Sashe 27
Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Ina ce wannan maganar mun rufe babinta tun wattanin da suka gabata dalilin da ya sanya fa kenan nake jin shakkun gaya miki saboda na fi kowa sanin halin rigimarki."
Na ce." Me ka mayar da ni mara son zaman lafiya ko me? ko duk wannan addu'ar da fatan alherin da na yi muku baka gamsu ba har sai ka jefe mini magana idan ka boye mini cikin matarka ai ba zaka 'boye mini haihuwar ba tunda ba zata ta'ba dawwama dashi a jikinta ba."
Shiru ya yi mini bai tanka mini ba.
Hakan ya kara dagula mini raina. Gabad'aya ma sai nake ganin yana so ne ya raina mini wayo ya muna tsaka da rikici ya wulakanta ni har da tukwicin saki ban yi masa komai ba kuma ya zo ya ce mini na taya shi murna akan wane dalili. Haushinsa da nake ji sai ya dawo sabo dal, na ji kamar na ce ya bar mini gidana amma babu halin hakan.
Ya kwanta tare da rufe idonsa yana jina ina ta sakin maganganu bai tanka mini ba. Na goge hawayen da ya d'an zubo mini a kumatu na tashi na fita.
Hauwa tana da ciki wannan ya nuna cewa daga zarar ta fara haihuwa zata kar'bi gidan. Ni kuma saboda son zuciyarsa na d'auki ciki na yi wahalar rainonsa da nakud'a na haihu daga baya abinda na haifa ya mutu. Ita Hauwa itace mai rayayyun 'ya'ya kenan.
Kishi ya rufe mini ido gabad'aya tunanina ya kulle har sai da muka yi waya da Anti Yagana ta sake mayar da ni hanya tukkuna na dan samu sasaauci tabbas Allah ne mai yi kuma shi ne mai kashewa da rayawa. Idan ya so duka yaran da Hauwa zata haifa su zama rayayyu idan ya so kuma ya d'auki ransu ba kuma tare da wata lalura ba. Tabbas akwai wannan ciwon kuma kisa yake yi bayan ya gama galabaitarwa amma hakan ba zai zama hujjar da za a ce ba za a haihu ba domin yana iya canza komai hakan ba abu ne mai wahala ba a wurinsa. Da wannan tauhidin nata muka yi sallama jikina duka babu karsashi da sukuni na sake yin tubus a lokacin da na tuna irin rantsuwar da ta dinga yi akan yadda ta tabbatar da cewa yana sona domin idan babu soyayya ba zai ta'ba zama irin yadda nake so ba har ya kwana a k'ukutance gida irin wannan da babu tsaro a cikinsa.
Haka na wanzu cikin nazari da tunanin rayuwar da zan fuskanta a gaba.
Dutsan guga na ce Yusura ta kar'bo mini a shago, tunda ko babu wuta babban gen suke kunnawa da kaina na goge masa kayan tsaf na ajiye masa a gefansa bacci yake yi sosai wanda na tabbatar da cewa maganin da ya sha ne yake tasiri a jikinsa.
Ni da yarinyar dai muka yi akin towon har da man shanu ya sayo na kuwa soya shi da albasa mai yawa. Na ce idan zai tafi asibiti sai ya zo ya tafi dana Gwaggo domin zai yi mata dad'i a baki.
Na had'a masa komai cikin babban tire har zobo na yi masa wanda ya ji citta duk don saboda ya samu sau'kin kirjinsa.
Biyu saura na koma d'akin har yanzu dai bai motsa ba ga lokacin sallah.
A hankali na dan bubbigi gefan katifar bashi da nauyin bacci dama can ya bude ido yana kallona na ce." Lokacin sallah ya yi.".
Ya yun'kura ya tashi zaune yana fad'in." Ina buk'atar ruwan zafi wanka zan yi tukkuna."
Na ce." Da ka ha'kura da wankan nan tunda ba ka jin dadin jikinka."
Girgiza kansa ya yi. "A a ki sama mini ruwan d'umi kawai.
Na tashi na fita ban sake cewa komai ba. A babbar tunkuya na d'ora masa ruwan sai da ya tafasa tukkuna na juye a bokiti na surka da d'umi sosai na kai masa bandakin d'akin.
Ya tashi jikinsa da kwari sosai ya shiga bandaki na bi shi da kallo jikina a d'an sanyaye ni kuma shine kaddarata jiyyarsa tsakanin jiya da daddare da yau jikina ya nuna ya na yi muguwar gajiya saboda kai kawo.
