Sashe 5
Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 10 min read
"Wallahi anti Yagana ba wannan ba ne, nasan ina jin babu dadi a raina amma ya zan yi, bayan Hauwa zai iya auro wasu mu zauna, wulakancin da ya tsiro dashi ne ba zan iya jura ba."
"Amina ki yi hakuri na gaya miki, matsalarki ba ta kai wadda za ki tayar da hankalinki ba, mijinki yana sonki yayin da ya gama d'okin amarya komai zai sake shi, ke dai ki cigaba da kyautata masa kuma ki godewa Allah mahaifiyarsa tana k'aunarki to duk abinda za ki ga ni a wannan lokacin ki daure ba zai dawwama ba."
Shiru kawai na yi Ina jinta, na san ba don komai take kafe ni a gidan ba, sai dan gudun lissafin aure, yadda na san halinta hakan ta san nawa, ina da hakuri amma kuma duk ranar dana furje babu mai iya tankwarani, kuma idan na bar abu na bar shi kenan har abada.
Ta ce. " Kina jina ko Amina." Na ce." Ina jinki Anti Yagana. Sai ta cigaba da cewa." Akwai bikin da za a yi na yar gidan Babanmu Auwalu 'dan autan su Dada zai aurar da yaranshi uku maza biyu mace daya, shine Dada ta ce a sanar miki sabon watan da zamu shiga in sha Allahu."
Na ce." Zan gayawa maigidan, in sha Allah na san dai ba zai hana ba, dama kiran da na yi miki d'azu zan gaya miki za mu je umara ni da Hajja jibi in sha Allahu zamu tafi."
Ta ce." To kin ga kin samu dama sai ki tsananta da addu'a akan komai, dama kuma ita rayuwar duniya haka ta gada yau dad'i gobe kuka, ki godewa Allah kaddararki mai kyau ce."
Na ce." In sha Allah Anti Yagana a gaishe mini dasu Fadila da kyau.
Tunda na yi waya da Anti Yagana na ji sasaauci a cikin raina, na kuma yi kokarin danne abin a cikin zuciyata, domin na tabbatar da cewa Hajja ta fahimci damuwata ran kowa sai ya 'baci har shi maigidan.
Satinmu uku a saudiya ni da Hajja muka dawo. Tun ina can hankalina yake kan Yusi domin kuwa zuciyata gabad'aya bata aminta da matar gidan ba.
Duk yadda nake zaton ganinsa a firgice sai kuma na ga akasin haka lafiya lau na same shi har da 'yar ki'ba ya kara.
Nan na fahimci azancinta kishi da kisan mummuke akaina ne, amma bata ta'ba nunawa akan yaron ba, a wasu lukutan ma idan ya zo ya same mu a falo har jansa da wasa take yi shi ma da yake d'an gari ne anti ya kira kiranta.
Ranar da muka dawo na fahimci ya zama d'an dakinta sosai domin magana daya zai ce mini anti ta yi mini kaza ko ta ba ni abu kaza.
Ban tambaye shi maigidan ba, domin jiya da daddare kafin mu taso mun yi magana ta chart ya ce mini zamu dawo mu iske baya gida zai shiga Kano kuma zai kwana biyu.
Ban nuna damuwata ba domin ban sanya a raina cewa lallai sai ya yi murna da dawowata ba, abinda nake bashi kafin tafiyata yana da wadda take bashi a yau na kuwa tabbatar da cewa baya cikin bu'katuwa. Dama tun kafin tafiyata na cirewa zuciyata da gangar jikina sha'awarsa shiyasa idan za mu had'u ban cika kallonshi ba, wanda a lokacin da muke shiri kallansa kadai kan iya jefa ni a wani yanayi balle hancina ya ji kamshin turaransa da wannan ma yana jan ra'ayina sosai. Raina na cire a kansa ba wai don ba na jin sha'awar ba, tana motsa mini sa'i da lokaci na kan danne ne kawai tunda na kudire wani abu a raina.
Kwanansa biyu kamar yadda ya fad'a ya dawo. Kadaran kadahan muka gaisa da juna kamar wasu abokanan gaba, amma na ji dadi da Hajja bata fahimci akwai wani abu a tsakanina dashi ba.
Yadda bai nemi ba haka ni ma ban neme shi ba duk da nasan dole ne girki ya dawo hannuna ranar kuma ni zan kwana dashi
Kwana biyuna suka tafi a banza Hauwa ta kar'bi nata .
Tsayin sati Hajja ta kara a gidan na mu kafin ta fara haramar tafiya gida, ban so tafiyarta ba amma ta kafe a cewarta dama ba ta yi mini alkawarin zama dindindin ba.
