← Book details Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 33

Sashe 14

Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Haka muka karya a daddafe har yaran suma gabad'aya jikinsu ya yi sanyi ganin yadda muke cikin alhini da damuwa Yusi dai ya takure a kusurwar kujera har da kuka sai da anti Yagana ta rarrashi tukkuna ya yi shiru.
Garba almajirin anti Yagana ya shigo ya ajiye robarsa a bakin kicin ya shigo falon muka gaisa anti Yagana ta ce ya yi maza ya zuba ruwa a diro amma kafin nan ya fara wanke shi. Har ya juya zai fita sai ya tsaya yana kallon Yusi ya ce." Ka je in ji wannan din nan yama sunansa?" Ya tsaya yana tunani. fadila ta ce." Bak'on da suka zo tare?"
Da sauri ya daga kansa yana cigaba da cewa." E shi ya ce na kira shi yanzu ya je Babansa ya kira waya za su gaisa."
Na dubi Yusi da mamaki a tare da ni, dama duk safiya Yana kiran waya don su gaisa, da farko da Garba ya ce ya je na d'auka Sukairajun yana buk'atar wani abu ne bayan karin kummalon da aka kai masa.
Yaron ya tashi da saurinsa sai na dakatar dashi ina fad'in." Yusi dama Baban yana kiran waya ne ku gaisa kullum?"
Ya ce." E wataran ma har ya ce na bawa su Arif da Sultan su gaisa, ko Arif?" Ya fad'a yana kallonsa. Ya ce." Eh hakane har ya ce a gaishe daku bakidaya.''
Na gyada da mamaki fal a tare da ni. To shin wai me mutumin nan yake nufi ne? Ni ban ma ga amfanin zaman Sukairaju a tare da ni ba, kuma yaro dai ni na haifi abina ba za a yi wannan munafurcin da ni ba, ka sake ni amma ka dinga bibiyar 'yan uwana har da yaron da na haifa da wani namijin.
Na ce ." To koma ka zauna ba za ka je ba."
Anti Yagana da sauri ta ce." Akan me?" Shiru na yi kawai Ina kallonta da mamakin neman dalilin da take yi wanda ta fi kowa sani.
Tana kurbar kunun gyadar da ta tsiyaya kofi ta ce." Ki kyale shi kawai ya je, idan kuma ba so kike ki fito da komai fili ba, ta inda ya fi ki wayo kenan, yadda yake tafiyar da lamarin a siyasance sai ki zuba Ido ki ga iya gudun ruwansa."
Na yi shiru Ina nazarin maganarta. Ni dai da ta barni zan datse alakar ne daga yau din, shi ma Sukairajun na sallameshi don ban ga amfanin zamansa a tare damu ba illa dorawa masu gidan nauyi da ya yi."
Kimanin minti ashirin yaron ya yi da fita sai gashi ya shigo ya zauna yana kallon anti Yagana ya ce." Baba ya ce na gaya miki zai kira ki yanzu."
Da sauri ta ce." To shikkenan Yusifa."
Kawai na saki baki ina kallon ikon Allah. Gabad'aya abincin ma da nake ci sai ya fita daga raina na zuba mata ido a lokacin da ya kirata suna magana akan rashin lafiyar Gwaggwo.
Anti Yagana ta saki jiki da baki tana ta jadadda masa yadda Gwaggwon take jin jiki har da ce masa tana kwance bata iya motsa komai na jikinta.
Da yake handsfree ta sanya wayar ina jin muryarsa tar yana cewa." Ni muna gaisawa da Yusuf na ji ya fashe mini da kuka koda na tambayeshi shine yake gaya mini kakarsa ce babu lafiya kukan yaron ya daga mini hankali kwarai da gaske dalilin da ya sanya ma kenan na kira ki domin na tabbatar ya gaya mini duk yadda aka yi, zan yi waya asibitin Malam din duk abinda ake bukata game ba zai gagara ba idan ma gado za su bata hakan zai fi sauki Allah Ya bata lafiya."
Anti Yagana tana ta amsawa da Amin Ya Allah, mun gode sosai da kulawa Allah ya kara arziki da wadata."
Suka yi sallama ta juyo tana kallona raina a tsananin 'bace na mik'a hannu dukkunsu har shi Yusi din ba su ankara ba na kife shi da marin da ba tabbatar zai gigita shi .
Illai kuwa a ki'dime ya tashi ya yi hanyar waje hannunsa dafa da kumatunsa hawaye suka fara kasa tsere a kuncinsa.
Anti Yagana ta rufe ni da fad'a tana fad'in." Sai kin je kin tsiyayar masa da ruwan ido haka kawai saboda zalinci zaki kifa masa wannan mugun marin me ya yi miki? Lefin dai ba zai wuce ya gayawa mijinki magana ba, shikkenan fa sai ki lahanta shi.''
Shiru na yi ban tanka mata ba kawai na tashi da zumar barin wajan. Yaron da yake tsaye a bakin kofa ya d'auka dukansa zan sake yi ya fita a guje yana sheshsheka.
D'aki na shiga na zauna a gefan katifa kaina a daure domin duk yadda na kai ga ganin na hasaso abinda mutumin nan yake nufi a kaina na kasa ganewa.
Shin wai ko ya manta da cewar ya sake ni ne, wane irin munafurci ne wannan da neman lallai sai ya d'ora mini lefi. Ka sake ni ka fita daga sha'anina mana.
Wayata na d'auka da sauri kiransa zan yi domin na ji shin me yake nufi da ni ne.
Kamar yana jiran kiran nawa karaf ya daga. A kaurare babu gaisuwa balle girmamawa dalili duk ya zubar da mutuncinsa a idona bana son mutum munafiki.
Na ce." Ban gane abinda kake nufi ba, ko ka manta cewa yanzu babu wata alaka da take tsakanina dakai? Ina ruwanka da bibiyar abinda ya shafe ni. Gwaggwo dai mahaifiyar mijina ce wanda mutuwa ta yi mana kutse ta shiga tsakani, na tabbata kuwa a duniyar nan ba zan sake katari da namiji mai nagartarsa ba. Kana ta bina da sharri, ka yi nan ka 'bata ni, ka bi nan ka 'bata ni, to ta Allah ba taka ba, ka ja tsumman rayuwarka, ba ma buk'atar ko kwabonka, ba na son munafurci ni."
Chapter 14 · 0% Book details