Sashe 4
Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A tsanake ya yi sallama da mika godiya ga Allah da salatin annabi sannan ya fara da ce wa."
Ni dai Alhaji Tajudden Ibrahimu 'Danbatta a iya sanina da hasashena babu wani wanda yake karkashina da hakkinshi yake a wuyana. Tabbas wannan ka'idata ne kuma tsarina ne ba na d'aukar tsaffi aiki, matasa majiya karfi nake d'auka. A cikin matasan ma muddin na fahimcin gazawar wani nakan sallameshi na maye gurbinsa da wanda na tabbatar da cewa za mu taimaki juna.
Ma'aikatu nake dasu ba gwamnati ba ce ni. Babu yarjejiyar fansho da garatuti a form dina. Duk wani ma'aikici na ya san da wannan ya kuma amince da hakan. Ra'ayina ne yin alheri ga duk wanda na sallama saboda wani dalili, ra'ayina ne yin alheri da ihsani ga iyalan wanda ya rasu a karkashina, amma abinda nake so mutane su fahimta anan shine ba dole ba ne, ba kuma tilas ba ne in d'auki kudi na bawa wanda ya mutu ko wanda na sallama daga aiki kamar dai yadda na fad'a da farko ni ba gwamnati ba ne. Kuma maganar da mutane suke yi akan ba na zuwa ta'aziya ko dubiya wannan sharri ne aka yi mini. A duk lokacin da wani lamari ya faru muddin ina gari na kan yi kokari na je, idan kuwa wani uzuri ya rike ni na kan tura Alhaji Sammani da 'yan tawagarsa wad'anda duk suke a k'arkashin ikona kuma da alheri mai yawa. A lokacin da Aminu Salihi ya rasu ba na gari, kuma Allah ne shedata na tura a je a yi musu ta'aziyya tare da miliyar biyar domin a bawa magada, wannan shine abinda na yi. Ina so na gayawa duniya cewa' duk wannan maganganun da suke ta yawo akaina ba ni da hakki ila iyaka wanda na d'auki Amana na d'amka masa shi ya zambace ni. Babu wanda bai san yadda nake da Alhaji Sammani ba. Yau na fito na gayawa duniya cewa Sammani ne ya haddasa wannan lamari kuma ban fadi hakan domin na 'bata shi don na wanke kaina ba. A duniya kana iya zama da mutum da zuciya daya har ka dinga ya'kini a zuciyarka ba zai ci amanarka ba amma daga baya a samu matsala. Abinda ya faru kenan a tsakanina da Alhaji Sammani sai gashi lokaci kan'kani yana nema ya kai ni 'kasa, to saboda haka masu zargina da zagina ku bari domin ba ku da hujjar yin 'batanci a gare ni, sai ma dorawa kanku zunubi mai girma da kuke yi."
[8/17, 9:56 AM] Aunty B: 63
Cikin sanin makamar aiki d'anjaridar ya ce." To Allah Ya taimake ka za mu su mu ji karin bayani daga bakinka dangane da maganar da fita jiya da daddare wanda ake ta jita-jitar cewa da yawun Uwargidanka maganar ta fita, masu bibiyar sha'anin za su so su ji wani karin haske daga bakinka"
Dariya ya yi kafin ya ce." Babu yawun matata dangane da maganar jiya. Ni asalima ban san cewa tsohon mijinta ya yi aiki da ni ba sai da maganar nan ta fita, idan ma da yawunta a maganar ban ga aibu ba domin ta fito ne a matsayinta na uwa tana nemawa yaranta hakkinsu kamar dai yadda sauran mutane suke fitowa. Da ita da sauran iyayen marayun da suka yi magana na yi alkawarin bawa kowaccensu miliyan biyar biyar domin dogo da kai, kuma su kula da yaransu. Wannan na yi ne saboda Allah, sannan kuma har yau hanya a bud'e take ga duk wanda yake da k'orafi akaina zai iya tunkarata kaitsaye idan kuma hakan zai yi masa wahala zai iya isar da sakonsa ta kafafan sadawarsa domin korafinsa ya isa gare ni, a shirye nake da bawa matasa gudumuwa muddin sun bu'kaci hakan daga wurina."
Wannan maganar tasa ta k'arshe ita ta karya karsashin d'anjaridar duk k'wakwarsa sai ya rasa abinda zai fad'a domin kuwa an riga an dabaibayeshi da halin girma da dattako.
To abinda ya dinga tashe kenan a kafafan sadarwa. Wasu na fad'in hirar a rubuce ya yin da wasu ke d'ora bidiyon hirar a shafikansu ana ta zuba sharhi da cacar baki da bawa hammata iska idan aka samu b'angaranci daga mabiya dake comment section.
An nufe shi da sharri sai kuma Allah Ya juyar da lamarin mabiyansa suka kara ninkuwa sakamakon hirar da aka yi dashi kuma yawancinsu duk matasa ne majiya karfi wanda suka rasa abin yi.