To har dai Hajja ta tattara kayanta ta koma kano gidanta na Danbatta ba fahimci komai ba dalili a tsukin kwanakin ba kasafai yake zama a gida ba da daddare kuma kafin ya shigo ya shige d'aki ta kwanta.
Yau saura kwana shiga bikin da anti Yagana ta gaya mini, kuma har ga Allah Ina son zuwa ko babu komai zan shiga cikin 'yan uwa na yi walwala ko zuciyata za ta yi sanyi.
Ba magana muke yi ba don na lura 'kebe kaina da na yi ya sosa masa zuciya sosai, ya kuma ji ciwon rashin zuwana dakinsa shiru kawai ya yi mini.
Na dinga tunanin hanyar da zan bi domin na gaya masa.
Rashin lafiya 'karya na 'kirkira, na kwanta yini guda ban fito ba. Yusi ya dawo daga islamiyya ya gan ni a kwance ya fara tambayata sai na ce masa kaina ne yake ciwo.
Jikinsa sai ya yi sanyi ya zauna gefena yana yi mini sannu yana ta tattaba wuyana wai na tashi nasha magani, don ya kyaleni na ce masa nasha d'azu da rana .
Ya'ki ya matsa ko'ina ko massalaci bai je ba, tare muka yi magariba da Isha'i a d'aki.
Misalin takwas da rabi aka murda kofar d'akin aka shigo.
Hauwa ce cikin kwaliyya har yanzu dai tana cancarewarta irin na amare.
Mamaki sosai ya kama ni, na tashi zaune Ina kallonta. Yusi kuwa fuskarsa ta fadada da fara'a tun kafin ta k'araso yake fad'in." Anti."
Ta saki fuskarta tana amsawa ta d'an dafa kafad'arsa tana kallona da murmushi a fuskarta take cewa." Amina barka da dare."
" Barka dai na furta a takaice domin ni ba yarinya ba ce balle ta ce zata nuna bariki kar nake kallonta, kuma ba wai ta samu dama ba ne, kawai na kyaleta ne saboda ni ma ina ji da tawa da mijinta ina so ya shiga gonata ne kawai.
Ta ce." Yau tun safe ba ki fito ba, ban kuma ji motsin Yusi ba dukda yau asabar nasan yana tahfiz amma idan ya je sama wajan babansa ya kan leko wurina mu gaisa har musha hirar Kamalu."
Na dubeta a tsanake na ce." Ba na jin dadi wallahi tun bayan dawowarmu zazzabi yake damuna."
Da d'an alhini a tattare da ita ta ce." Amma Kuma sai ki yi shiru, ai da kin gaya mini sai na baki magani."
A sakarce na kalleta ina jin kamar na bugeta da mari, saboda ba ni da lafiya sai na gaya mata tunda ita nake aure.
[8/18, 10:38 AM] Aunty B: 64
Ta juya da karsashinta tana fad'in." Bari na gayawa maigidan b... Bata kàrasa ba na katse ta hanyar fad'in." Saki na yi?''
Sai ta juyo tana kallona. Na dubi tsabar idonta na ce." Ban sanya ki ba, don haka cire kanki daga wannan sabgar ki kalleni da kyau ba sakarai ba ce, balle ki ce za ki yi mini ta 'yan duniya kallonki kawai nake yi Hauwa."
Murmushi ta yi sai kuma ta d'an ta'be bakinta ta ce. " Menene abin fusata ranki ya dad'e, ni menene nawa a ciki, ba ni na kar zomon ba, zaman tare ne fa ya sanya na shigo dakinki, hakki ne na musulunci, ni kuma ba zan yi gaba dake ba domin ba dabi'ata ba ce hakan, amma ki yi hakuri idan abinda na yi miki ya 'bata miki rai."
Ban tanka mata ba har ta gama maganarta ta fita na ja tsaki mai karfi tare da kawar da kaina gefe.
Yusi da kansa yake sunkuye tunda muka soma maganar ya dago cikin yanayi na sanyi jiki da rashin jin dadin abinda ya faru ya ce." Mama to kin ce kada ta baki magani, kuma kin ce kada ta gayawa Baba yanzu ya za a yi to."
Shiru na yi ban ce masa komai ba domin har yanzu raina a b'ace yake dangane da rainin hankalin da Hauwa take ko'karin yi mini.
Wato ta fahimci zaman doya da manjar da muke yi shine da 'kumaji da gwarin guiwarta take taka 'kasa da ko'karin mayar da ni wawiya.
