← Book details Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 33

Sashe 28

Gudun Aure Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Muka fara bugawa dashi domin akan sai ya kwanta da ni fa acewarsa towon da na bashi ne ya tayar masa sha'awa ni kuwa nasan ba haka ba ne kawai neman fitina yake yi tunda ya samu kansa mura da zazzafin sun yi sau'ki, na riga na san da wahala dama hakan bata faru ba sanin hali yafi sanin kama.
Ya rufe d'aki gam! ni kuma ina jin tsoron yarinyar nan ta ji shiru ga d'aki a kulle ta gane wani abu muke yi. Ni kaina a cikin buk'atar nake nasan kuma yadda na tara sha'awa haduwarmu ba za ta yi kyau ba.
Ganin yadda nake ta fargaba akan kada yarinyar ta fahimci wani abu da farko yana magana a hankali sai ya fara daga muryarsa tunda ya lura ba na son hakan yana cakumo ni da kokawa, takaici da b'acin rai suka dame ni, na rasa yadda zan yi dashi duk ya yamutsa ni gabad'aya rigar jikina ma ya cire mini.
Hawayen takaici suka dan zubo mini a kumatu a mai hali baya fasawa. Muna tsaka da hakan aka kira wayarsa hakan ya ba ni damar kwacewa a gaggauce na d'auki rigata ina sanyawa a jikina.
Hauwa ce ta kira wai bata da lafiya bayan haka kuma gidan ya yi mata girma.
Ban jin amsar da zai bata ba na fita daga d'akin da saurin gaske tsakargidan na samu Yusura tana kwance kan tabarma tana kallo a wayata.
Na sauke ajiyar zuciya cikin yakini da amincewa ba ta ji abinda ya faru ba tunda da alama kallon ya d'auke mata hankali. Na zauna gefanta muna kallon tare amma hankalina kaf yana kansa. Ina dan jin motsinsa da amsa kiran waya jefi jefi.
To a takaice dai a ranar da yamma aka sallami Gwaggo daga asibiti Hamusu ya zo ya sanar da ni cewa yanzu tana gida kuma babbar yayarsu da take aure a kamaru ta zo yanzu haka suna tare da gwaggon. Na ji dadin zuwa Yaya Talatu da yake haka muke kiranta a can kamaru ta yi aure da yaranta hud'u shiyasa ba sosai a ake ganinta ba sai da gagarimin dalili tun bayan rasuwar Yaya Amina bata sake zuwa ba sai yanzu. Na tabbatar kuwa ba zata koma ba sai jikin Gwaggon ya kara kwari da izinin Allah.
Hamusu kafin ya fita ya tambayeni Yallabai na ce masa Yana ciki Yana hutawa.
Koda na koma d'akin sai na same shi akan dadduma ya idar da sallar la'asar muka had'a ido na yi saurin shigewa bandaki na d'auro alwala na fito fuskata a d'aure bai sake birjiro mini da wata fitinar fa ganin yadda na keta bata raina sosai ya ce na bashi ragowar shayin da na yi masa alkawari. Na hada masa da zafinsa rau na ajiye a gabansa sai bi na da ido yake yi Ina sake cin kunu.
Ni kaina nasan abinda nake yi din bai kai a ce ya kyaleni dan shi ba sai don ya ga rashin dacewar hakan akaran kansa shiyasa ya janye fadi ma yake yi ya gaji da zaman gidan so yake dare ya yi yayi tafiyarsa. Uffan dai ban ce masa ba domin ba na so kuma wata magana ta yi tsayi a junanmu.
A nan din ya yi sallar Isha'i, ya ce na d'umama masa ragowar towonsa na yi masa yadda ya buk'ata ya zauna ya ci sosai ya kira Sukairaju a waya suka yi magana duk Ina zaune minti talatin ya iso har kofar gidan.
