Sashe 23
Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yaran nan gabad'aya Allah Ya tayaka ri'ko." Ya ce." Na kuwa gode gwaggo, dama ai Yusuf nawa ne, na kar'ba har dashi Kamalun kuma zan ri'ke kamar ni na haifesu, ai ni ne da godiya Gwaggo." Sai ta sanya hannu tana goge hawayen da ya fara zuba a kuncinta. Sahura na taya ta. Ni kuwa gabad'aya jikina ya gama mutuwa ashe bana nan gwaggo ta kasafce mini yara. To idan kuma muka rabu fa, dama an ta'ba kyautar d'an mutum, ni kuwa da wace irin kalma ya yi amfani wurin janyo hankalinta irin haka. Har ya fice da tawagarsa ban dawo hayyacina ba sai da na ji muryar Sahura tana cewa." Lallai baka da ta Ido Yusi bin sa za ka yi ba zaka zauna wurin Gwaggo ka yi mata kwana biyu ba." Da saurin gaske na dubi bakin kofa wanda ya yi daidai da lokacin da yaron ya bude ya fita da sauri yana dariya." Na dubeta da mamaki mai yawa a tare da ni. Duk sha'kuwata da Yusi yau ya nuna mini iyakata sam baya son ma had'a ido da ni. Sai kawai na ji 'kwalla ta ciko idona, amma ban bari ta zuba ba na dinga mayar da ita ina jin Gwaggo na ta fad'in nagarta da mutuncinsa Sahura dama haka take so ta biye mata suna ta binkito abubuwan da yake aikatawa na bayan fage. Na juya ina laluben Hamusu a d'akin shi ma baya nan, daga ni sai Sahura da Gwaggwo da alama tun lokacin da ya zo tafiya ya bi bayansa shi ma. Gaskiya masu kudi da mulki suna jin dad'i sai ka ga babba da yaro kowa ya yi mubaya'a shiyasa idan a ka yi katari da wanda bai san menene zamani ba sai ya fara d'agawa da izza daga lokacin da Allah ya kar'bi damar daga hannunsa sai ya gane Allah daya ne. Ban iya sakin jikina da Gwaggo ba tun bayan tafiyarsa bakina ya mutu domin kuwa ban ga abinda zan ce mata ba, mafi yawancin hirar ita da Sahura suke yin ta. Muna zaune inna Zulai ta shigo, mu gaisa cikin mutunci har aka d'an ta'ba wasa da dariya tunda macace mai barkwanci.. Sai bayan Isha'i Hamusu ya dawo yana fad'in can Danbattan ya bi su. Har yana gayawa Gwaggo sakon gaisuwar Hajja kafin ta zo. Murmushi kawai na ke yi ina kallonsa cikin raina ina tunanin irin dambarwar da muka sha akansa har da su Allah Ya isa. Allah sarki shi kuwa sai rawar jiki yake yi saboda kyawun zuciya. Muka yi sallama da Gwaggo da alkawarin zan sake shigowa gobe idan ba a sallameta ba amma ba da safe ba sai yamma, saboda ba na so na sake riskarsa tunda ya ce zai kawo Hajja kuma da safen. Bakin titi muka fita muna jiran abin hawa Hamusu yana fad'in." Anti mutanan nan suna da karamci wallahi ashe Yallabai gada ya yi wurin mahaifiyarsa wallahi ba ki yadda ta karamma ni ba jin cewar ni kanin mahaifin Yusi ne, ta sanya aka kawo abinci da abinsha har da kyautar kudi dubu talatin fa." Murmushi na yi na ce." Hamusu kenan." Ya ce." Wallahi anti Amina da gaske nake fa samun mutane masu dattako a irin wannan zamanin sai an tona, su dai Allah ya gama yi musu komai." Sahura ta cafe maganar tana cewa." Sai ma ka ga yadda yake wasa da dariya da ma'aikatansa abin zai baka mamaki wallahi, ai muna cikin alheri Hamusu na gaya maka idan zai shigo kano sau hamsin a shekara wallahi sai mun san ya shigo domin mu da muke aiki dashi a sassan reshen kamfanoninsanan yana yi mana alheri kwarai da gaske. Ya ce." Ni ma sheda ne anti Sahura na ga alherinsa yau ." Na ce." Sheda a ina Hamusu Yayanka Aminu mai ya tsira dashi?" Suka dube ni da wani irin yanayi. Na ce." Kwarai kuwa, ko za ka iya nuna mini abinda Yaya Aminu ya tsira dashi kafin ya mutu. Sai wahala fa, amma shine kake so ka bugi kirji kace kaima shaida ne ko akansa ko Hamusu.." [9/8, 11:00 AM] Aunty B: 75 A sanyaye da rashin karsashi Hamusu ya bi ni da kallo a lokacin dana gama maganata. Yadda na fahimta kawai ya yi shiru ne ba wai don bashi da abin fad'i ba. Sahura kam akan tun akan titin ta fara yi mini sababi, abu ne mai wahala kaga abinda zai tunzurata tana da mugun ha'kuri da d'auke kai, ko a makaranta ma bata da abokin fad'a kowa nata ne, ansha yin fad'a kace-kace da muguwar gaba a ajinmu amma sannu a hankali ita take shiga rigimar kuma ta sasanta. Na lura kuwa akan mutumin nan bata da hakuri tunda wannan shine karo na biyu da ta bud'e mini wuta kamar 'yar cikinta. Na farko lokacin da na yi dogon rubutu akansa a fece book, dukda a waya mukayi muyasar yawun na lura ranta ya yi mugun b'acin dalilin da ya sanya ma kenan na sauko har na nemeta da ta