Sashe 22
Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
To sai wajejan biyar na yamma muka gama shiri nida Sahura muka fito da zummar tafiya asibitin. Yusura na gidan anan muka barta dama tunda suka zo na cewa uwar ta bar mini ita ba jayayya ta ce dama ai taki ce. Hijabi nasa har kasa na rufe fuskata da nikab saboda ba na so jama'a su gane ni. Tare muka shiga shago da ita na gayawa yaran zan fita amma ba zan jima ba zan dawo, ita Kuma Yusura na ce mata ta rufe gidan daga ciki. A daidaita sahu guda muka d'auka har asibitin Malam. Muna d'an ta'ba hira na ce." Sahura duk abin nan da nake yi wallahi idan na tuna halin da Alhaji Muntari yake ciki sai na ji kasala ta kama ni, haka kawai nake tausayawa masa ki ba ni kwarin gwiwar taimakonsa tunda ke ki ka gaya mini yadda yanayin jikin nasa yake." Ta ce." Sis kina da raguwar zuciya gaskiya, na taimaka miki ta wace siga kenan?" "Idan mun shiga sai mu binciki asibitin bangaran maza ko Allah zai sa mu samu d'akin da yake sai na dubo shi." "Kina da tabbacin yana asibitin har yanzu watanni uku fa na ce miki da suka wuce, wata'kila ma an sallameshi yanzu." Na ce." Sai mu sanya rana ki raka ni na duba shi a gidansa, wallahi har yanzu ina tuna irin alherinsa akan Kamalu ya yi mini kokari sosai akan Yusi lokacin da ya aureni bai bambamta tsakaninsa da yaransa ba." Ta ce." Kina cikin wannan rikicin sis, kada ki rikitowa kanki wani don Allah ki bar maganar nan, idan ki ka yi masa addu'a daga nan ma ya isa ai Allah ya ga zuciyarki." "Babu abinda zai faru Sahura Ubangiji da zuciya yake amfani." Shiru ta yi tana girgiza kanta kamar buk'atata bata damu karbuwa ba a wurinta. To muna shiga asibitin muka fara cin karo da motocinsa tunda komai nasa baya 'buya duk motocinsa akwai alama mai d'auke da ayyukansa na yau da gobe Cikin faduwar gaba na ce." Kada dai mutumin nan ya sauka." Na d'auka a zuciyata nake maganar sai da na ji maganar Sahura tana fad'in." Shine ma ai kin san komai nasa a bayyane yake duk inda yake sai an gane, kuma tunda naga wannan motacin na tabbatar yana cikin asibitin nan." Na ce." Sahura kin ga irin abinda nake gaya miki ko? Matar nan fa mahaifiyar tsohon mijina ce amma ya yi ruwa da tsaki akan lamarinta ni ya hana ni ma aiwatar da komai, don girman Allah ki gaya mini ta yaya za a yarda da abinda zan fada a kansa." Muna cigaba da tafiya ta ce.'' Kin san kuma Yana da tausayi da zuciyar Imani fa, shiyasa ake ta yi masa sha'awar mulki domin ana yi masa kyakykyawan zato da wahala ya samu labari ko ya ga mai neman taimako bai taimaka masa ba, ya yi da jiki da aljihunsa wannan yana daya daga cikin kyawawan halayensa. [9/6, 10:17 AM] Aunty B: 74 Shiru kawai na yi ban ce mata komai ba domin gabad'aya kaina ya kulle da al'amarin nan da yake faruwa. Kiran da ya shigo wayata ya katse nazarin da nake yi. Hamusu ne, cikin nutsuwa na daga wayar nasa a kunnena. Sai da ya fara gaishe ni tukkuna ya furta." Kun shigo asibitin ne anti?" A takaice na ce masa ." Eh, na dora da fadin wai kai baka gajiya da gaisuwa ne Hamusu Ina ce da safe mun gaisa haka ma d'azu dana kira ka sai da ka gaishe ni gaisuwa nawa za mu yi ne a rana." Dariya ya fara yi kafin ya ce." Ai babu lefi anti girmamawa ce, kin cancanci hakan ne." Humm kawai na ce Ina ko'karin kashe wayar ya ce.'' Yallabai ma bai jima da shigowa ba tare da su Yusi suka shigo." Ban yi mamakin jin cewa suna tare ba domin akwai Sukairaju a tsakani. A takaice na furta." To babu lefi muna daf da shigowa ni da Sahura.'' Ban jira amsarsa ba na datse kiran. Ni da Sahura babu wanda ya sake wata magana har muka isa d'akin da Gwaggo take kwance wanda 'yansanda biyu ke tsaye a bakin kofa. Ko ba a fad'a ba nasan masu tsaronsa ne. Muka kàrasa wurin suka nemi su hana mu shiga wai sai ya fito tukkuna. Kawai na tsaya Ina kallonsu dan ban iya furta komai ba Sahura ce take ko'karin nuna musu wani abu Hamusu ne ya fito tare da wani likita suna magana. Ganinmu da sauri ya ce." Yallabai ya haka kuma iyalinsa ce fa, ita kuma wannan kawarta ce." Da sauri wanda yake tsaye a bakin kofar ya gyara yana sunkuyar da kansa ya ce." Madam sorry ban gane ki ba kasancewar kin rufe fuskarki, a yi hakuri." A nutse na ce." Babu komai." Na juya ina sauraran tattaunawar da suka yi da likitan yana fad'in tunda jikin ya yi sau'ki za a iya sallamarta gobe ko jibi ya dube ni yana kara yi mini bayanin yanayin jikin nata, da kulawar da ya kamata a dinga bata da kuma canjin abinci