Sashe 1
Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
[8/14, 10:39 AM] Aunty B: *61*
Ganin yana waya da Sukairaju akan sha'anin matarsa ya sanya na tashi ba tare da na ce komai ba na nufi d'akina na bar su a wurin.
Mintina goma sha biyar Yusi ya shigo lokacin ina gyara jeran madubina na dube shi a nutse na ce." Yusi idonka kenan baka nema na, ka manta da ni ko?"
Ya rungume ni yana yana dariya yana cewa." Mama kece fa kika ce duk lokacin da na ganku a falo kuna zaune na daina zuwa wurin."
Na gyad'a kai Ina cewa." E haka na ce, amma me yasa da kuka dawo baka neme ni ba, ai ka zo mu gaisa ko?"
Ya rike hannuna yana fad'in ." To ki yi hakuri." Ban ce komai ba na cigaba da gyara kayan shafata sai yasa hannu yana taya ni. Ya ce." Mama nasan yanzu Yayana ya kara girma ko?"
Na ce." Sosai ma, ai za mu sake komawa duba shi in sha Allah." Da murna a tare dashi ya ce." To shikkenan mama, amma yaushe zai gama karatun kuma idan an sallamo shi daga makarantar a ina zai zauna."
Na dube shi a nutse na furta." A can wajan Gwaggwo mana, mun yi magana da Hamusu zai dinga tafiya dashi kasuwa."
Wannan maganar na yi ta ne a daidai lokacin da maigidan ya turo kofar d'akin a bazata don ban yi tsammanin hakan ba ya shigo. Yana da kaifin ji dalilin da ya sanya ma kenan ban tsaya yin kokwanto akan ya ji ko bai ji ba.
Kawai na zuba masa ido yayin da shima ya zuba mini nasa idon wanda suke cike da tuhuma da zargi. Na fahimci yanzu yadda ya tsani mutuwarsa haka ya tsani jin sunan Hamusu a bakina, ban san menene dalilin da ya sanya ya d'ora masa karan tsana ba, bayan ada ba haka yake ba.
Yusi ya bashi hannu suka cafka dama sararsu kenan motsi kad'an sai su had'a hannu. Ya dafa kansa da cewa." Ka je d'akina na rage maka abinci." Sai ya sake bashi hannu a karo na biyu suka tafa.
Ya kama hanya da sauri ya bude d'akin ya fita. Ya rage da gani sai shi a d'akin. Na nemi gefan gado na zauna ina kallonsa don ban san da mai ya shigo ba, na san dai tunda ya ji maganar Hamusu ba zai yi shiru ba. A cikin halayensa marasa kyau akwai zargi na gama fahimtarsa.
Na gyara yanayin fuskata sosai domin tarar abinda yake bakinsa. Ya zauna a gefana yana fad'in.'' Wace magana na ji kuna tattaunawa da Yusuf yanzu dai shine abokin shawararki ko?"
Murmushin takaici na yi na ce." A a kai ne abokin shawarata Baba, magana muke yi akan Kamalu yana tambayata idan ya dawo daga makaranta a Ina zai zauna na ce masa can wurin kakarsu Gwaggo mun yi magana da Hamusu zai dinga tafiya dashi kasuwa."
Ya gyada kansa yana dubana ya furta." Ashe kina bibiyar sha'anin yaron."
Cike da mamaki na ce sosai ma kuwa." Ya furta." Babu inda zai zauna sai nan tare da mu gabad'aya domin raba kan yaran zumuncinsu zai yi rauni, baya ga haka kuma, a can unguwar taku ya lalace ai, to me zai sanya kuma a sake mayar dashi, idan har kun yanke shawarar zamansa a can kano to sai ku had'a da d'an'uwansa gabad'aya ku ajiyesu a waje daya."
Na yi shiru ina auna maganarsa. Gabad'aya kaina ya kulle na gaza fahimtar abinda yake nufi da wannan maganganun yanzu ina iya furta wata magana ya canza mini manufa, ni dashi duka ba mu da karfin iko kamar dangin Babansu. Hamusu kuma yana iyakacin bakin kokarinsa wajan ganin ya bashi girma kuma bashi da wata matsala, amma tunda sun nema kuma suna da hakki akan yaran nan ya kamata a ce wannan karon na yi kawaici da alkunya na ba su daya na rike d'aya, amma ina ganin ba zan samu goyon bayansa ba, nema ma yake ya mayar da abin rigima da 'bangaranci.
Na share shi kawai ban ce masa komai ba domin ina danne zuciyata ne ba na son na biye masa na san idan muka fara ni dashi gabad'aya ba zata yi mana kyau ba."
Ya tashi zai fita na ce." A game da maganarka ta d'azu ina da ja kai."
Ya tsaya tare da juyowa yana kallona.
"Wace magana kenan."