yi mini jagorar ganinsa. Sai wannan shine karo na biyu sam ta manta akan titi muke fad'i take yi a gaban kowa ma za ki iya fad'in haka Amina domin na lura hankalinki ragaggene, to bari ki ji wallahi kanki kike da'bawa wuka, karonku na farko ke dashi ba ki labari ba, ballantana yanzu da kike karkashinsa. ai duk mai hankali zai fahimci jawabin da ya yi cewa babu dole akan abinda yake yi ma'aikatansa ne, ihisani ne kawai a tsakani kuma ke da bakinki ki ka gaya mini akwai wanda ya ke shirya wannan zalinci, wallahi abin kunya ne a ji wannan maganar daga bakinki sis, domin duniya ce zata zageki, ni kan haka gaskiya zan iya yin nesa dake tunda ba kya d'aukar ke shawarata" Ta karaci bambaminta ban tanka mata ba. Hamusu ne dai yake ta tausarta na yi musu shiru ina ta ko'karin tsayar da abin hawa. Kawai na ga ta tsayar da wani ta yi shigewarta tana gaya masa ja'in zai kaita. Na saki baki ina bin babur din da kallo har ya 'bace daga wurin. Mamaki mai yawa ya rufe, ni dai a ganina ban ga abinda tayar da jijiyar wuya akan maganata ba. Murmushi kawai na yi ina gyada kai lallai lamari ya baci tunda Sahura ta yi irin wannan fushin mun tawo tare kuma mun rabu da takaicin juna. Hamusu ya tsayar mini da abin hawa. Na shiga na zauna ina dan nazarinsa shi kansa yanayinsa duk babu dadi ya nuna abinda ya faru ba yi masa sukari ba. Hannuna na daga masa ina fad'in sai ka shigo. Direban ya ja da k'arfi muka bar wurin. Tsaf na samu gidan Yusura ta gyara ko'ina, tana kwance a falo ita kadai shiru sai ta ba ni tausayi sosai ta kar'bi jakkar hannuna tana yi mini sannu da zuwa. Na zauna babu k'wari a jikina ta kawo mini ruwa na dan kurba kad'an sai da na d'an samu nutsuwa tukkuna na tashi na dauro alwala tunda magriba a hanya ta yi mana, gashi ana kiran Isha'i. Tare muka gabatar da sallar da ita bayan mun idar na ce ta zuba abinci ta ci, domin ni gabad'aya cikina a cushe yake. Saboda kada kad'aicin ya yi mata yawa na bata wayata na ce ta shiga ta yi kallo. Na shige d'aki na kwanta da tunani a cikin k'wanyata. Ina daga cikin d'akin a kwance na ji an kira ni a waya kafin ma na yun'kura ta shigo d'akin tana fad'in." mama ana kira." Wayar na kar'ba ta kama hanya ta fita. Hamusu ne na daga a nutse ina kiran sunansa ya gaishe ni kamar koyaushe na amsa sai ya dora da fadin ." Anti ba zan samu shigowa yanzu sai gobe in sha Allahu Ina fatan babu matsala ko?" Murmushi na yi na ce." Babu komai Hamusu ko kaima fushin kake yi da ni ne irin na Sahura?" "A a anti, ai duk abinda ki ke yi kina yi akan d'an'uwana ta yaya zan yi fushi dake amma kuma fa maganar anti Sahura akan hanya take anti Amina, Ina ganin zuwa yanzu ya kamata ace kin manta da abinda ya faru, idan an yi duba da irin tarin alheran mutumin nan, bai cancanci suka da zambo a wurinki ba." Dariya kawai na yi domin ni kaina na san ba ni da hujja mai karfi da zan ri'ke domin kare kaina. Na ce." To na ji ai ba zan ki amfani da shawararka ba Hamusu zan kiyaye." Sai ya saki muryarsa sosai yana fad'in." Na ji dadin hakan sosai Anti Allah Ya kara girma." A hankali na amsa Ina dan murmushi wato dai ni a ko'ina ba ni da sa'a, ba ni da magoya baya muddin akansa ne. Sahura na fara nema a waya domin ba na so ta kwana da takaicina. Kiran duniya ta'ki daga mini waya. Sai na tura mata text na ban ha'kuri har da yar zolaya. Amma ba ta yi maido mini da amsa ba. Ban ha'kura ba na sake kira nan bata daga ba sai na rabu da ita zuwa gobe da safe nasan ta dan sauka. Na kwalawa Yusura kira ta shigo na mik'a mata wayar tare da cewa." Je ki cigaba da kallonki." Tagogin d'akin na bud'e dalilin zafin da na ji yana nasata. Dama tun can ban sanya fanka a d'akin ba sai ta tsaye na saya nake amfani da ita to tana can shago yara na amfani da ita dalilin da ya assasawa uwardakin zafi abun ya hadu da tasowar hadari. Bude tagogin da na yi ya sanya sauro shigowa dole ta sanya ni barin d'akin bayan na yi wanka na samu riga ta shan iska mai hannun shimi na sanya amma ta sauko mini sosai sai dai ta matse mini jiki sai na sanya hijabi akai na fito falon na samu Yusura ta bingire bacci ya kwasheta ga waya tana yi da film din bahubali wanda Yusi ya matsa dole sai da aka tura mini a wayar anti Yagana yake wai yana son film din zai dinga gani. Dole bacci ya kwasheta ga iskar fanka ga ta hadari yake tasowa ba ina jin dalilin da ya sanya ma kenan d'akin ya