← Book details Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 33

Sashe 25

Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 9 min read

D'akin ne ya yi shiru tun bayan ajiye maganata bai ce komai ba sai karar saukar ruwan sama da ake ta shekawa. Na dube shi a hankali sai na ga yana rawar d'ari alamun sanyi. Muka had'a ido. Ya ce." Ki ba ni abu na gaya miki ko so ki ke yi na cire na yi tsirara ne sanyi ya dame ni."
Na tashi na zuga akwati na d'auko masa zani da wata irigar irin ta jikina na mik'a masa ya tashi ya fara kicikicin cire kayan da suke jikinsa har yanzu rawar sanyin yake yi.
Ya miko mini zanina Yana fad'in." Ban san yadda zan yi na daura wannan ba, kar'bi abinki wannan ma ta isa. Na kar'ba ina me saurin dauke kaina gabana na bugawa ganin yadda girmansa ya fito sosai domin ba tare da kare jikinsa ba ya cire wandonsa akan idonsa sai na kauce daga wajan da sauri na matsa can gefe tare da sunkuyar da kaina k'asa fargabar wani abu na fara yi.
Ya juyo yana kallona na dai sake kawar da kaina a karo na biyu rigar ta kwanta ajikinsa tunda me hade da cotton da robo ce har ilayau girman nasa yana nan a tsaye na san kuwa da wahala idan ba mu yi rigima ba.
Kulle kofar d'akin kararaf alamun zura sakata shi ya dawo da ni hayyacina ya rufe ya nufo ni a hankali cikin karamin sauti ya ce." Rigar ta yi mini kyau ko?"
Kawai na saki baki ina kallonsa, nasan bashi da alkunya da kawaici a wannan fagen kunya kuwa gaba ya bata ba baya ba, zai iya cewa zai neme ni ga yarinyar mutane akwance a rumfa, bayan haka kuma zahirin gaskiya ni dashi muna ficewa ne daga hayyacinmu Iran muna wannan lamari ihu da nishi da surutai samfur-samfur ba irin wanda ba ma yi.
[9/9, 9:19 AM] Aunty B: 76
Wata wawar runguma ya yi mini wadda ban yi tsammaninta ba a lokacin da ya k'araso wajan da nake tsaye. Gabad'aya muka fad'i a wurin domin kafafuna sun yi sanyi kuma ban tsammaci hakan ba. Sosai ya makale ni a jikinsa yana fitar da wani irin numfashi tare da sansanar sassasan jikina. Ban yarda na kar'bi lamarin ba domin yin hakan a wurina kamar abin kunya ne, na farko har yanzu zuciyata ba ta gama aminta da nadamarsa ba, na biyu kuma ba zan ta'ba yarda wata mu'amula ta shiga tsakaninmu ba yarinyar mutane tana kwance a falo na tabbatar da cewa abinda za mu yi ni dashi sai ya tasheta har ta fahimci wani abu.
Wata'kila ya yi amfani da wannan damar ne domin a ganinsa zan janye abinda na kudira domin sanin wacece ni ta wannan fanin babu kara balle kawaici ni dashi din duk kanwar ja ce ballantana yanzu da muke cike da tsananin buk'atar juna ko bai fad'a ba nasan hakurinsa ne ya kare shiyasa ya canza wata dubarar.
Na tattara dukkanin karfina na 'ban'bare shi daga jikina, domin d'umin jikinsa da yadda yake ta 'bari bai dame ni ba don ban kawo cewa zazzabi ne ya kama shi ba.
Na tashi tsaye ina numfashi gabana na cigaba da buguwa domin ban san kuma abinda zai sake biyo baya ba tunda na fi kowa sanin halinsa.
Ganin ya silale ya kwanta a kasan kafet din ya yi male-male kamar matacce daga wajan da nake tsaye ina jin sautin nishinsa sai jikina ya dan yi sanyi fargaba ta dirar mini dama ya gaya mini ciwo zai iya kama shi dalilin dukan ruwan da ya jima jikinsa bai kar'ba ba.