"Dangane da amanar matarka da ka ce ka ba ni, ban kar'ba gaskiya domin ni ma nema nake yi ka ri'ke amanata don har yanzu ban san kaina ba."
Ya ce." Ai hakkinki ne a matsayinki na uwargida ki ri'ke mini amanar gida da duk wanda na kawo na ajiye shiyasa na gaya miki."
Na ce." Ban kar'ba ba gaskiya kuma zuciyata ba ta aminta da zamanta a samanka ba, idan adalci za ka yi kawai ka ce mata ta sauko kasa."
A nutse ya furta." Ba ki ji uzurinta ba ne, tana da ciwon kirji ta ce ko a wajan aiki a kasa take ba ta iya zurga-zurgar hawa sama."
D'auke kaina na yi ban ce masa komai ba. Ya ce." Idan kina ganin da damuwa to kema sai ki tattaro ki hawo saman ku tare bakidaya hakan zai fi."
"Ina buk'atar tsinka jinina, da zan hau ai da tun kafin ta zo gidan na hau."
Ya daga kafad'arsa ba tare da ya ce mini komai ba ya bud'e kofa ya fita.
Na ja jiki ahankali na kwanta saman gado ina matse jikina kawai na ji hawaye na fita daga idona.
Ajiyar zuciya na sauke tare da dan rintse ido yayin da damuwa ke sake sukar ilaihin jikina.
Daurewa kawai nake yi ganinsa ya k'ara motsa mini sha'awar da ta dame ni.
Haka na 'kàrasa yinina cikin damuwa da takura da daddare da kyar na fita falon shi ma don kada Hajja ta zargi wani abin ne, na same su kuwa gabad'aya har ita amaryar inda ta sheka ado da wani uban Les ta soka d'aurin dankwali wanda ya fito da k'arin gashin da ta yi. Kwaliyya ta yi sosai irin ta amare har dasu gashin ido ga sarka nan d'azu awarwaro da zubona a yatsun hannunta.
Ban damu ba domin abin da ya dame ni daban shiyasa adonta bai d'auke mini hankali ba, abinda dai ya so ya bata mini rai bai wuce ganinsa zaune a saitinta ba suna magana da juna.
Na yi 'kokari sosai wajan nuna ban san me suke yi ba, muka gaisa har shi din da yake dan satar kallona itama amaryar ta yi mini sannu da fitowa Hajja tana cewa" ai yanzu nake shirin aika Yusi ya kiraki." Na ce." Wallahi ina yin sallar magriba bacci ya kwashe ni sai yanzu na farka.
Kafin tayi magana aka kira shi a waya maganarsa ta d'auki hankalinmu gabad'aya zance ne dai bai mutu ba domin iyalan wani mamacin ma sun sake yin magana a sahar nan ta fece book inda suma suke kalubalantarsa akan take hakkinsu da ya yi.
Gidan jaridar da duniya ta aminta da rahotanninsu sune suka kira shi domin neman k'arin bayani da kuma neman alfarma samun lokaci daga wajensa don su tattauna ya kuma wanke kansa dangane da zargin da jama'a suke yi a kansa.
Kafin ma ya kammala wayar Sukairaju ya shigo, ya d'an tsaya daga gefe bayan ya gaishe mu. Sai da ya bari ya gama wayar tukkuna ya risina tare da mika wayar hannunsa.
Ya kar'ba kimanin minti biyar ya gama dubawa ya mika masa wayarsa a nutse ya ce." Kada ku damu in sha Allahu alheri ne, gobe za mu tattauna da gidan jarigar Amana daily trust zan wanke kaina bisa zargin da jama'a suke yi mini.,
Sukairaju ya sake risinawa yana fad'in." Ranka ya dad'e lamarin ne ya karad'a gari mussaman social media jama'a sai maganganu marasa dad'i suke yi akanka, dalilin da ya sanya hankalinmu ya tashi kenan"
Ya furta." No kada ku damu zai wuce an riski kalubale iri iri, an cimma nasara kuma, wannan ba komai ba ne, zan dai yi bincike akai sosai."
Hajja ta ce." Amma dai Alhaji Sammani bai kyautawa rayuwarsa ba wallahi, yanzu wanene ya san iya adadin mutanan da ya takewa hakki."
Ya ce." Sai Allah Hajja domin wad'anda suka rasu a 'karkashin ayyukana suna da yawa wallahi, kuma duk wanda na tabbatar da mutuwarsa zan fitar da hakkinsa na bayar, shi Sammanin shine ya zalince ni."
Sukairaju ya k'ara shigowa a karo na biyu da sauri ya nufo shi da waya, kafin ya k'arasa ya dakatar dashi yana cewa." Sukairaju na gaji da magana daya don Allah kada ka k'araso nan, na san inda matsalar take zan kuma yi maganinta."