da wad'anda Allah Ya sa suna da rabo, amma in sha Allahu kuwa zan yi masa maganar idan na koma duk yadda muka yi dashi sai na sanar da kai."
Da farinciki mai yawa ya fara godiya har da kirari kamar wani maroki na dinga dariya ina zolayarsa da cewa sharad'in idan na yi masa hanya ya samu babu shi ba kara aure fad'i yake yi." Na yarda ai tuntuni na gaya mini Yagana ta rufe kofar kece ba ki yarda ba."
[8/29, 5:24 PM] Aunty B: 69
Dariya kawai na yi domin nasan yana fad'a ne kawai amma ba har zuciya ba, babu wani namiji da zai so ya rayu ya mutu da mace daya yawancinsu suna ha'kura ne saboda wasu dalilai amma an riga an hallicesu da son mata wannan a jininsu yake akwai ma mazan da suke da tarangahuma sun yarda su tara matan duk abinda ma zai faru sai dai ya faru. To wad'annan sune za mu kira da masu rashin tsinkaye da hangen nesa.
gajiya na yi da tunani na tashi na je na kwanta wanda bacci da k'yar ya d'auke ni. Misalin shida da rabi wayar Hamusu ta tashe ni daga b'ingirewar da na yi bayan sallar asubahi
Muka gaisa sosai dalili mun kwana biyu ba mu gaisa ba kamar yasan maigidan yana adawa da hakan a tsukin ya rage kira na a waya sai dai ya turo mini da voice note ta whasap. Ni ma sai na fi jin dadin hakan. Nan yake gaya mini Gwaggo ce bata da lafiya dalilin da ya sanya ya kira ni domin jikin nata ya fara tsanani.
Cikin kankanin lokaci na ji hawaye ya cika kwarmin idona. Gabad'aya sai na diririce hankalina ya tashi sosai, na ce." Hamusu ina nan maiduguri na zo bikin yaran d'an'uwan Dada, ita Gwaggwon za ta san shi tunda tare suka taso. Amma zan yi kokarin d'auko hanya gobe yadda kake fad'in jikin nata hankalina ya tashi sosai wallahi, ina fatan kun kai ta asibiti.
Ya ce." Kiran da na yi miki kenan, domin babban asibiti nake so mu kaita su bata gado sugar ne da hawan jini, mun je asibitin murtala likita ya dubata ya rubuto magani an Siya kwana biyu an samu sau'ki wallahi jiya kuma sai ta tashi bata iya motsa komai a jikinta, kuma ba damar na yi amfani da kudinki ban gaya miki ba "
Raina ne ya baci jin abinda yake fada. Na ce." Hamusu wannan wace irin magana ce, ashe akwai ranar da za ka iya nuna mini cewa Gwaggwo ba ta haife ni ba, kudin nawa wanene yake juya mini Ina ce kaine jigo har sai ka tambaye don za ka kai Gwaggwo asibiti wallahi baka taba ba ni haushi ba irin yau."
Ya ce." Ki yi hakuri anti Amina ta wani gefan fa Ina da gaskiya, kudi suna iya shiga tsakanin kowa shiyasa sanarwar take da amfani."
Na ce." Ka ga malam maganar ta isheni haka don Allah, ka je daga dubu daya zuwa dubu dari biyar har abinda ya yi sama na amince muddin akan gwaggo ne. Sai ya fara godiya ban jira na saurari sauran maganar ba na datse kiran na fita falo.
Anti Yagana tana kicin tana aikin karin kummalo Fadila tana taimaka mata
Yusi da sauran yaran sun fito bakin famfo suna ta burush da wasa da ruwa.
Na dan jingina a jikin bango a sanyaye na ce." Anti Yagana mun tashi lafiya ya hidima?"
Ta amsa hankalinta yana kan abinda take yi, na ce.'' Ina ganin gobe asubanci zan yi zuwa kano Gwaggo bata da lafiya yanzu nan Hamusu yake gaya mini jikin nata sai a hankali."
Ina dire maganar da take bakina Yusi ya zo ya tsaya da burush dinsa a hannuna.
Anti Yagana cikin alhini ta ce." Allah sarki Gwaggwo ciwon har ya kai ace bata san wanda yake kanta ba, kenan tana asibiti a kwance."
Na ce." Ina fa, tana gida saboda shashancin Hamsu bai gaya mini ba har sai da ciwon ya ci k'arfinta wai ya kaita asibitin murtala da farko yanzu kuma abin yayi tsanani shine fa ya kira ni yake gaya mini da abin haushi wai yana neman izini zai yi amfani da kudina.
Ta ja tsaki tana fad'in." Wauta da rashin hankali shikkenan don ya d'auki Gwaggwo ya kaita asibiti da kudinki sai ki ce masa don me, ya ba ni haushi wallahi."
" Wallahi ni ma ba ki ji yadda raina ya baci ba wannan ai shiririta ce rashin lafiya ya wuce komai, kuma ko dukiyata zata kare akan nemawa Gwaggwo lafiya anti Yagana wallahi ba zan damu ba"
Ya girgiza kai tana cewa." Kwarai kuwa ai Ido ba mudu ba ya san kima."
"Mama wai Gwaggo ce bata da lafiya?"
Na dube shi ya zuba mini ido da yanayi na damuwa a tare dashi.
Na ce." E, itace amma jikin da sauki alhamdulillahi."
A sanyaye ya ce." Mama idan za ki je zan biki don Allah."
Ya fad'a muryarsa har tana rawa, sai ya ba ni tausayi ni ma na ji idona ya ciko da kwalla dama daurewa kawai nake yi.