Sashe 2
Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya tsaya bai kàrasa ba kamar yadda aka umarce shi amma bai fita ba ya sake sunkuyar da kansa da ladabi ya ce." Sir lamarin ne ya sake yin tsamari ne wannan yana da kyau ka duba domin daga gida abin ya sake fitowa."
Shiru ya yi bai ce masa komai ba, sai hakan ya bashi damar isa wajensa ya mik'a masa wayar tare da nuna masa abinda yake zo ya gani.
Da sauri na ga ya d'ago kansa yana kallona da mamaki mai yawa a tare dashi.
Ban kawo komai ba balle na zargi abin ya shafe ni.
Ko da ya gama karantawa bai ce komai ba ya bashi umarnin fita. Numfashi ya fesar kafin ya yun'kura ya tashi ya nufi samansa ba tare da ya sake wata magana ba.
Gabad'aya hankalinmu ya tashi har mahaifiyartasa, ta ma manta wadda take dashi fadi take yi Amina tashi ki bi shi maza domin yana buk'atar wani a kusa dashi.
Ni kaina sai bayan na tashi din ne naga kamar rashin dacewar hakan tunda ga amaryarsa a ganina ita ya kamata ta je kusa dashi.
Sai na dan tsaya da tafiya.
Ta sake fad'in." Maza ki je mana, kin san shekaru sun fara hawa kansa kada ya yanke jiki ya fad'i.
Gabana ya buga da karfin gaske dana tuna rashin lafiyar da yayi kwanaki fad'uwa ya yi har sai da aka d'auke shi bai san inda kansa yake ba.
Na nufi saman da sassarfa da fargabar abinda zai biyo baya.
yana zaune a gefan gado ya d'an tallafe ha'barsa da hannu kamar mai nazari na nufe shi yayin da tausayinsa yake tsirga mini, kusa dashi na zauna a nutse na ce." Baba kada tunani ya haddasa maka ciwo, kaifa babba ne, kuma kayi gwagwarmaya menene baka gani ba don Allah kada ka damu akan wannan abin, muna cikin tsananin bukatarka a yanzu."
Ya dube ni a nutse ya furta." Ke da yaranki Kuna buk'atar hakkin tsohon mijinki Aminu Salihi wanda na take bayan rasuwarsa ko?"
Gabana ya wani buga da mugun karfi. Na zuba masa ido Ina kallo lebana yana rawa tsabar mamaki da tashin hankali.
Ya d'auki wayarsa dake saman dirowa ya farara labule. Minti uku ya miko mini, babu gardama na kar'ba wani pege ne da ban san me shi ba, akayi tagging dina wanda ya yi rubutun yana magana akan yadda Alhaji Tajo yake amfani da matasa domin tara dukiya har yana bada labarin Yaya Aminu da irin bautar da ya yi masa yana kuma jadaddawa a rubutunsa cewa da yawuna ya fito yake magana akan hakkina dana yarana da aka take.
Cikin wani irin yanayi na tsantsar damuwa da tashin hankali na shiga fece book din ina ta scrolling abinda yake ta trading kenan. 'Cewa jita jitar da ake ji dangane da Alhaji Tajo da ma'aikatansa gaskiya ne, domin kuwa matarsa wadda yake aure a yanzu tsohon mijinta Aminu Salihi kafin rasuwarsa ya yi aiki a karkashinsa wanda kowa shaida ne dangane da yadda ya bautata masa a wata majiyar ma ana cewa sanadiyar aikinsa ne ya kamu da lalura sa'i daya kuma ya kore shi daga aiki domin ya gane bashi da mamora karfinsa ya kare, bayan ya sallameshi daga aiki bai bashi komai ba, a haka Aminu Salihi ya yi ta jiyya har ya rasu da damuwar hakan. Rahoto ya tabbatar da cewa da yawun Aminu Salisu mai hula wannan 'yar kasuwar nan da ta yi shura wajan fashion designer a kafafan sadarwa da amincewarta wannan rahontan ya fita."
Gidajen jaridu da wanda suka kai da wanda basu kai ba sai posta hoto na da nasa suke yi. Wasu ma harda hoton yaya Aminu da Kamalu da Yusi.
Kuka ya k'wace mini da k'arfi na sanya hannu na toshe bakina Ina kallonsa hawaye na shatata.
Ya kar'bi wayarsa ya ajiye ya matsa daga kusa da ni, ya ja jikinsa ya jingina da allon gadonsa.
A hankali na matsa kusa dashi ina kuka na ce." Wallahi tallahi Baba ba da yawuna aka fitar da wannan maganar ba, asalima ban san me pege din ba idan ka lura sabon shafi ne ba a jima da bud'e shi ba, wata'kila an shirya mini hakane domin a 'bata ni a wurinka, ba zan ta'ba cin zarafinka a duniya ba Baba idan ban ya'da alherinka ba ai ba zan yad'a sharri a kanka ba, ka yarda da ni wallahi ba ni da masaniya abinda yake faruwa, babu hannuna."