Na dan matsa kusa dashi a hankali na ce." Tunda ruwan ya tsagaita kuma sha biyu ba ta cika ba ni dai ka tashi ka tafi."
Idonsa da suke lumshe ya bude ya dubeni a hankali ya furta." Ba ki da imani Amina, ban yi tunanin kiyayyar da ki ke yi mini takai haka ba na gode."
Ya mayar da idonsa ya rufe yana sake janyo numfashi sama-sama. Har yanzu bai fara ba ni tausayi ba don sai nake ganin kamar karya yake yi don ya samu kaina ne. Na dan sunkuya kusa da kansa nasa hannuna a wuyansa sai na ji mugun zafi na cire da sauri na dora a saman kansa nan ma ya d'auki zafi kwarai da gaske.
Daga nan na gazgata cewa ba karya yake yi ba. Na dube shi a kwance sanye da rigata kamar wani mara galihu, kamar ba wannan attajiri mutumin nan da duniya take yayin sa ba, kamar ba wannan dattijon mutumin nan da daruruwan jama'a ke ci da aha a karkashinsa ba, kamar ba shine wanda jami'an tsaro ke risina masa ba suke kuma tsaron lafiyarsa. Yau gashi a karamin gida takurarre kwance a kasan kafet a d'akin da babu fanka. Sai na fara dawowa nutsuwata domin zuciyata ta fara yi mini munana tunani akansa wai idan ya mutu daga ni sai a shi a cikin irin wannan yanayin wace amsa zan bawa jama'a da manema labarai.
Na sake rud'ewa a lokacin da na ga yana kokawa da sauro don sai cizonsa suke yi yana bugewa da hannunsa.
Da sauri na riko kansa na dora a cinyata na furta." Sannu ka ga zazzabi ne ya rufe ka, dan tashi na gyara maka katifar sai ka kwanta ka ji."
Ya dan motsa kad'an kafin a hankali ya ce." Ba na so, ai ina ganin lokacin da ki ka tayar da katifar saboda kada na kwanta, na gaya mini ai ni nasan dole sai na yi mura da ciwon kai."
Murya na rawa na ce." To ai ba ni nace ka zo ba balle kace na kira ka ruwan sama ya doke ka asalima ban san za ka zo ba, kuma da ka ga hadari ai sai ka ha'kura."
Shiru ya yi bai ce mini komai ba sai jan hanci yake yi alamun ya toshe!
Na buga na raya ya tashi na kwantar da katifar ya ki tashi. Gashi sauro sai cizonmu yake yi ni da shi dukda akwai haske a d'akin amma bai hana sauron tasiri ba ga sanyi irin na ruwan da aka shara yana ta surarowa.
Na ji hawaye na nema ya k'wace mini domin hankali ya kara tashi a lokacin da na ga jikin nasa baya sau'ki sai gaba yake yi. Ya tattare waje daya yana ta rawar jiki. Na fara kuka cikin damuwa da zullumi na cigaba da rarrashin ya tashi na shimfida katifar ina da zannuwa a cikin akwatina na lullube shi. Ya ce ba zai tashi ba ai da farko ya nemi na bashi zanin na'ki na bashi."
Na sauke kansa dake cinyata da sauri na bude akwati na d'auko zannuwana biyu na zo na rufa masa. Domin na tabbatar da cewa bayan ciwon kan da mura da yake yi a yanzu zai iya wayar gari da zazzabin cizon sauro mai tsanani tunda bai saba ba. Da kaina na dinga buge masa sauron da tafin hannuna wanda duk yasha jininsa. Ni ban damu ma da wanda yake cizona ba. Cikin hawaye da jan hanci na ce." Ko za ka je cikin motarka ka kwanta a ciki tunda nan da sauro."
