Sashe 7
Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
"Ko da ke, ko babu ke, za su yi bikinsu, ba ni so iyalina su yi nisa da dai kusa ne sai na barki amma gaskiya maiduguri ya yi nisa, kuma kin ga sai kin yi kwanaki kafin ki ce zaki dawo."
Jin ya fadi haka ya sanya na ce." Ai kai zaka fad'i kwanakin da zan yi."
Ya yi shiru yana lumshe ido kamar me shirin bacci.
Na dawo kusa dashi na zauna na ri'ke hannunsa a hankali na ce." Ka ji my love."
Ya bude idonsa da suka dan canza yana kallona ya ce ." Yaushe rabon da na ji wannan sunan abakinki, yanzu ai kina bukatar zuwa biki ko?"
Shiru na yi ban ce komai ba.
Ya girgiza kansa tare da sake rufe idonsa. Jikinsa na sake matsawa sosai a hankali na ce." Ka ji sweet love." Bai tare da ya bud'e idonsa ba ya ce." Matsa kada ki sanya na yi abinda ban yi niyya ba."
Ban matsa ba, sai ma hannuna dana sa Ina d'an jan gemunsa a hankali.
Ya bude Ido muka tsirawa juna ido.
Hauwa ta turo kofar d'akin ta shigo hannunta ri'ke da wani kwando cike da kayan abinci.
Janye idonta ta yi ta wuce can wajan da yake zama domin cin abinci ta fara shirya wurin.
A hankali na dan matsa daga kusa dashi ina fad'in." Ka amince ko?"'
"Zan yi shawara tukkun zuwa yamma zan gaya miki abinda na yanke."
Don kada ya tsinka ni a gabanta ya sa na tashi daga kusa dashi ba tare da na ce komai ba na kama hanya fita. Na ji ta ce." Amina tsaya kawai a yi ta ta kare, ba zan bari a ginu a haka ba domin dukkaninmu musulmai ne, ba maguzawa ba, idan shi mijinki yana jin tsoronki, ni gaskiya ba a haifi wata mace da zan ji tsoro ba, kuma ba zan yarda na yi zaman boranci ba, ba kuma zan yarda a tauye mini hakki ba."
Na ce." Akan me kike wannan zantukan."
Da mamaki da takaici ta ce.'' Au tambayata ki ke yi akan me nake yin magana."
Na ce." 'Kwarai kuwa."
Yana zaune yana jin mu bai ce komai ba.
Ta ce." Jiya girkin waye?"
Na ce." Oho!"
Ta zo iya wuya kawai sai ji na yi ta lallayo ashar ta jefo mini tana huci." Ni za ki mayar sakarai, kina abu kamar mai tabin kwakwalwa, na rantse miki da Allah ba za mu wanye lafiya dake ba, tunda ni ban shiga huriminki ba, ba zai yiwu ranar girkina ki dinga yi mini kutse ba."
Na dube shi shima yana cike da mamakin zagin da ta yi don sai hararta yake.
Na ce." Ka ji tana zagina ko?"
Ya ce." Je ki kawai, ki kyale ni da ita."
Ta kara fusata tana cewa." A dake ni a hana ni kuka, kuma a ce ba zan yi magana ba, sai ta fashe da kuka mai karfi
Ya ce." Idan zagi ne ni zaki ga domin ni na kwana da Amina a ranar girkinki, amma ita bata da lefi, Hauwa wannan ya zama na farko ya kuma zama na karshe kada ki kuskura na kara jin zagi a gidana, kin nuna mini rashin tarbiya da kuma rashin aiki da ilimi.
Ni ba namijin da mace take d'agawa hankali ba ne, ni na yi miki ba daidai ba, a wurina zaki nemi hakkinki, ita Amina ai bata da lefi.
Ta sake fusata tana cewa." Haka zaka ce ko? Ni me yasa ba ka nemana a ranar girkinta duk da bata zuwa dakinka ai baka taba zuwar mini da bukata ba."
Ya ce." Ai shiyasa na ce miki a wajena za ki nemi hakkinki, domin itama dole na yi mata."
Ina tsaye ina jinsu duk abinda ta fad'a a kaina sai ya tare maganar yaki bari sunana ya fito. Cikin raina na ce idan don na ji dad'i ne ban ji ba, domin kuwa wataran ni ma zai iya kware mini baya a gabanta, na bude d'akin ba fita na barsu suna ta turzawa, amma na yi mamakin sosai, domin ni a tunanina tunda ba na zuwa dakinsa ranar girkina ita da shi suna kwanciyar aure, ashe zargin hakan kawai nake, ashe shine dalilin da ya sanya jiya ya famshe kwanakinsa.
Yini na yi cikin zullumi da tunanin zai barni ko ba zai barni ba.
Har na yi shirin kwanciya sai gashi ya shigo shi ma da shirin kwanciyar na zuba masa ido har ya k'araso ya zauna a gefana, yadda nake kallonsa shima haka yake kallona.
Na daure na ce." Da ka sani ka ce na fito falo sai mu yi magana, kada ta zargi wani abu."
Ya ce." Ina jin tsoronta kenan?"
Girgiza kaina na yi a hankali na ce." Ba haka nake nufi ba, kai zaka nemi zaman lafiya a gidanka."
"Kada ku zauna lafiya don Allah kin ji ko."
Jan bakina na yi na shiru na rabu dashi abinda dai na kudire a raina shine idan za ta ce zata yi mini hayaniya ko ta zage ni kaniyarta zan ci, tunda ga wanda ya yi mata nan
Ya dube ni a tsanake kafin ya ce." Na kira Anti Yagana a waya kan maganarmu dake ta d'azu."
Yanayin yadda ya yi maganar ya sanya ni jin sanyi a cikin raina, har ga Allah ina jin dadin yadda yake mutunta anti Yagana har ya sakaya sunanta.
Na nutsu Ina kallonsa. Ya cigaba da cewa." Na amince za ki je amma da sharad'in kwana uku kacal za ku tafi a jirgi ke da Yusi da Sukairaju nasa a yi muku shirin hakan, kada ki sa'ba umarnina."
Da sauri na ce." In sha Allahu na gode sosai Allah Ya kara girma." Ya amsa da "Amin." Kafin ya cigaba da cewa." Ni ma yana da kyau na bada gudumawa ko."
Murmushi na yi ban ce komai ba.
Ya ce." Nawa ki ke ganin zan basu."
Na dube shi sai na dan ji tausayinsa, shi dai abin sa bai rufe masa ido ba.
Na ce." Ko nawa ka basu sun gode."
Ya ce." Ai shawara na tambayeki sai ki ce mini ka basu abu kaza."
Na ce." Wallahi ban san abinda zan ce maka ba.
Shiru ya yi yana lalube a wayarsa.
Shigowar sa'ko na ji a wayata dake gefana na d'auka ina dubawa miliyan goma ne.
Na dube shi cikin mamaki mai tsanani. A nutse ya ce." Ki cire miliyan biyar ki basu gudumawace ni dake. Miliyan biyar din kuma kudin yaranki ne wanda na yi muku alkawarin satikan da suka wuce ba ke kadai na bawa kuna da yawa.
Na ce." To ai ni ban ce ina neman hakki ba."
"Idan ba ki ce ba yaran fa?" Ya fad'a yana kallona.
Na ce." Ni dai gaskiya dawo maka dasu zan yi wallahi.
Ya mike yana fad'in." Ki dawo dasu ki ga 'bacin rai, ki ajiyewa yaran zasu amfana anan gaba in sha Allahu, kuma koda jita jita zata sake tashi a gari ba zasu zarge ni ba."