Ni kaina na ji dad'i sosai dana saurari hirar mussaman wurin da ya wanke ni daga zargin da jama'a suke yi mini, duk k'wakwar d'anjaridar bai yarda ya soke ni ya soki iyayena ba, yana ta ko'karin kare mini mutunci amma hakan bai hana shi azabtar da ni ta karkashin kasa ba, gigin sabon aure ne ko tasirin asiri na kasa gane wanda yake dawainiya dashi sai sha mini kamshi yake yi
abinda na lura dashi shine tun ranar da Hauwa ta kwana a dakinsa wasu daga cikin al'amuransa suka canza. Mussaman daga 'bangarena. Bai iya tsayawa ya 'bata lokaci mu yi magana ba. Yau kwana uku kenan tare suke kwana na riga na san hakan dole zai faru tunda kwanaki bakwai musulunci ya tanadar mata shiyasa kwatansu bai daga mini hankali ba
Yadda dai ya canza a lokaci kan'kani shine abinda ya fi damuna tun washe garin ranar da suka kwana lamarin ya sauya salo. Zuciyata ta dinga yi mini sa'ke-sake akanta domin dai Ina ganin akwai hanyoyin da tabi wajan janye masa hankali ko asiri ko amfani da maganin mata. Sau daya dana hau samansa da zummar gaisuwa na fuskanci fuskar gizako ban 'kara marmarin sha'awa hawa ba, domin ba na so ko yaya ne ya yi mini abinda zai sanya ta samu kofar yi mini kallon banza.
ina tsammanin Hajja ce ta yi masa maganar tafiyarmu saudiya domin ni ban samu kofa ba tunda ban ga fuska. Kwanan Hauwa biyar da tarewa ya kira ni a waya, lokacin ina bandaki ina wanka, na ji ringing har sau biyu kwata kwata ban tsammaci shi din ba, domin kafin shigata bandakin na kira Anti Yagana a waya ba ta daga ba, sai nake tunanin ko itace ta kira.
Ina fitowa na dauki wayar ina dubawa wanda ya yi daidai da lokacin da ya sake kira na dan ji faduwar gaba kad'an dalili na san ba kasafai yake kar'bar uzuri idan ya kira waya ba a daga ba.
Cikin nutsuwa nasa a kunne kafin na ce komai a hasale ya furta." Kina ina ne Ina ta kiran waya."
Na tausa harshena na ce." Wanka nake yi."
Tsaki ya ja wanda ya ta'ba mini zuciya sosai, tunda nake dashi bai ta'ba yi mini tsaki ba, sai yau don kawai ban daga waya ba, a ganina tsaki yana daya daga cikin nau'ika na wulakanta mutum, kuma wata'kila tana zaune a kusa dashi ya yi mini haka.
Raina ya 'baci sosai zafin zuciyata ya motsa na dinga ji kamar na kashe wayar ma domin ban san wane kalar wulakanci zai yi mini a gaba ba.
Ya ce." Hajja ta yi mini magana akan tafiyarku jibi na ce ni ba ki gaya mini ba, ban sani ba ko kina da wani mijin bayan ni kin gaya masa."
'Kafafuna ne suka dinga kyarma jin maganar da ta fito daga bakinsa sai na ji wani gumi ya yanke mini kamar ba daga wanka na fito ba. Gabana na bugawa cikin kaduwa da furucinsa na ce" Ban gane abinda ka ke nufi?"
"Kin ji abinda na fad'a ai ba sai na maimaitamana ba, ba ni da wani mutuncin a wurinki, da ni da banza duk daya."
Na ce." Ka ga Baba, har yanzu ban fahimci inda maganarka ta dosa ba, in banda neman fitina kai ka ba ni kujerar nan ba tare dana roka ba, haka zalika kuma ka fini sanin yaushe ne tafiya, to me zai sanya haka kawai saboda kana jin haushinsa ka nemi daga mini hankali. Me nayi maka?ka jima kana zargina saboda kawai ka aureni bazawara baka tauna magana motsi kad'an zan yi sai ka mayar da abin wata manufa, idan ka gaji da ni kana da dama a hannuna fa."
"Ki zage ni kin ji ko, ai fitsara da rashin kunya ba sabon abu ba ne a wajanki Amina, kowa yana shura ya gagara ta fannin alheri amma ke duk wanda zai bude bud'e baki aibunki zai fad'a. Ina so ki sani wallahi tallahi ba zan juri wannan sakarcin ba, ba zai yiwu da mutuncina da k'imata a gari ki zubar mini da ita ba."
Na danne kukan da yake so ya kufce mini na ce." wani abun kuma aka ce maka na aikata? wannan cin mutuncin ya isa haka Baba, ko namiji ka kama ni dashi iyakacin abinda za ka yi mini kenan, idan ba ka sona yanzu don Allah kada mu 'batawa juna lokaci mu rabu cikin mutunci ba sai ka kayi mini 'kaharu ba."
Kashe wayar ya yi ba tare da ya sake ce mini komai ba. Na ajiye wayar a gefena tare da rufe fuskata da tafukan hannayena kuka mai karfin gaske ya k'wace mini.
Cikin rashin kuzari na dubi wayata da na ajiye a gefe lambar anti Yagana ce. Sai zuciyata ta sake karyewa hawaye ya cigaba da zuba. Cikin kuka na daya jin yanayin muryata ya sanya jikinta yin sanyi a hankali ta ce." Menene kuma? Ina ce magana ta mutu tunda maigidanki da kansa ya fito ya wanke ki a idon jama'a, kukan kuma na menene?"
Na ce." Anti Yagana kisan mummuk'e yake yi mini wallahi na rasa gane inda ya dosa, ai kin ga dai ya fito ya nunawa duniya girma da matsayina, amma wallahi duk wannan k'aunar da kulawar a yanzu babu ita, a tsukin nan cikakkiyar gaisuwa bata wanzuwa a tsakaninmu abinda ya fi daga mini hankali yawan zargina da yake yi, motsi kad'an zai canza mini manufa, kin ga zargi a cikin aure haramun ne."
A sanyaye ta ce." Sai fa kin yi hakuri a wannan lukutan kin kawar da kai gefe guda, kin ki ji, kin ki gani, tunda yana da sabuwar amarya, ke ma kuma kishi yana damunki Amina, Ina ganin shine abinda ya hana ki zaman lafiya da mijinki."