Cikin halin da yake ciki ya ce.'' Har yanzu dai ba ki yi maraba da ziyarar da na kawo miki ba ko, ki ka sani ma ko mutuwa zan yi sallama na zo yi miki."
Na sake shiga tashin hankali jin abinda ya furta. Ba shakka a wannan lokacin ana tsaka da yin mutuwar fuj'an, don an ce maka mutum ya rasu babu jinya kada ka yi mamaki.
Na karaya sosai da sosai cikin kukan da nake ta dannewa na ce." Ba zaka mutu a gidana ba, wane hali kake so na shiga wasu cewa za su ni ce na kashe ka."
Ya yi shiru bai ce komai ba. Na cigaba da kuka a hankali don ba na so dalilin abinda yake faruwa Yusura ta tashi. Kansa da yake cinyata nake ta shafawa ina ta jijjigashi domin na rasa ma abinda zan yi, ba na ajiyar magani balle na bashi gashi an yi ruwa dare ya tsala ba na tsammanin za a samu masu chamis.
Agogon da yake d'akin na duba sha biyu da arba'in, ruwan ya d'auke tsaf. A hankali na sauke kansa na janyo zannuwan na rufe shi gabad'aya har fuskarsa na tashi zan fita. Na ji ya ce." Ina za ki je?"
Da sauri na ce." Zan duba shago ne idan ba su kwanta ba sai na ce Hamusu ya duba chamis mafi kusa a samo maka magani.
Ya ce." Dawo a bari sai gari ya waye abu daya za ki yi mini na samu bacci."
Na dawo na zauna ina fad'in." Menene?
Ya tashi zaune yana kallona muka zubawa juna ido da gaske ciwo yake domin alamun hakan ya bayyana a fuskarsa.
Ya furta." Ni ban iya mura fa ba, tana galabaitar da ni sosai, ki shimfidar da katifar."
Ban ce komai ba na tashi na yi abinda ya bukata domin ni a wannan ga'bar kokarina kawai na samu bacci ya d'auke shi da safe koma menene sai ya faru.
Ya dube ni a hankali ya ce." Cire hijabin ki kwanta."
Wallahi sai a sannan na tuna da karamin hijabi a wuyana."
Na cire na kwanta kamar dai yadda ya buk'ata, na zuba masa ido ina jiran ganin abinda zai yi a gaba. Ya hayo katifar da zannuwan dana rufe shi kawai naga ya kwanta a saman jikina ya fara gyara zannuwan domin lullube mu.
Jikina ya d'auki zafi sakamakon zafin da jikinsa yake yi, shiru kawai na yi ban ce masa uffan amma shi kansa ya san ba zan iya daukarsa a haka har garin Allah ya waye ba kamar akwai zalinci a ciki.
Cikin d'an karamin sauti a daidai fuskata na ji hucin numfashinsa Yana fad'in. " Zan d'an fi jin sau'kin sanyin da yake damuna, idan kin gaji sai ki maye gurbina."
Cikin d'an jan numfashi na ce." Ban gane na maye gurbinka ba, amma kai ma kasan hakan ba zai yiwu ba ko kana fa da nauyi."
"Duk nauyina ai ban kai ki ba, na ce idan kin gaji ki dawo samana shikkenan ko?"
Shiru na yi. Muka cigaba da sakin numfashi jikinsa ya fara shikawa alamun bacci ya fara d'aukarsa. Daga na motsa zai motsa shi. Na furta." Gaskiya sai dai ni na maye gurbinka da kyar fa nake numfashi wallahi ka fi ni nauyi."
Bai ce komai ba ya Birkita ya kwanta kan katifar yana fad'in." Hau shikkenan ko?'
Na gyara zannuwan na hau yasa hannuwansa biyu ya tallefeni na lullube mana jiki da zannuwan amma basu ratsa mu duka ba.
Chapter 25 · 0% Book details