Maganarsa na ji daga bandakin wai na mika masa kayansa.
Ya zuro hannunsa na bashi kayan gabad'aya har singilitin da wandon ciki.
Na je na d'auko tiren dana shirya masa abinci na ajiye masa a gefan daddumar dana shimfida masa.
Bandakin tsakargida na yi wanka na koma cikin d'akin na same shi ya idar da sallah yana waya da Hajja har yana cewa da ita ta bashi Yusi. Ban ce komai na fara had'a masa abincin a maidaidaicin filat na ajiye a gabansa gefe da yajin daddawa da man shanu.
Na tsiyaya masa zobon a kofi.
Ga mamakina na ji ya fara dariya harda kyakyatawa ina jiyo muryar Yusi kad'an-kad'an ko me yake ce masa oho, na ji yana fad'in." Idan na kasa juyo da hankalinta kai ma sai ka zo ka gwada taka sa'ar don wannan Maman naka ta fini rigima."
Na ji maganarsa Yana fad'in." Dukana za ta yi wallahi ni tsoronta nake ji Baba."
Yana dai dariyar ya ce masa "idan ta dake ka sai na rama maka ai."
Jin haka na san da ni suke lallai ma Yusi ashe na zama abin zolaya a wurinsa, ban yi tsammanin akwai ranar da za ta zo yaron nan ya manta da ni ba.
Suna gama wayar ya dube ni yana fad'in." Kin ji ni da Yusuf ko? shi ya ba ni shawara na zo na baki hakuri, da na ce ya zo mu je tare ya ce a a dukansa ki ke yi.''
Murmushin takaici na yi na ce." Ai na ji abinda kuka shirya kai kuma ka rasa wanda zai baka shawara sai wannan mashiriricin."
Ya d'an janyo filat din da nasa masa towon ya tallafe da hannunsa yana fad'in." To menene ai yaronki ne ya rayu dake zai fiye da ni zai fi kowa sanin halinki."
Gyada kaina na yi a hankali na ce.'' Kun kyauta kai dashi ai."
Ya yi bismillah yana cewa." Towon nan tun kafin na yi loma guda yawuna ya tsinke wallahi."
Yadda ya tallafe filat din a hannunsa shine abinda ya ba ni dariya na tashi ina fad'in." Ka dai ci a nutse kada ka 'kware."
Bai ce mini komai ba ya cigaba da cin abinsa na zauna gefan katifa a nutse na janyo akwatin kayana na shiga duba kayan da zan sanya na yi wankan tun d'azu amma ban samu sukunin canza kayan ba ballantana na yi sallah. Na ji dai dadin ganin yadda jikin nasa ya yi sau'ki gashi nan har ya zage yana cin abinci.
[9/11, 9:26 AM] Aunty B: 78
Cikin rashin sukuni na gama shiryawa domin a jikina na ji cewa kallona yake yi. Ina juyowa kuwa muka yi ido hud'u da filat din towon a hannunsa yana ci yana kuma kallona kamar wanda ya samu tibi. Na d'an zumbura baki can k'asa-kasa na ce." Ni kam wane irin kallo ne wannan?"
"Me ki ka ce?"
Shiru na yi ban ce komai. Sai ya cigaba da cewa." Kin ce idan ni maye ne na ci kaina ko?"
Da sauri na dube shi da mamaki a tare da ni." Haka na fad'a?" Na ce cikin sigar tuhumarsa. Sai kuwa ya daga kansa." Eh mana haka ki ka ce ai na ji, yanzu kuwa zan zo na cinye ki, ai kin ba ni magani na yi ragal da ni, sannan kin ba ni towo da tantakwashi me ki ke tsammanin zai faru?"
Dariya maganarsa ta ba ni, na ce." Kana nufin ka warware kenan, muryarka fa har yanzu bata fita sosai."
Yana sud'e yatsun hannunsa ya ce." Za ki tabbatar da haka idan ki ka ji ni a jikinki."
Na ce." Ai ba ka fara ba, domin kuwa gidan nan bashi da wani tsaro kai ka san kanka ni ma nasan wanene kai ."
Ya yi shiru bai tanka mini yana cigaba da sud'e hannunsa na ce." Wai miyar ce ta yi dadi ko towon?"
"Duka sun yi dadi wallahi kin biya ni sosai yanzu abinda ya rage kawai ki cikashe ladanki ki ba ni kanki?"
Girgiza kaina na yi kawai Ina dubansa. Wani irin mutum ne da bashi da ta ido sakaka yake sakin maganarsa babu kunya balle kawaici.