← Book details Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 33

Sashe 12

Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Dariya ce ta k'wace mini duk da halin da nake ciki amma yadda anti Yagana ta hakikance tsakaninta da Allah sai ta ba ni tausayi da dariya na ce." Anti Yagana ki yi hakuri ba zan iya hayakin komai ba indai akan bawan Allan nan ne, mu yi addu'a kawai idan da alheri komawata gidansa sai na yi hakuri na koma, idan kuma babu alheri sai ki ga Allah ya kawo mini wani."
Ta 'bata rai tana cewa." Matsalata dake taurin kai Amina, kishiyarki wallahi ba a zaune suke ba, babban burinsu ki fice ki bar gidan, kin ga idan ba ki ba ni goyon baya ba sai na yi asarar kudina dubu arba'in na fitar aka ba ni turaran nan da kuma wannan rubutun."
Na cika da mamakin jin kudin da ta bayar har dubu arba'in lallai anti Yagana ta d'auki lamarin nan da girma, ai idan dan ta ni ce wallahi ba wani yawon neman taimako da zan yi a ci kudina a banza. Na tabbata anti Yagana bata ta'ba zuwa wurin wani malami ba sai akan matsalata hakan ne ya sanya na amince zan yi amfani da maganin amma da sharad'in ko da bai kira ba to ba zata kira shi ba domin ta ce mini malamin ya ce idan bai kira ba to sai a kira shi.
Ta amince da abinda na ce ni kuma na kar'bi rubutun da turaran a take a lokacin na fasa daya nasha ba tare da yakini ba.
Da kanta ta je ta hura wuta ta ruru sosai ta shigo da garwashin da yawa a cikin kasko irin na kasa ni dai kallonta kawai nake yi ina mamakin yadda ta d'auki al'amarin.
D'aki ta nufa da rushin wutar kafin ta kwalo mini kira na tashi na je na sameta tana kwance ledar turaran, ta ce." Sai kin cire kayan jikinki tsaf sai ki rufa da wannan zanin, amma idan kin zuba turaran akan wutar sai ki dinga yi kina kiran sunansa.
Fashewa na yi da dariya na fadi saman gado ina kyakyatawa domin duk yadda na kai ga son ganin na danne dariyar kasawa na yi.
Ta yi kasa'ke da ledar maganin a hannunta tana hararata. Ni kuwa Ina dariyar na ce." Wallahi anti Yagana dariya kike ba ni, wani irin turare ne wannan da har sai na yi tum'bur haihuwar uwata, na rantse da Allah malaman nan suna nema su jefa mata a masifa."
Ta sha kunu tana cewa." Kina d'auka abin nan da wasa ko Amina, nema ma ki ke yi ki mayar da ni mahaukaciya saboda baki da mutunci ko ina tsaye akanki amma ki sanya ni a gaba kina yi mini dariya ba za ki fahimci abinda nake nusasheki ba sai ranar da ma'kiya suka kai ki 'kasa tukkuna."
Ganin yadda ranta ya 'baci ya sanya na tashi zaune sosai na kar'bi ledar da turaran yake daure Ina fad'in." Zan yi yadda ki ke so anti Yagana"
Shiru ta yi mini tana cigaba da wurgo mini harara. Babu yadda na iya da ita haka na tashi na fara cire kayan jikina, ya rage daga ni sai rigar mama tana tsaye tana kallona na dubeta tare da cewa." Ko suma din na cire su?"
Ta girgiza kai." Ki bar su kawai ai."
Ban sake cewa komai ba na zuba turaran akan wutar lokaci guda hayakin mai kauri ya tashi na yi sauri na rufa zanin ajikina na dukufa kan wutar ita kuma da sauri ta kama hanyar fita tana fad'in." Kada ki manta ki dinga ambaton sunansa fa."
Na ce." To shikkenan."
Ina jin karar jan kofarta na cillar da zanin na tashi daga kan wutar na matsa gefe ina haki da tari ya sarke ni.
Hayakin ya cigaba da bin iska ina gefe guda. Na ji motsin bude kofarta a guje na d'auki zanin na je na dukufa kan wutar ta leko tana cewa." To kin ga haka ai ya fi, kin shaki hayakin sosai, in sha Allahu da izinin Allah zai kira waya yau din nan sai a daidaita, malamin ma cewa ya yi hakuri zai bayar."
A zuciyata na ce.'' Anti Yagana da tun farko kin k'adaita Allah ba za ki nufi wajan wani malami ba, suma duk hasashe suke yi.
To haka muka yini muna tattauna sha'anin Hadiza da abinda ta aikata, ni ma yanzu na dawo daga rakiyar Ummansu domin ta zama bakin ganga na yarda itace take dorata a gwadabe mara kyau amma duk lokacin da zata kira ni a waya nuna mini take yi itama Hadizan tafi k'arfinta ha'kuri take da halinta a zahiri kenan amma a bad'ini bakinsu d'aya. Na riga na gama fahimtar cewa Hadiza da ni take gasa tun daga kan mutuwar aurena kawowa yanzu burinta itama ta tara arziki har ta kere mini.
Tun bayan sallar Isha'i na lura da anti Yagana jikinta ya yi sanyi duk wani abu da take yi babu kuzari domin abincin dare ma ni na yi mana towon samovita miyar ku'bewa tun yamma take ce mini jikinta yana ciwo dalilin da ya sanya kenan tasha Panadol ta kwanta amma dai karin kasalarta yana da ala'ka da dakon kiran wayar Alhaji Tajo domin yadda na fahimta ta gama aminta da abinda malaminta ya gaya mata.
Muna d'an ta'ba hira sama-sama Babandi ya zo, bai samu wata tar'ba ta arziki ba a wajan matar gidan anti Yagana kenan, ni kaina daurewa kawai na yi nake tanka masa amma duk da haka babu cikakkiyar sakewa kamar yadda muka saba, ina jin hakan da ya fahimta ne ya sanya shi yi mana sallama ba tare da ya shirya tafiyar ba domin idan dai za mu had'u muka shafe sama da awa biyar muna hira ba tare da gajiya ba, yanzu kam ko minti talatin bai yi ba ya kama hanya ya tafi ba karsashi a tare dashi.
Anti Yagana ta rakashi da tsaki da harara duk ina kallonta ban ce mata komai ba.
goma da wani abu Babansu Fadila ya shigo ita lokacin ta shiga d'aki tana kintsawa.
Ya tsaya a falon muna dan ta'ba hira da yake akwai sabo a tsakanimu dukda wani sa'in idan na zo garin har na kare kwanakina bai fi sau biyu muke had'uwa dalili shi din babban direba ne kuma yana da muk'ami a tashar da suke ajiye motocinsu da asuba yake fita sai dare yake dawowa kamar i yanzu.
Ya tsaya yana tsokanata da fad'in." Ranki ya dad'e ina kamun 'kafa fa, a cewa maigidan a irin wad'annan motocin nasa muna neman koda guda d'aya ce wadda za mu dinga lodi daga nan kudu, idan haya ake bayarwa a taimaka a ba mu, idan kuma za a ba mu ne sojan haya zuwa shekara biyu in sha Allahu sai mu mayar da kudin, dama tuntuni nake so na samu dama na bi ta karkashinki, kwanaki an ce mana ya rabawa direbobi biyar kuma uku daga ciki ma an ce kyauta ya basu ba mutum biyu ya kar'ba."
Chapter 12 · 0% Book details