← Book details Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 33

Sashe 19

Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Yusura na sanya ta shiga kicin domin ta yi mana abinda za mu ci na ce ta yi da d'an yawa sai mu tafi dashi asibiti amma kafin nan na umarceta da ta fara dafa mini shayi tukkuna na d'umama cikina dan a hautsine nake jin cikina.
Ina lure da Sahura sai kallona take yi a fakaice da dai na gaji da kallon da take yi mini na ce." Wai ke don Allah kallon me ki ke yi mini ne? Ina fa kallonki tunda ki ka zauna ki ke bina da ido na canza ne?"
Tana dariya ta ce." Sosai kuwa kin canza wallahi wannan kamar ba Aminar da na sani ba ce, wannan kamar an 'bareta daga leda."
Na dubi jikina ina son ganin abinda ya sanya ta fadi hakan.
Ta cigaba da cewa." Tunda na zauna kamshinki yake surnanowa hancina kamshin ma irin na manya ne wallahi irin kamshin Oga ki ke yi sis, kin ga yadda fatarki take sheki kuwa kin cika kin zama wata 'yar gayu dubu fa faratan yatsun hannunki dana kafafu ki tas dasu.
Da sauri na fara duban yatsuna ina fad'in." Ke kam Sahura kin fiye zuzuta abu wallahi, ni dama can haka faratan yatsuna suke ai ba na lalle shiyasa suka yi haske."
"Ba haka suke ba wallahi ke kaf fa kin canza launi komai naki ya sauya shekarunki ma sun 'buya."
Murmushi kawai na yi domin na riga na san duk abinda zan fada tana da amsar da zata ba ni.
Na ce." Ke ma ai kin sauya sosai Sahura kin yi ki'ba da haske."
Ta ce." Hum! ciwo nasha fa ki ce kawai na rame sis, gaya miki ne kawai ban yi ba watanni uku da suka wuce na yi 'bari na 'yan tagwaye wallahi nasha wahala sosai har sai da aka yi mini wankin mahaifa.
Cike da alhini da damuwa na furta." Amma ba ki kyauta mini ba wallahi, ki tsallaken rijiya da baya irin wannan amma ki kasa gaya mini to menene amfanin hakan."
"In banda abinki ai abin alheri ake fad'awa mutum ba na tashin hankali ba, kawai kuma sai na kira ki na ce dake na yi 'bari."
Tsaki na ja na furta." Ba ki kyauta mini ba dai."
"Kin ga mu bar zancan nan tunda ya wuce, na gaya miki garin zirga zirgar asibiti na ga ana jigila da Alhaji Muntari a asibitin Murtala bashi da lafiya wallahi ba ki ga yadda ya rame ba da alama dai yana jin jiki domin kuwa bai san wanda yake kansa ba suna ta yawo dashi a kan keken nan babu gado, Maman Salimat din ce ma muka gaisa a tsaitsaye itama bata wani gane ni ba sai da na ce mata ni ce Sahura kawarki maman Yusura tukkuna ta gane ni, dana tambayeta ta ce mini za su yi kokarin kai shi asibitin Malam ko Nasarawa amma fa ga dukkanin alamu babu abin domin da da akwai yadda yake cikin tsananin ciwo ba za su kai shi asibitin gwamnati ba."
Tunda ta fara maganar jikina ya shika fargaba da tsoron duniyar nan ya dabaibayeni. Na ce." Sahura ni wannan duniyar tsoro take ba ni wallahi, yau ka ji wannan masifa gobe ka ji wata. Ko yau kana tare da mutum amma gobe ace maka ya mutu, wallahi duk duniyar nan ta fice mini daga rai."
"Ai mai hankali ne kawai zai yi irin tunanin da kike yi sis, amma wanda ya riga ya auri duniyar ai gani zai yi duk abinda ake fad'a karya ne, ke akwai ma wad'anda basu yarda da mutuwa da ranar tsayuwa ba."
Na ce." To Allah Ya shiryesu masu irin wannan tunanin kuma ba ta gaya miki abinda yake damunsa ba."
"Gaskiya bata fad'a mini ba, a rikice fa take domin ga dukkanin alamu tun a gida sun ci kuka sun koshi, yadda dai jikinsa ya shika wuya ya langwane hannu ma haka nake ganin kamar ya samu mutuwar b'arin jiki"
Cike da tausayi na ce." kome ya janyo masa wannan mummunan ciwon oho, ga nauyi na iyali da yara, gashi shi kuma a iya zamana dashi na fahimci cewa bashi da plan in banda wannan gidan nasa fa ba na tsammanin yana da wata kadara, duk abinda ya samu ya yi bushasha haka tsarinsa yake wallahi ya ba ni tausayi Sahura."
Ta ce." Ai don ma ba ki ganshi ba ne wallahi ba za ki ce shi ba ne, duk wannan jikin babu ya zaizaye ya yi duhu."
"Allah Ya bashi lafiya in sha Allahu za ki raka ni na dubo shi."
Ta dube ni da mamaki." Ki duba shi akan wace hujja da dai kin haihu dashi ne, amma sis yanzu da auran wani za ki je duba tsohon mijinki."
"To menene Sahura ciwo fa aka ce, don na duba shi sai ya zama lefi, saboda kawai abin magana bashi da wahala, ke fa da bakinki ki ka ce yana buk'atar taimako, ni kuma ina so idona ya gane mini muddin akwai buk'atar taimako zan taimaka masa wallahi domin ni ma ya taimaka mini ya rike ni da yarana ko yaya ne dole na dubi alherin da ya yi mini a baya."
A dan sanyaye ta ce." Ban'ki ta taki ba sisi, amma kin san ba kowane namiji ne zai yarda da uzurinki ba, kin san kowa da irin fahimtarsa."
Tsaki na ja na ce." Sahura kyale ni don Allah, ba dai akan oganki kike magana ba, yanzu ma rigima muke yi sai mu d'ora da wannan."
Chapter 19 · 0% Book details