da sauransu. Na ce." In sha Allahu za a kiyaye. Ya yi mana sallama cikin girmamawa da kulawa ba don mun kai ba sai don alfarmar wani wanda duniya ta d'aukaka shi. Hamusu shi ya shige gaba kafin mu bi bayan shi ni da Sahura haka kawai sai na fara jin faduwar gaba kamar wadda ta tunkari ajalinta. Gwaggo na zaune sosai a gefan gado Yusi yana kusa da ita da lemon zaki a hannunsa yana bare mata. Yayin da shi kuma yake hakimce a wata kujera dake d'akin wadda take kallon gadon da Gwaggo take zaune. Da alama hira suke yi yanayin da muka riskesu gabad'aya fuskokinsu sun nuna farinciki da murmushi. Sukairaju da abokin tagwaitakarshi 'Dahuru dama su biyu ne masu take masa baya escort d'insa kenan suna tsaye a kansa. Sai gwiwata ta yi sanyi ganin yadda kaf hankalin Gwaggo yake kansa cikin kulawa suna magana shi ma ya bada hankalinsa kacokan gareta. Muka yi sallama gabad'aya ina kallon Sahura ta nufi wurin da yake da azama. Ni kuwa da sauri na kawar da kaina na nufi Gwaggo da kulawa ina fad'in." Alhamdulillahi Gwaggo jiki ya yi sau'ki ma sha Allah." Yadda na rungumeta itama haka ta rungume ni ta dora hannunta wanda yake da wadatar lafiya a bayana tana fad'in.'' Na ji sauki sosai Amina, na gode muku kwarai da gaske, yadda kuka yi mana Allah Ya sa ku ma yaranku su yi muku, Allah Ya yi albarka." Na dan gyara na zauna gefanta har yanzu ina ri'ke da ita a jikina na ce."Babu komai Gwaggwo, ai na yi wa Hamusu fad'a a lokacin da yake gaya mini, na ce daka yanzu kada ya kara bari sai abu ya yi nisa tukkuna zai gaya mini, ban ji dad'in abinda ya yi ba ko kad'an." Murmushi kawai ta yi bata ce komai ba. Yusi da tun shigowarmu yake ta satar kallona Ina kallonsa yaron kamar yana shakkata a tsorace ya ce." Mama ina yini?" Na dubi shi a tsanake na amsa da "Lafiya lau ya kake?" Da dan murmushi ya ce." Ina nan lau Mama ." Na harareshi da fad'in." Ai na ji labarin shegantakar da ka yi, za mu had'u ne." Dariya ya yi yana sunkuyar da kainsa. Jikina ne gabad'aya ya mutu sakamakon idonsa da ya zuba mini, a jikina na jiki hakan a nutse na dubi wurin da yake muka had'a ido fuskarsa babu yabo babu fallasa yake ta kallona. Sahura ta iso wurin da muke da wani irin yanayi a tare da ita, ba ita kadai ba ma na lura duk wanda yake d'akin bai ji dadin abinda na yi ba, shi ma Hamusu duk ya yi tsumu-tsumu sai ya'ke ya ke yi. Cikin nutsuwa na dube tare da cewa." Yallabai barka da yamma." Bai yi nauwar amsawa ba ya ce." Barkanmu dai mun same ku lafiya." Na amsa da "Lafiya lau." Da wahala dama ya nuna akwai 'baraka a tsakaninmu bai iya nunawa a bainar jama'a ba zan yi masa wannan shedar ya iya taku. Bayan amsawarsa ma sai ya biyo ni da kyataccen murmushi. Na yi saurin dauke kaina gabana na cigaba da bugawa. Ni kaina na san Allah Ya jarrabe ni shi, domin ko Yaya Aminu karyar so nake yi masa. wannan mutumin ya riga da ya gama sace zuciyata. Inda Allah Ya taimaka ni ban ta'ba nuna masa tsananin so ballantana ya rike hakan a matsayin makamin da zai ya'ke ni. Gyaran murya ya yi gabad'aya muka dubi wurin da yake. Ya tashi tsaye a nutse ya nufo inda muke hakan ya ba ni damar kare masa kallo, sai na ga ma ya kara ki'ba a cikin 'yan kwanakin nan da ba mu yi a tare ba. Na janye idona daga kansa Ina tunanin wanda yake cikin matsala ne zai murmure irin haka, rayuwarsa kawai yake yi ta jin dad'i tunda ai ba ke kadai ba ce da wata kawai yana yaudarar mutane ne. Hasashen zuciyata ya zauna daram a cikin kwanyata na yarda fa wanda yake tattare da damuwa za a same shi a firgice shi kam ya murje ya kara haske abinsa. Kai na ya tsaya kamshin da yake fita daga jikinsa ya tsananta sakamakon kusantuwarmu sai jikina ya fara neman ya mutu lamarin da nake ta dankwafewa yana yunkoro mini. Kamshin da ya riga ya kama jikinsa shi ma yana taka muhimmiyar rawa wurin galabaitar da ni. Sunkuyar da kaina na yi tsigar jikina ta na motsawa. Ya fara magana da dattako kamar ya cika cikakken mara aibu. "Zan tafi Gwaggwo Ina addu'a da fatan Allah Ya k'ara miki lafiya, in sha Allahu kuma gobe da kaina zan yi wa Hajja jagora domin ta zo ta duba jikin naki." Cikin rawar murya Gwaggwo ta ce." To na gode sosai, Ubangiji Allah Ya saka maka da alheri, abinda ka yi mana Allah Ya ninka maka ranar lahira, Allah Ya sa wannan taimakon ya zama shine matakin shigarka aljanna, kamar dai yadda na gaya maka ga Amina nan ita da yaranta mun baka amana yadda ka dubi yaran nan kaima Allah Ya dubeka, ni dai idan ta ni ce na baka