Yusi ya dame ni da magana na buga masa tsawa raina a b'ace na ce." Idan ba ka yi mini shiru ba wallahi sai ranka ya 'baci yanzu nan, idan na mutu ai lokacina ne ya cika, ba wanda zai jira duniyar kowa sai ya mutu.
Sai ya fashe da kuka tare da sanya kansa a tsakiyar gwiwarsa. Na janye idona daga gare shi na cigaba da tunanin hanyar da zan bi wajan ganin na dafa mutumin nan cikin ruwan sanyi domin zuciyata na ga alama ba zata iya juriyar nan da anti Yagana take ta nanata mini ba, a yanzu da ni bana tsoro ko fargar a lissafa mini auran ai ba ni kadai ba ce.
Wajan tara da kwata na dare ya shigo dakin. Hankalinsa yana kan Yusi dake can kan dadduma a kwance ya ci kuka ya koshi, na yi na yi dashi ya fita ya ci abinci ya'ki, biscuits din da nake ajiyewa a d'akin ya ci da lemo kawai ya ha'kura, ni kuwa dama damuwar da nake ciki bata barni sha'awar komai ba.
Kallo d'aya na yi masa na janye idona daga kansa Ina dan hade jikina sakamakon jin yanayina na nema ya sauya.
Ni na san wannan rikicin da nake ji baya rasa nasa da buk'ata irin ta gangar jiki. Tun kafin auransa da Hauwa sha'awa take damuna tun ranar da na banki magunguñ nan, ranar d'aurin auransa kenan, har muke je saudiya muka dawo abin na damuna kawai ina dannewa ne, abinda jiki ya riga ya saba dole idan ya buk'ata bai samu ba ya shiga wani yanayi. Ba zan ta'ba nemansa ba abinda na kudire kenan a raina.
Ya je ya daga shi a rikice yana fad'in." Kai aboki menene haka? ba ka da lafiya ne?" Yana maganar yana tattaba wuyana.
Yaron ya share hawayen dake zubo masa. Ai sai ya kara rikicewa ya dago shi sosai yana kallona ya furta." Bashi da lafiya ne?"
Share shi na yi ban bashi amsa ba.
Da gaya haka sai ya sake mayar da hankalinsa kan yaron yana tambayarsa. Da 'kyar muryarsa can kasa ya ce." Mama ce bata da lafiya shine take cewa mutuwa za ta yi?"
Ya dago da sauri yana kallona, ban dube shi ba ina dai kallon duk wani motsinsa ta gefan Idona.
Sai ya tashi yaron tsaye ya riko hannunsa suka nufo wajena, sai a lokacin na dubesu ina daga kwance ban motsa ba ya zauna kusa da ni shi kuma Yusi ya tsaya saitin kaina tare da dora hannunsa a saman goshina.
"Me yake damunki?" Yafada da 'yar kulawa.
A takaice na ce." Me ka ga ni?"
Ya zuba mini ido da yanayi na jin haushin amsar dana bashi. Ya girgiza kansa kafin ya dubi Yusi ya ce." Ka je wurin Antinka tana da abu mai dadi ka ce in ji ni ta baka."
Ya amsa da "To." Ya kama hanya ya fita. Ya juyo gare ni sosai yana cewa." Ki gaya mini abinda yake damunki domin ba ni so Allah Ya kama ni da hakkinki, ni dai nawa hakkin da ki ka take kullum ina gayawa Allah ya bi mini."
Jin abinda ya ce sai na tashi zaune sosai na dube tare da cewa." Hakki kuma na nawa ka take mini, ba ni da buk'atar kasan abinda nake ciki a halin yanzu domin abinda ya shafe ni."
Ya gyada kansa da fad'in." Okey to bari ba kira Antinki don na lura ita kadai zata gaya miki ki ji, yadda kike tsoranta ba kya tsoron mahaifin.....Kafin ya k'arasa na buga katifar gadon da k'arfin gaske na bude muryarta sosai na ce." Kada ka kuskura wallahi, na gaya maka duk abinda za mu yi ni da kai sunan mahaifina ya daina fitowa daga bakinka, idan babba ya zubar da girmansa sai karami ya hau ya taka, ba fa zan lamunta ba wallahi, ban raina naka iyaye ba ban ga dalilin da zai sanya ka raina nawa ba."
A tsanake ya ce." Rashin kunya ba inda zata kai ki, burunki na sake ki kije ki cigaba da harkokin tallata sura a social media ni kuma ban zan sake ki ba wallahi, domin duk inda aka je aka dawo za a ce Tajo ya ta'ba auranta, kin ga kenan yadda ki ka 'bata sunanki ni ma kin 'bata mini nawa."