[8/16, 9:06 AM] Aunty B: *62*
Ya dube ni a yayin da na gama firgicewa domin hankalina ya kai ma'kura wajan tashi jin yadda lamarin yake nema ya sauya salo, hakika duk wanda ya shirya wannan lamarin ya yi mini farin sani. Na san dai kafin k'addarar aure ta ratsa tsakanina dashi a ko'ina na kan saki bakina na soki sha'aninsa na kushe shi, na nuna ba na daya daga cikin mabiyansa idan aka tambaye ni hujja ba na rufewa fad'a nake yi. Ban ta'ba tunanin hakan zai janyo mini gagarimar matsala ba tunda ban ta'ba zaton aure zai ratsa tsakaninmu.
Ganin yadda na kanainaiyeshi da ro'ko da magiya ya sanya ya sassauta fuskarsa ya gyara zamansa a tsanake ya dube ni yana ce wa." Me yasa tunda muka yi aure ba ki gaya mini cewa Aminu Salihi ne mahaifin Yusuf ba.
Hannu na sanya na goge hawayen da suke zuba na ce." Ban san ta yadda zan gaya maka ba wallahi, ni dai abinda nake so ka fahimta shine wallahi ba ni da hannu wajan wannan rubutun. Abinda na yi Imani dashi shine duk wanda ya shirya hakan yana da masaniya akan sha'anina."
Ya zuba mini ido kafin ya ce." To ke wa kike ganin zai hakan a cikin wad'anda ki ka sani ko kike tarayya dasu."
Na hada hannuna da nasa na rintse a na ce." Wallahi ba zance ba Baba, ka yarda da dani har cikin zuciyata babu mugun nufi a tsakaninmu."
Ya ce." Ai dama ni ma ban ce da mugun nufi ba, abinda dai ya fi damuna yadda ba ki sanar da ni cewa uban yaranki ya ta'ba aiki a k'arkashina ba, kin ga dole ne yanzu zuciyata ta d'ora zargi akan cewa da hannunki maganar nan ta fita, da kin sanar da ni tuntuni da Ina ga da duk haka ba ta faruwa."
A sanyaye na ce." Ban san ya za a yi na gaya maka ba, to na ce maka me? ya fa riga ya mutu shekara da shekaru kuma maganarsa a tsakaninmu zata iya haifar da wata matsalar maigirma."
Ya d'an jima yana kallona kafin ya ce." Ki gaya mini gaskiya shin bayan rasuwar Aminu Salihi Alhaji Sammani ya je ya yi muku ta'aziya ko bai je ba."
Girgiza kaina na yi a hankali na ce." Bai je ba."
Ya ce." Kin ga hakan yana nufin kudin dana fitar da sunan magada suna wajansa"
Shiru na yi ban ce komai ba, ni dai burina kada ya zarge akan abinda yake ta yawo a kafafan sadarwa.
Ya dan riko kafadata tare da sanya tafin hannunsa yana goge mini fuska ya ce." Daina kukan haka na aminta dake wata'kila ana bin ki ta karkashin kasa ne to sai aka samu wannan damar amma duk yadda akayi wanda ya fitar da maganar nan ya san ki ciki da waje, babu komai zai wuce in sha Allahu."
Yana maganar yana dan bubbuga bayana. Zuciyata ta dan yi sanyi amma har yanzu damuwar bata sake ni ba, domin yadda ake ta sukarsa ana yad'a sharri akan harkokinsa ya tsaya mini a raina.
Luwai na yi a jikinsa ina sauke ajiyar zuciya yayin da hannunsa yake dan dukan bayana a hankali a hankali d'akin ya yi shiru na tsayin mintina goma babu sautin komai sai na numfashinmu.... Daidai lokacin da nake yun'kurin zare jikina daga nasa ta turo d'akin ta shigo duk muka bita da kallo
Cikin 'yar fargaba na cire jikina daga nasa na d'an ja gefa, ta k'araso a nutse babu fara'a a tare da ita ta ce.'' Kin san dai ba haka ake yi ba ko? kada ki bud'e kofar fitina a tsakaninmu lamarin ba zai yi mana kyau ba wallahi, wace macece za ta yarda ayi mata wannan iskacin, aka ce ki zo domin ki kula dashi me yasa ba ki gayyace ni ba, a matsayin matarsa nake kuma amaryarsa me ya sa za ki 'kebe dashi kusan mintina talatin, kin san dai ko ke aka yi wa haka ba za ki ki dadi ba."
Shiru na yi ban ce mata komai ba, domin duk maganganunta akan hanya suke tana da gaskiya kuma ko ni ce ba zan yarda ba gaskiya dalilin ma da ya sanya kenan na ja bakina na yi mata shiru tana ta furzar da takaicinta. Jin tana sanyo Hajja a ciki ya sanya ya ce." Ba za ki yi mana shiru ba ko? ke wai me yasa ba kya aiki da iliminki ne, me ki ka shigo ki ka ina yi da ita da kike so ki zage ni."
Sai ta rushe da kuka tana cewa." Ni ba da kai nake ba, ai ta san ba ta kyauta mini ba shiyasa ta yi shiru bata da gaskiya, kai kuma kana biye mata, har kana so ka kare ta."
Yunkurawa na yi na tashi domin fita daga d'akin ta bi ni da harara tana jan tsaki ban kulata ba na kama hanya na fice zuciyata a cunkushe.