Nan na fahimci ya kira shi ne domin ya ja shi a mota. Da zai tafi bai sake tayar mini da wata magana ba, sai kuma jikina ya mutu na d'auka zai sake yi mini maganar zabar gidan da zan zauna kamar yadda ya bukata. Cikakkiyar sallama ba mu yi ba ya kama hanya zai fita, na bi shi a baya da agogonsa da ya manta a kan katifa. Ya kar'bi abinsa kawai ya yi gaba, hakan da ya yi sai ya tsaya mini a rai, ita gaskiya d'aci gare ta, ban ga abin jin haushi ba tunda iyakacin bakin kokarina na yi masa.
Koda na idar da sallar Isha'i sai na kira Sahura na ci sa'a ta daga muka gaisa na ce." Kin daina jin haushina kenan?'
Babu annashuwa ta ce." Ba zan daina jin haushinki ba sai kin gyara halinki."
Ina dariya na ce." Wani hali ne da ni mai muni Sahura."
Shiru ta yi mini ba ta ba ni amsa ba, na ce." Mutumin fa anan gidana ya kwana".
Da mamaki ta furta." Da gaske ?"
"Wallahi bai jima da tafiya ba ruwan jiya da daddare ya d'an same shi?"
Tana jimantawa ta ce." Amina kin samu kan bawan Allan nan wallahi ki ji tsoron Allah, ban ga namijin da yake bibikon mace kamar na ki ba, ki zauna ki yi nazari ke kanki kin san idan baya tsananin sonki ba zai ta'ba yarda ya kwana a wannan gidan na ki ba.
Ina dariya na ce." Haka ma Anti Yagana ta fad'a ni kuwa jinku nake yi ni nasan wanene shi, amma kin san wani abu ya ba ni tausayi ni kaina wallahi ba ki ga yadda ya sha wahala jiya ba saboda dukan da ruwa ya yi masa ya lafke zazzabi mura tari da ciwon kai da kyar muka rintsa ga uban sauro da zafi a d'akin."
"Humm! ki bari dai ya k'wace miki za ki yi kuka wallahi."
"Ba wani kuka da zan yi Sahura ha'kuri da juna muke yi ni dashi fa kuma kune kuke ganin kamar ni nake cutarsa, mu bar maganar nan haka sis tunda kin kasa fahimta amma ina so ki san da cewa amaryarsa na d'auke da juna biyu d'azu yake gaya mini."
"To shine me? kema Allah Ya ba ki naki rabon ba shikkenan."
"Sahura ba na jin fa zan yarda na sake haihuwa haka kawai ba zan yanki tikitin wahala da hannuna ba."
A takaice ta ce." Shikkenan ai." Yadda ta fad'i maganar shi ya tabbatar mini da cewa cikin takaici take ta ce." Wanki fa nake yi ki ka kira waya zan kashe."
Na ce." Da daddare wanki Sahura?'
"Ina da me yi mini ne?''
Ta ba ni amsa a kufule?"
Na ce." Ki had'a ki bayar zan biya."
"A a, ni menene amfanin lafiyata."
Na ce." Na ga alama rigima ki ke nema Sahura a ina zan samu mai kunshi ne?''
"Muna da su anan sosai."
Na ce." To ko za ki turo mini ita ta zo ta yi mini."
"Idan hakan ya yi miki sai na turo ta."
Na ce." Duk abinki dai ba zan yarda na yi fad'a dake ba Sahura."
Ta ce." Dama kin ji na ce miki mu yi fad'a, ai gaskiya d'aci ne da ita."
Tafad'a tana d'an jan tsaki.
Na ce." Ai na ji shawararki shiyasa ma na amince zan cigaba da zama dashi gashi har ina neman mai kunshi haihuwa ce dai na ce ba zan yi ba."
"To kada Allah Ya sa ki yi, idan kin samu cikin ki zubar kawai."
Ta datse kiran ba tare da na farga ba.
Dariya na dinga yi mamakinta ya rufe ni wai lallai sai ta gaya mini bakar magana alhalin ba ita za ta yi mini zaman auran ba, mai d'aki shi ya san inda yake yi masa yoyo.
Chapter 28 · 0% Book details