Sashe 16
Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Ya yi ta kiran wayata ban daga ba, da ya gaji sai ya kira ta yaron nasa, kimanin minti goma suna magana kafin su gama wanda ni lokacin ma na gama da wani direba inda na d'auki shatar mota guda na biya..
Ya k'araso yana tambayar direban yadda muka yi duk ya gaya masa ai na riga na biya ba tare da ya dube ni ba yake gayawa direban tare za mu tafi.
Na dubi direban ina fad'in.'' Ni da na biya ka kudin motar umarnina zaka bi ko nasa."
Cikin ladabi ya d'an risinar da kansa ya ce." Ranki ya dad'e umarninki zan bi, amma yana da kyau mu tafi tare dashi tunda yana tsoronki ne kin san fuskarki da ta maigidanki ba 'boyayyiya ba ce, ni na yi mamakin ma ganinki cikin tashar nan.
Jin haka ya sanya da sauri na bude motar na shiga domin sam ban yi wannan tunanin ba yanzu abin sai ya zama magana da yayatawa kafafen sadarwa.
Na dubi Sukairaju da yake ta ko'karin sanya akwati a bayan mota na dan leka ta tagar motar a nutse na ce." Ka je ka taho da Yusi ina nan ina jiranka."
Yadda ya amsa da sauri shi ya tabbatar mini da cewa bai kawo cewa dabara na shirya masa ba.
Ina ganin ya shiga adaidaita sahu. Na dubi direban da yake jingine a jikin motarsa na ce." Ka shigo mu tafi na gama magana dashi ya koma gobe zai biyo bayana da yarona."
Ya d'an yi jim yana kallona kamar bai yarda ba, na 'bata rai tare da cewa." Ka ga idan ba za ka je zan fito na nemi wata motar menene hakane?"
Ya bude motar ya shiga ya zauna a mazauninsa jikinsa duk babu k'wari haka ya kunna motar wani abokinsa ya zo ya tsaya suka d'an yi magana kafin ya bar wajan shi kuma ya ja motar muka fita daga cikin tashar sai sannan hankalina ya kwanta.
Bayan mun d'auki hanya sosai na kira Hamusu domin jin a ina aka kwana nasan tunda mutumin nan ya yi ruwa da tsaki akan lamarin nan da wahala gwaggo bata kwana asibiti ba. Illai kuwa muna gaisawa ya fara da cewa." Yanzu nan da na fito daga wanka nake shirin kiranki wallahi, jiya wajan goma da rabi na samu kira daga maigidanki ya ce mini mota tana zuwa daga asibitin Malam za ta d'auki Gwaggwo babban likita zai dubata sosai. In takaice miki dai Gwaggo tana can an bata gwado kuma jiki da sauki alhamdulillahi na dawo gida domin na yi wanka, anti Amina ki kara yi mana godiya a wajansa lallai yana abinda ya dace da dukiyarsa wallahi anti Amina d'akin da aka kwantar da Gwaggo daban yake da sauran ita kadai ce ba hayaniya kuma tun jiya da daddaren likitoci suka ta zaryar shigowa dubata."
Jikina ya d'an shika kad'an jin yadda Hamusu yake yi mini bayani kamar ya fashe da kuka sai godiya yake yi. Cikin raina na ce.' Haushinka yake ji Hamusu amma saboda iya taku da neman suna ya dabaibayeka da alherinsa ta inda da wahala ka hangi kuskuransa.
Na ce." Babu damuwa Hamusu ai Gwaggwo ta wuce komai, ni ma gani a kan hanya in sha Allahu daga zarar na sauka zan kira wayarka."
Babanmu na kira na gaya masa ina kan hanya. Na kira Sahura itama na sanar da ita, daga nan sai na fara tunanin inda zan sauka, ba zan iya zuwa gidan Hajja ba gaskiya gidanmu kuma babu spece d'akin da na yi zawarci Ummansu Saminu tana kiwon kaji. Kawai sai na yanke shawarar sauka a gidana na kuntau. Yana kulle har yanzu shagon ne dai ake ta hada hada a cikinsa dama mun yi da Hamusu cewa idan auransa ya tashi zai zauna a ciki gidan to an samu tsaiko ne daga bangaran budurwar da yake nema babanta ya ce sai ta yi karatun likitanci shi kuma ya'ki ya canza wata ya dage sai ita yanzu dai an kai kudi an sa rana shakara uku mun ci shekara daya yanzu saura shekara biyu.
Sake kiransa na yi a karo na biyu na umarce da cewa ya sanya yara su wanke gidan su gyara shi sosai, shekara kusan biyu dole a samu datti. Ya ba ni tabbacin cewa kafin na sauka za a kammala.
Koda muka isa ban fito ba saboda Ina gudun idanun mutane can tsallaken titin da muke na hangi masu sayar da abaya da hijab da nikab na fito da kudi na ce wa direban ya je ya sayo mini nikab.
Ya kawo mini na rufe fuskata sai kwayoyin idona kawai ake gani. Na kira Hamusu na sanar dashi. Minti talatin a tsakani ya k'araso kan sabon babur d'insa da ya saya.
Na fito daga motar Ina yi wa direban sallama shi kuma sai risinawa yake yi. Har na hau babur din na ce da Hamusu ya dakata dubu biyar na sake bashi bayan kudin motarsa dana biya shi tun a tashar garinsu. Ya dinga godiya kamar ya ari baki, har dai Hamusu ya ja babur din ban daina jiyo sautin muryarsa ba.
Mun hau titi sosai ya ce.' anti ina za mu je ne? Gida zan kai ki ki huta ko kuma asibitin zan wuce da ke."
Na ce." Hamusu kai ni asibiti na fara duba jikin Gwaggo hankali ya fi kwanciya."
Yana yar dariya ya furta." Ai fa Gwaggwo jiki alhamdulillahi wallahi yau ta ci abinci sosai, kuma ta d'an ta'ba hira amma dai yanzu da na fito daga asibitin bacci take yi."
Na ce." Fara kaini dai na ga yanayin jikin nata Hamusu."
Ya ce.'' To anti Yusi fa a Ina ki ka baro shi a can wajan su anti Yaganar."
Na ce." Eh can na baro shi Hamusu."
"Àmma na so kin taho dashi anti ko dan Gwaggwon."
Na ce." Ai wata'kila wani satin Anti Yaganar za ta zo nasan kuma tare za ta zo da yaran. Ni kaina tafiyar ai bata shiri ba ce shine dalili."
Na gaya masa haka dan maganar ta mutu.